Gwamnatin tarayya zata sa dokar hawa mashin.

 Gwamnatin tarayya tana duba yuwuwar haramta hawa Babura wanda akafi sani da Okada.

Attorney Janar na kasa Kuma ministan Shara’a Abubakar Malami, ya bayyana haka a lokacin zantawarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan kammala taro akan shaánin tsaro wanda shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Okada


Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa ana anfani da masu okada wajen hakar maádanai a fadin kasarnan kuma haramta okada zai taiaka wajen hana yan bindiga samun kudade.

Ministan wanda suka tara da ministan harkokin cikin gida  Rauf Aregbesola da Mohammed Dingyadi, ya bayyana cewa taron yam aida hankali ne akan yadda za a daile ayyukan yan taádda.

Ya bayyana cewa gwamnati tana bukatar daukar kwarararn matakai saboda yan taáddan sun fadada ayyukan zuwa hanyoyi da dama da suka hada da wajen hakar maádanai da kuma karbar kudin fansa.

Akan ko Gwamnati zata duba illar dake tattare da hana okadan kuma da harkokin hakar maádanai ga yan najeriya musanman talakawa, ministan ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta Gwamnace ta yi abin da zai anfani kasa da alumma baki daya ba wai mutun guda ba.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post