INEC zata wallafa takardun da yan takaran yan majaisar dokoki suka gabatar mata

 Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta  INEC ta bukaci yan najeriya su yi nazarin takardu da yan takaran Gwamna dana yan majaisar dokoki suka gabatar mata wanda zata wallafa a kasa baki daya a juma'ar nan.

INSC


Shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a wajen rantsar da sabon kwamishinan hukumar zabe a jihar Kogi , Dr Hale Gabriel Longpet a Abuja.

Ya riki yan najeriya cikin har da yan takara da suyi anfani da wannan dama wajen duba dukkanin takardun na yan takara tare da shigar da duk wani koke ko matsala da suka gano a tattare da takardun musanman idan sun sabawwa dokar zabe na 2022. 

Professor Yakubu ya bayyana cewa tuni dai hukumar zaben ta shawo kan wasu korafe korafeb zaben fidda gwani na jamiyyu akan zaben 2023. 

Shugaban hukumar zaben ya jaddada kudurin hukumar na tabbatar da ganin cewa kwamishinan hukumar zaben yayi abin daya dace har zuwa karewar waádinshi.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post