A ranar laraban nan ne 21 ga watan yulin 2022, kungiyar matasan karamar hukumar Lere (LELOGYF) ta tattauna da wakilan da aka turo da gyare gyaren da in an kammala zasu Mai da wutan a Karamar hukumar Lere Wanda Hon.Muhammad Lawal Rabiu ke jagoranta.
LELOGYF |
Sakataren kungiyar, Abdullahi Shehu ya bayya mana cewa, "a tattaunawan mu Dasu, sun tabbatar Mana da cewa anturo su ne daga hukumar sugar lantarki domin suyi aikin gyare gyare Wanda daga bisani bayan kammala aikin, su hada wutan."
Abdullahi, Ya kara da cewa, "Kaman yadda Yan siyasan mu da kungiyoyi sukayi ta kokarin ganin an maida wuta a baya Wanda har akazo Yanzu Hakan ba yiwu ba , Yanzu matakin da Hon. Lawal Muhammad Rabi'u ya dauka yasha bambam, Wanda muke da kyakkyawwn fatan Ganin ta hanyar za'a dace don ganin an magance matsalar."
"Matsalar wutan lantarkin da yanzu muna kusan kimanin shekara biyu kenan." Inji Sakataren kungiyar.
Read also: Latarki: Matsalar wutar Lantarki ya kusa zuwa karshe a Lere
Har wa yau ya baytana cewa "Manyan Yan siyasan mu irin su; Hon. Abubakar Buba, Eng. Ahmed Muneer da Manyan sarakunanmu, da kuma Kungiyoyin dattawar mu na Lere LGA kaman su Gidauniyar masarautan Lere, SAPPEF Na Samainaka sunyi iyakan kokarin su Amman Abin yaci tura."
"Muna masu tabbatar Ma matasan Karamar hukumar Lere da cewa kungiya zataci gaba da bada nata gudunmawan dari bisa dari ga duk Wanda keson saka hannun jarinsa gurin ganin an ceto karamar hukumar Lere daga duhun rashin wutan lantarki."
Daga karshe ya nuna jin dadi game da matakin da ake yanzu, ya kuma nuna godiya tare da rokon Allah, Allah yasa aikin da Hon Lawal Muhammad Rabiu yadauko yakaiga ci.