Hukuncin Azumin Arafat Ranar Juma'a

 Duk wani alheri na cikin bin magabata kamar yadda dukkan sharri ya tattara a shaci fadin yan baya. Malamai magabata sun yi bayanin cewa haramcin keɓe ranar Juma'a da azumi ya takaita ne kawai ga masu niyyar haka, don haka idan ranar Arafat ta zo daidai da ranar Juma'a, to babu laifi a keɓe ta da azumi kuma ba a wajabta yin azumin kwana ɗaya kafin ta.

Ibn Qudamah ya ce a cikin Al-Mughni: Na ce: "Wani mutum ya kasance yana azumi wata yini ba ya azumci wani mai bin sa (wato azumin annabi Dawud), sai shan ruwansa ya fado ranar alhamis, azumin kuma ya fado masa ​​ranar Juma’a, shan ruwa na gaba kuma ya zo a ranar Asabar, sai haka yasa ya azumci Juma’a ita kadai? Sai ya ce: shi ai wannan bai yi niyyar azumin juma'a a kebance ba, abin da aka kyamata shine kebance ranar Juma’a da gangan". 

Ya kamata a lura da cewa hanin da aka ambata a hadisi, hani ne na karhanci, ba hani na harakci ba. A cikin ‘Awnul Ma’bood: Al-Tibi ya ce, "mafi rinjayen malamai sun yi ittifaqi a kan cewa hanin kebe ranar juma'a da azumi, hani ne na karhanci ba bani na haramci ba". 

Don haka bisa dogaro da maganganun malaman da suka isa su yi fatawa akan wannan mas'ala, ba wata matsala a azumin ranar ARAFAT da ya fado a gobe juma'a. Jama'a mu kwana na niyyar azumi. Allah ya karba daga care mu, amin.

Allah shine masanin daidai

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post