Ka ba abokinka aron ₦4,000,000.00 a shekarar da ta gabata, kuma tun a wancan lokacin ya ki biya, wanda hakan ya sa abokantakar ta tabarbare.
Ka roke shi kawai ya biyaka ₦2,000,000.00 ka manta da sauran saboda kana cikin matsalar kudi.
Abokinka sai yace ₦1,500,000.00 kawai zai iya baka tunda shi kadai yake da shi.
Hakan yasa ka amince domin baka da wani zaɓi.
A ƙarshe ka ba shi bayanan asusun ka don aika adadin kudin kai tsaye zuwa bankin ka
Kana tashi da safe, ka duba wani sako dake wayarka kawai sai ka ga ₦15,000,000.00 a cikin asusun bankin ka.
Ka ci gaba da kallon fuskar wayar cikin mamaki amma kuma tabbas ₦15m ne.
Sai ka dauko wayar ka ka sami missed calls guda 53 daga gare shi da kuma karin sakonnin tes guda 27 yana rokonka da ka mayar da ₦13,500,000.00 tunda kawai ya nufa ya tura ₦1,500,000.00 kuma ya yi kuskure ya kara wani karin "0."
Idan kai ne abokin ya za kayi;
1. Aika da baya ₦ 13,500,000.00
2. Zaka ɗauki ₦4,000,000.00 ka ne?
3. Rike kudin duka ₦15,000,000.00
4. Kashe wayarka kuma ka bar yakin?
Ina neman amsar ku a comment box.