Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai hari a wani shingen binciken sojoji da ke gindin shahararren dutsen Zuma Rock a jihar Neja a daren Alhamis.
Inda aka kai harin na da nisan kilomita biyu zuwa Zuba a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar wata kungiyar tsaro ta Eons Intelligence ta hanyar tabbatar da shafinta na Twitter, @eonsintelligenc, ta ce ‘yan bindiga da sojoji sun yi artabu da bindiga a shingen binciken ababan hawa da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.
JUST IN: Armed bandits and the military are currently engaged in a gun duel at the checkpoint in Zuma Rock Madalla, along the Kaduna-Abuja highway. Reinforcement team is now in pursuit of the bandits... Details later
— Eons Intelligence (@eonsintelligenc) July 28, 2022
Keep up the Good work Oga
ReplyDeleteMay Allah protect us
ReplyDelete