Hanyar Kiyaye Gyambon Kwanciya (Pressure sore) A Alƙur'ani.

Hanyar Kiyaye Gyambon Kwanciya (Pressure sore) A Alƙur'ani.

Gyambon kwanciya, wato "pressure sore" ko kuma "bed sore" a turance, lahani ne ga fata zuwa tsoka sakamakon tsawaitar kwanciya, musamman a gadon baya, wato kwanciyar rigingine ko reran. 

Gyambon kwanciya ya fi faruwa a sassan jiki da tudun ƙashi ya bayyana ko kuma inda ƙashi ya fi kusa da fata kamar bayan kwankwaso, ƙeya, gwiwar hannu da dunduniya.

Tsawaitar kwanciya a sashi ko ɓangare ɗaya na sanya fata ta ɗaɗe har kuma ta fashe. Idan matsalar ta ci gaba, kitsen ƙasan fata zai cinye har tsoka ta bayyana.

Idan ba a shawo kan matsalar ba, haka abin zai ci gaba da cinye tsokoki har ƙashi ya bayyana. Bayyanar ƙashi na nuni da cewa gyambon kwanciya ya kai mataki mafi tsanani.

Gyambon kwanciya ya fi samun majinyata da suka daɗe a kwance, musamman waɗanda ba sa iya jujjuya jikinsu daga dama zuwa hagu.

Haka nan, majinyata masu fama da larurorin ƙwalƙwalwa, laka da kuma waɗanda ba sa cikin hayyacinsu sun fi haɗarin samun gyambon kwanciya.

Sababin gyambon kwanciya na da alaƙa da ƙaranci ko rashin gudanawar jini a sassan jiki sakamakon matsi, nauyi ko danniya daga kwanciya, kamar yadda dukan sassan jiki suka dogara da gudanawar jini domin oksijin da sinadaran abinci da magani.

Ƙaranci ko rashin gudanawar jini a wani sashin jiki na 'yan awanni zai sanya kwayoyin halittar jiki su fara mutuwa. Saboda haka ne, sai fata ta fara lalacewa har ta fashe ko ta ruɓe.

Har wa yau, danshi, lema ko tirjiya a makwanci na daga cikin abubuwan da ke ƙara hadarin samun gyambon kwanciya.

Fatar jiki ita ce garkuwar farko domin yaƙar cutuka a jikin ɗan Adam. Idan fata ta fashe, to kowace irin ƙwayar cuta na iya shiga jiki cikin sauƙi. Saboda haka, bayan wahalar biƙin gwambon kwanciya, akwai mummunan haɗarin harbuwa daga ƙwayoyin cuta iri-iri.

Sau da yawa, matsalar harbuwa da ƙwayoyin cuta daga gyambon kwanciya, ita ce ke lashe rayukan majinyata saɓanin larurar da ta fara kwantar da su.

Kimiyyar lafiya ta bayyana hanyoyin kiyaye faruwar gyambon kwanciya. Hanyoyin sun haɗa da: tsabtar jiki, kawar da danshi ko lema da kuma jujjuya majinyaci duk awa biyu. Wannan hikima ta bayyana ne a wajen ƙarni na 20 a likitancin zamani.

Amma wannan hikima ta jujjuya majinyaci, tuni Alƙur'ani Mai Tsarki ya yi bayaninta kimanin shekara 1,400 da suka shuɗe.

A Suratul Kahfi, Allah ya ba da labarin "mutanen kogo", waɗanda Allah ya sanya wa bacci har tsawon shekaru 309. Inda Allah ya bayyyana wata hikima ta adana jikinsu ba tare da sun lalace ba tsawon waɗancan shekaru. 

A Suratul Kahfi, a wani ɓangare na aya ta 18, Allah ya ce,

 وَنُـقَلِّبُهُمۡ ذَاتَ الۡيَمِيۡنِ وَ ذَاتَ الشِّمَالِ​​ 

" ....kuma Munã jũjjaya su wajen dãma da wajen hagu,...."

Allah ya ce Shi Yake jujjuya su saboda mai bacci yana jujjuyawa amma bai san yadda ko sa'ad da yake juyawar ba. 

Duk da cewa Allah Mai Iko ne ya adana jikinsu ba tare da jujjuya su ba. Amma saboda Ya nuna mana cewa jikin ɗan Adam ba zai zauna lafiya ƙalau ba ba tare da ana jujjuya shi ba.

Ta amfani da wannan hikima ne, likitoci da ma'aikatan jinya suke ba da shawarar jujjuya majinyaci duk bayan awa biyu, musamman wanda ke fama da larurar da ba zai iya juya kansa ba.


Jujjuya majinyaci duk bayan awa biyu zuwa ɓangarorin jikinsa zai taimaka wajen:

1. Kiyaye gyambon kwanciya.

2. Rage ciwon jiki da gaɓoɓi.

3. Daskarewar jini a cikin jijiyoyin jini musamman a ƙafafu, da dai sauransu.

Daga ƙarshe, ga duk majinyacin da aka kwantar a asibiti, zai fi kyau ma'aikacin jinya ko likitan fisiyo su kula da jujjuya shi, ko kuma su nusar da masu zaman jinya su riƙa jujjuya shi domin guje wa afkuwar waɗannan matsaloli.

Za ku iya duba wasu ƙarin hotunan gyambon kwanciya a sashin tsokaci (comment section).

Source: Physio Hausa

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post