Kungiyar kwallon kafa ta mata na kasa da shekaru ashirin ta Nigeria ta lallasa kasa Korea da ci 1 da nema wanda Esther ONYENEZIDE ta saka kwallon a raga a minti 83 da taimakon OKWUCHUKWU.
Idan za a iya tunawa, a satin da ya gabata ne Falconet suka lallasa takwarar su ta kasar Faransa da ci daya da nema wanda hakan ya basu daman yin nasara har sau biyu a matakin rukuni.
A rukunin C, Nageriya ita ta daya da maki 6, sai Korea da ta ke biye ma Nijeriya da maki 3 sai kuma Faransa da Canada Wanda basu da maki ko daya inda suke matakin na 3 da na 4.
Najeriya dai za su kara da takwarar su ta kasar Canada ne a wasan karshe na rukuni daga bisani sai wasan mataki na gaba
Tags
SPORTS