Antony ya ci kwallo daya a wasan sa na farko - The Voice Online Nigeria

 

Antony ya ci kwallo daya a wasan sa na farko - The Voice Online Nigeria

Idan Za a tunawa, Ranar 31 ga wata Agustan 2022 ne kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kammala ciki da siyan Dan wasan gefe na kungiyar kwallon kafa ta Ajax wato Antony tare da me tsaron raga na kungiyar Newcastle United, Martin Dubravka.

Dan wasan mai shekaru 22 yayi atisaye ranar juma'a tare da sauran 'fan wasan kungiyar.

Dan wasan ya kasan ce haziki wanda ya taka rawar gani a kungiyar kwallon kafa ta Ajax wanda ya bada gudunmawa sosai.

Yau 4 ga watan Satumban 2022, Antony ya fara buga ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wasa wanda shine Dan wasan da ya fara saka kwallo a raga kafin a tafi hutun Rabin lokaci.

Bayan dawowa saga hutun rabin lokacine kungiyar kwallon kafa ta Arsenal itama ta saka kwallo daya a ragar Manchester, wanda ba dadewa Marcus Rashpord ya kara saka kwallo ta biyu da ta uku.

Wasan da Manchester United ta lallasa Arsenal ci 3-1 a gidan Manchester United (Old Trafford).

Wannan Nasara ya ba Manchester United daman kasancewa a mataki na 5 da making 12 a tebur na premier League.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post