Abin da ke kawo cigaban ko wacce Al'umma sune ababen more rayuwa kamar hanyoyi, makarantu, gadoji, asibitoci, da sauran su, tare da samarwa matasa aikin yi.
Al'ummar Saulawa da na Janmarmara sake karamar hukumar Ikara sun bukaci Gwamnatin jira Kaduna da ta gyara musu hanya da gadar da ta hada wadannan garuruwa biyu wanda hakan na kawo masu koma baya a harkokin su na yau da kullum.
A zantawar da mukayi da wani mazaunin garin wanda ya nemi da a boye sunan sa, ya shaida mana cewa suna matukar shan wahala wajen tsallaka wannan gada musamman idan anyi ruwa.
"Duk lokacin da akayi ruwa sai mun jira ruwan ya wuce sannan zamu iya wucewa domin zuwa wajen aiki ko makaranta" Inji shi.
Ya kara dacewa, "mafi yawancin mazauna wannan gari manoma ne, rashin hangar yana kawo mana koma baya musamman wajen kai kayan gona kasuwa".
"Muna kira ga Shugaban karamar hukumar Ikara, Hon. Dr. Ibrahim Salihu, da Gwamnar Bihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa'i da basu ruwa da tsaki su taimaka su gyara mana wannan hanya tare da gadar."