Daudar Gora book 2 page 62

 

Daudar Gora book 2 page 62

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (62)

........Tofa dan-dan-dan, da alama dama irin wannan damar Iffah ke jiran samu, dan cikin ƙanƙanin lokaci duk da darene masarautar ta ɗauki ɗumi, yayinda aka kwashi Ameera Haifah da Jasrah zuwa asibiti, Miran Arshaan kuwa da jikinsa ke tsumar tsoro gaba ɗaya ya gama gigicewa, dan sai zuwa yanzu ya dawo a hayyacinsa. Tuni kuwa ya tsure da ganin abinda ya aikata, sai kawai ya ɓige da borin kunya. Sudai jami'an babu wanda yace da shi komai, sun tattara komai akan sai zuwa da safe za'a kai maganar ga Shahan-shan. Abu dai mafi ɗaure kai shine miye tsakaninsa da Ameera Haifah ɗin har haka a irin wannan tsohon daren, dan a ƙala fa ƙarfe biyu na dare kenan....


        ★★.....


  A lokacin da duk ake waccan dambarwar anan ta-ƙurya ce ke ganawa da manomin ganyayyakin shayin Shahan-shan. A cikin ɓadda kamarta ta ke, dan haka shi bai san wacece ba. Hasalima magana da Jazaa sukeyinta ita dai tana hakimce komai batace ba. Da farko yaso bijirewa, amma ganin wata lukutiyar jakkar kuɗi da zinare ga barazanar halaka zuri'arsa kuma tuni ya miƙa wuya akan an gama. Malikat Bushirat tai murmushin basawa ta ɗauke kanta. Kwalayen ganyen shayin da uwa ta kawo kan ya fara kaiwa sashen Shahan-shan ɗin kafin wanda zasu noma ya tsiro nan ma Jazaa duk ta ajiye masa su har uku.... ..


     Hummmm 🥱🚴.


        ★★......


      Zaune take bayan idar da sallar asuba, yanda ta ƙurama waje ɗaya ido zai baka tabbacin tunani take. Sai lokaci zuwa lokaci da takan saki murmushi, harda cusa kanta cikin ƙafafunta kamar mai jin kunyar wani da ke gabanta. Ta ɗan jima a hakan kafin ta miƙe kamar wadda aka tsikara idonta kan agogon ɗakin. Tasan yanzu kam yana Gym ne tunda har ya kai yanzu bai shigo ba. Itama tsaf ta shirya cikin kayan motsa jiki ta, sun mata matuƙar ƙyau da fidda ainahin surarta komai ɗam. Ɗan wani bana ta saka a kanta siriri kalar kayan sannan ta ɗaura takalma da ɗaura after dress saman sport wears ɗin. Shiru tai tana bin Gym ɗin data shigo da kallo, babu kowa komai ma a kashe yake, da alama banan yazo ba. Fuska ta ɗan ɓata da tura baki gaba, har zata koma sai kuma ta tuno randa ta samesa a can sama yana wasan takobi shi da Miran Arshaan. “Yes!” ta faɗa tana wani kashe ido ɗaya da yin juyi sannan ta nufi can cikin takunta na nutsuwa. 

     Shelanta sunanta da na'urar ƙofar tayi kamar yanda ta saba duk wanda zai gitta ta cikinta ya sashi dakatawa da jujjuya takobin ya juyo a hankali. Tuni hadiman wajen sun jujjuya bayansu sukam. Yanda take takowa garesa kamar wata tarwaɗa yasa shi gagara cigaba da abinda yake yi.

          “Good morning ”.

     Ta faɗa cikin rashin tsoron nan nata na bayyane tana ɗaura yatsanta saman tsintsiyar hannunsa ta zano a hankali ta dire kan ƙyaƙyƙyawar takobin da ya riƙe riƙon ƙasaita da ƙwarewa. Da kallo kawai ya bita batare da ya amsata ba. Itama sai bata nuna tasan yana kallonta ba ta zare takobin a cikin hannun nasa fuskarta da murmushi. ƙin sakar mata yay, sai ma cike da salo yay wani irin juyata bata ankara ba ta dawo saman jikinsa takobin a wuyanta sai dai bai ɗaura a kan fatar jikinta ba. Iffah jitai fitsari na neman kufce mata tsabar yanda ta tsorata har yana jin yanda jikinta ke tsuma. Ɗan duƙowa yay kansa a kafaɗarta bakinsa saitin kunnenta ya furta, “k takamarki tsokala ko?”.

     Idanunta da ke kawo ƙwalla ta shiga ƙiƙƙifatawa da girgiza mata kai a hankali. Cikin rawar harshe ta ce, “Eshaan Akhi na tuba”. 

       “Daga baya kenan”.  

    Ya faɗa yana ƙara matsar da takobin jikinta gaf. Sake tsurewa tai. Shiko sai faman danne dariya yake. 

     “Ki fanshi kanki”.

   Da sauri ta ce, “Da mi?”.

Ɗan lumshe idanunsa yay ya buɗe yana mai busa mata numfashinsa a wuyan. A ɗan salon taɓe baki ya ce, “Komai ma”.

        “Shike nan, shike nan naji na amince, amma dan ALLAH ka janye sau ɗaya da ake mutuwa rai ɗaya ne”. Yanzu kam kasa daurewa yay sai da murmushi ya suɓuce masa. Ya janye tare da ɗauke hanunsa dake saman cikinta ya juyota suna fuskantar juna. Hawaye fa da gaske sun cika mata idanu. Da ƙyar ya iya gimtse dariyarsa. Idanunsa ya maida ga hadiman wajen da suka juya bayansu tun ɗazun, ɗasss ɗasss yay da yatsunsa sau biyu, cikin abinda baifi sakkani ba sun bar wajen a ka barsu su biyu. Da baya-baya yaja zuwa table ɗin gefensu kaɗan, wata takobin ya ɗakko a cikin ƙyaƙyƙyawan kufanta ya dawo gabanta, hanunta ya riƙo ya ɗaura mata takobin sannan ya zare abayar ta ya ajiye tare da mata alamar bismillah. Kamar ba ita ta gama haɗiyar hawayeba yanzu ta wani dubi takobin shima ta dubesa ta ɗan murguɗa baki.

     Kansa ya maida gefe yana murmushi, ta re ajiye tsinin tasa takobin bisa ƙasa ya fara zagayata. Yana a tsaye daga bayanta ya juya takobin cikin salon tsokanarta kawai a bazata yaji tama kanta garkuwa. Idanu ya ɗan waro waje, da bin takobin da kallo kawai ta zuƙe ta maida masa hari. Cikin zafin nama ya kare kansa shima mamakinta na nan kasheshi. 

       “Dama kin iya wasan takobi?”.

    Ya tambaya da mamaki idanunsa cikin nata. Murmushi ta sakar masa da ƙara zuƙewa ta kai masa suka ta ƙasa. Nanma baya yay cikin zafin nama yay wata irin bahaguwar zuƙewa. Dariya tayi da dire takobinta ta fara zagayashi kamar yanda ya mata ɗazun, cikin salon ɗage gira da kashe masa ido ɗaya ta ce, “Zaka cigaba da tsayawa tambayar a ina na iyane na kaika ƙasa?”. Tsaiwarsa ya gyara da ƙyau yana murmushi da kamo lips ɗinsa na ƙasa ya tura cikin baki suka cigaba da zagaye juna. Sai kuma kowa ya yinƙuro cikin ragabza akai tsaiwar zakaru. Cikin ƙwarewa da nuna bajinta ga kowa suka cigaba da wasan mamaki na nan kashe Tajwar Eshaan a zuciya. Duk da ya fita ƙwarewa yanda ta iya ɗin itama na bashi mamaki matuƙa. Sai dai ya bita da salon saffa-saffa yanda bazai cutar da ita ba dan ƙarfinsu ba ɗaya bane......

    

        Tamkar wanda aka jeho kawai sukaji sallamarsa a kusan tsakkiyar wajen, dan kamar sai da ya matso gab da su ne ma yake sallamar. Da ga shi har Iffahn juyowa sukai, musamman Iffah da kamar wadda ta ma firgita, dan jikinta har rawa yake wajen neman abinda zata yafama jikinta, tsabar yanda ta rikice tama ƙi ganin after dress ɗin nata. Bata san yanda akai ba, tayaya ma kawai jinta tai a jikinsa,  jin ƙamshinsa ya sata ƙanƙamesa da sauri tana ƙoƙarin ɓoye kanta. 

        “What's wrong with you? Get out of here Aam!!” ya faɗa a matuƙar tsawace shima yana ƙanƙameta da juyawa da ita suka bama Miran Arshaan da yay mutuwar tsaye baya. 

      “I say aut!!!”.

    Ya sake faɗa da wata irin mummunar tsawar mai ƙaraji da har jikinsa na girgizawa, ga idanunsa sun yi wani irin kaɗawar masifa kamar wanda ake kaɗama gangi. Miran Arshaan har tuntuɓe yake yi tsabar firgicewa da tsawar Tajwar Eshaan ɗin. Bai taɓa sanin yaron nan ɗan bala'i bane irin yau. Next surar yarinyar nan ta matuƙar kidimashi, ashe abinda Jasim kenan ya gani kullum yake cikin sambatu da santin yarinyar, shi manemin matane tun yana da ƙananun shekaru, yayi mu'amula da mata ƙabila daban-daban a duniya da bai san adadi ba. A sanda yake ji da rashin ji har order ɗin mata suke ta online, yaga matan ma da sukafi Iffah ƙira amma wannan jikin dabanne. Ji yake yama kasa cigaba da tafiyar yanda jikinsa ke ɓari, sai kawai ya samu bango ya manne yana sauke numfashi gudu-gudu. (Humm)              

       Yanda Iffah taji zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri kamar zata ɓallo ƙirjinsa ta fito ga tsawar da yayma uncle ɗin nasa ya matuƙar sake ruɗar da ita fiye da tsoron ganinta a yanda take da tai gudu. Kanta ta shiga jujjuya masa da ƙanƙame hanunsa, sai kuma ta ɗan ɗago ta kalli fuskarsa. Ta wani irin kaɗawar masifa jazur hakama idanunsa gaba ɗaya sun juye mata cikin canjawar kammani. Dole ta maida idanunta ƙasan jikinta na rawar tsoro da yanayin nasa. Jitai kawai ya wani irin fisgar hanunta zuwa hanyar ƙofar da ta shigo, bai tsaya da ita ko ina na sai cikin bedroom. Yarfar da hannun yay yayi shigewarsa bathroom. Da kallo ta bisa hankalinta a tashe itama, dan ita kaɗai tasan kalar wutar masifar data gani a cikin idanunsan. Raya mata zuciyarta ta dingayi kawai tabar ɗakin nan karma ya fito ya sameta.....

      

      Koda ya fito bayan tsahon lokaci da ya ɗauka a bayin bai nema Iffah ba dan yana buƙatar shiga ɓacin rai, shi mai kishi ne, tabbas yanada matuƙar kishin da yakeji akan yarinyar nan zai iya ɓadda mutum. Wata irin tsanar Miran Jasim da Miran Arshaan yakeji irin wadda bai taɓa ji a kansu ba a dukkan abubuwan da suka aikata masa a baya, ga wani irin sara masa da kansa yake yi na ciwo. Jikin window ya ƙarasa hannunsa goye a bayansa batare da ya cire ko bathrobe ɗin jikinsa ba yana kallon sararin samaniya da ke haɗa wasu irin manyan bakaƙen giza-gizai na hadari, duk da safiyar tayi sosai garin yaƙi washewa sai ma rinewa yake sake yi kamar za'ai wata sabuwar magriba. Kiran waya ne ya shigo, ya share kamar bai jiba, aka sake kira nan ma kamar zai share sai kuma ya nufi wayar a fusace ya ɗaga. Sai dai yay shiru baice komai ba. Da ga can Sayeed Fayzul-haq ya gaishesa cike da girmamawa. Haushin kowa yake ji, duk da bashi yay lefinba ya samu rabonsa. Dan maimakon amsa gaisuwa a dake ya ce, “Ya akai”. Ɗan rikicewa Sayeed Fayzul-haq yayi, amma sai cikin dauriya da sake ƙanƙan da kai ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa tsakanin Miran Arshaan da Ameera Haifah tun a daren jiya. A zafafe ya ce, “Kaima jami'ai magana su kamashi a haɗashi da ɗayan sakaran, a saka na'urar ɗaukar magana. Itama Haifah ɗin Doctors su sallameta idan babu wata matsalar data shafi lafiayarta jami'an tsaro su rufeta”. Daga haka ya ajiye kan wayar yana huci. Duk yanda yake ƙoƙarin riƙe kansa da bin komai a sannu ya fahimci ba haka maƙiyansa suke buƙata. Fushinsa suke son gani, ainahinsa suke buƙatar ya nuna musu. Ya barsu da yarinyar nan ne kawai domin shi ɗin shugaba ne, shugaba kuma da haɗiyewa aka sansa, amma tunda so suke shi ya fito musu a Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ɗin sa to yanzu ne wasan zai fara........✍️


       _😆🥱TOFA ran ƴan maza ya ɓaci, al'ummar ƙasar ruman kuyi takanku mai RUMAN ɗinne da kansa ba aike ba🚴🚴._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post