Daudar Gora book 2 page 61

Daudar Gora book 2 page 61

 DAUDAR GORA…..I

Book 2

Chapter: 61


Tunda suka shigo idanunsa kyam a kansu, yana zaune a falo zama na kasaita da izza da jiran ta inda zata bullo. Tun bayan dawowarsa sallar isha'i ya duba bai ganta ba. Shegen miskilanci ya hanashi tambaya har sai bayan kusan awa daya sannan ya bincika ta cctv camaras. Anan yaga fitarta harma da nufar sashen Malikat Haseenat ita kadai ko tsoro babu tattare da ita duk da darene. Yayi tsammanin zuwan bamai jimawa bane, amma sai gashi har yay wanka yaci abincin dare yay yan ayyukansa babu labarinta, harya kwanta da tunanin zai iya shareta sai hakan ya gagara, gangar jikinsa da zuciyarsa suka tabbatar masa bafa zai iya rayuwa babu mahadinsa ba. Shine ya dawo falo yay zaman jiran ganin ta inda zata bullo kusan awa daya kenan.


Gaba daya sai Iffah taji ta tsure da kallon nasa, dan haka ta koma da baya-baya ta labe a bayan Malikat Haseenat. Idanunsa ya dauke daga kanta ya maida ga Malikat Haseenat din shima. Cikin dan motsa lips dinsa ka dan ya furta, "Barka da dare Jaddah".


Amsa masa tai cike da kulawa, tare da juyawa ta kamo hanun Iffah da ke labe a bayanta ta maidota gabanta. "Ga matarka nan tane tare dani tun dazun, ALLAH ya tashemu lafiya". Daga haka ta saki hannun Iffah ta gara kekenta ta nufi Elevator.


'"ALLAH ya huta gajiya". Ya fada a hankali yana dan lumshe ido da risinar da kansa alamar girmamawa a gareta. Shiru falon bayan tafiyarta babu wanda ya sake kwakwkwaran motsi. Shi ya

zuba mata idanun nan nasa masu kaifi, ita kuwa tana tsaye a inda Malikat Haseenat ta barta kanta a kasa tana wasa da yatsun hanunta, tsigar jikinta sai yamutsawa take dan har cikin jininta takejin tasirin kallonsa a kanta. Sun kwashi mintuna masu dan tsaho a haka kafin ya mike, gabanta yaje ya tsaya, ta rumtse idanu da karfi a tunaninta saukar mari ko wani abu dai mara kyau zata ji daga garesa. A mamakinta sai jin tattausan tafin hannunsa tai a saman nata ya zare jakkar hanunta, cikin takun nan nasa daddaya cike da izza ya rabata ya wuce.Numfashin da ta rike a kirji da makoshinta ta saki da karfi, sai kuma ta bude idanunta tabi bayansa da kallo har ya bace ma ganinta. Dan tarin dake neman rike makoshinta ta fara, dole ta nufi dining room ta samu ruwa ta sha. Daga haka takai zaune tana sauke numfashi. Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta tashi tabi bayansa tana addu'a a ranta.



Bata da tabbacin a inda yake, dan haka kawai ta nufi inda zuciyarta ke raya  mata  da fatan ALLAH yasa ba'a nan din yake ba. Sai dai kuma da alama ta taki rashin sa'ar. Dan tana shiga taci karo da shi zaune a kan gado da lap-top kan cinyarsa. Dakin babu haske mai karfi, sai hasken screen din laptop dinne ya haske kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar kamewa da

kwarjini. Sum-sum ta wuce hanyar bathroom tana dan turo baki. Sai da ta gama tsaftace kanta ta fito cikin bathrobe, yana a yanda ta barsa, hakan sai ya bata damar tsayawa ta bayansa ta shirya cikin kayan barci masu dan kauri da turarruka. A take kamshin dakin ya sake karfi. Fahimtar kamar fushi yake ya sata takowa inda yake cikin sanda, zaune takai gefensa amma ya share abinsa bai ko nuna ya san da zamanta ba. Cikin dan bata fuska da jin haushi sharetan da yay ta zame ta kwanta tare da dan ture lap-top din tasa kadan ta daura kanta a cinyarsa ta kwanta. Da kyar ya iya cigaba da rike kansa yaki kulata. Ganin ya cigaba da aikin dai ya sata kurama fuskarsa idanu, sai kuma ta kai hanunta kan kwantaccen gashin kumatunsa ta fara masa tafiyar tsutsa. (@) Yarinyar nan da tsokale-tsokalan masifa kike * ). Yayi kokarin ganin ya danne ya cije amma aikin na neman gagararsa, baima san sanda ya cije lips dinsa da rumtse idanunsa da dan karfi ba.


" ALLAH kayi hakuri bazan sake ba.ALLAH  banyi zaton zan dade ba na samu Mammy batajin dadi ne fa".


(Yarinyar nan sai ta kasheni zata huta) ya fada a zuciyarsa dake faman bugawa da sauri-sauri cikin kaikawo. A hankali ya janye hannayensa dake sarrafa lap-top din ya daura na damar kan nata dake cigaba da shafa fuskarsa. Rikesa yay yana kokarin son gain ya janye amma sai tai wani irin juyi ta maida fuskarta saitin cikinsa ta sakalo dayan hanun nata a bayansa ta kankamesa.


'"Kasheni kawai ki huta" ya fada cikin subutar harshe jikinsa na saki gaba daya.


      Iffah da bata fahimci ita mima yake nufin ba ta kyalkyale da siririyar dariya har yana jin dumin numfashinta a kan Fatar cikinsa. Ita a nata shirmen kankamesan da tai ne yaji zafi. "dan na kasheka dawa zan zauna?". Ta fada cikin dariyar tana kara cusa kanta jikinsa. Dole ya ajiye lap- top din ya kai kwance tare da dagota gaba dayanta ta hau saman jikinsa. Fuskarsa take kallo cike da dakewa kamar yanda shima yake kallon tata idanunsa a shanye. "Miyasa baki son a zauna lafiya?". Ya fada a hankali yana sake kankance idanunsa cikin nata. Idanun ta juya tana shagwabe fuska da dan cuna masa lips dinta. "Toni mi nayi? In dai zuwa wajen Jaddah ne ai nace kayi hakuri".


Dariya maganar ta bashi amma sai ya gimtse baiyi ba, ya dan tabe baki da tsatstsareta kaifafan idanunsa. Cikin dan dage gira

"Har na kai ki?".


"Hu'um, ni a suwa kuma, kana kallon kanka a mirror kuwa da kyau?. Badan kar ace nayi karya ba sai nace kafi kowa kyau a kasar ruman". Harga ALLAH ta bashi matukar dariya yanda ta fadi maganar cike da yarinta, yayinda zuciyar sa tai wani irin shiga farin ciki, domin kuwa bawai yafi kowa kyau din bane kamar yanda ta fada a zahirance, ya fahimci ta fara caukar karatunsa son sa ya fara shiga zuciyarta. Domin abinda kake so ne kawai kake ma kallon kasancewarsa a sama dana kowa. Shi kansa duk da yasan akwai kyawawan da suka fita ganinta yake samada kowa saboda kawai ita kadai yake so,kyawuntane kawai ke kayatar da shi. Bai fahimci murmushi yake ba sai da yaga yanda ta kura masa ido. Ya dan waro idanun waje alamar miye kuma, ita kuma sai ta girgiza masa kai tana murmushi da dan kauda idonta dake cikin nashi."Murmushi na maka kyau, gashi kuma baka son yi".


Hannayensa duk biyu ya doro a saman bayanta ya sake matso da ita ta kwanto jikinsa sosai, fuskarsu ta koma gab-gab har hancinsu na gogar na juna. "A komai k ta dabbance my sohaa".


"Kaima haka ai".


Ta fada tana dan sumbatar lips dinsa, sai tai saurin jan jikinta zata sauka dan sai da tai babban kokari wajen masa kiss din, amma kunya take ji. A hankali ya rikota bayan ya fisgo numfashinsa da ya nema kufcewa da kyar.Mirginasu yay suka koma saman hannayensu suna fuskantar juna, batare da jiran wani abu ba ya manne lips dinsu waje guda..






🥱🏃‍♀️Anfi karfin alkalamina anan.








       Babu alamar wasa tattare da shi, da ga tsayen da yake a kofa yana dubanta a yatsine ya ce,"Kifadi abinda zaki fada ina jinki, dan bazan wuce minti ashirin ba anan".


    Rai bace Ameera Haifah ke duba Miran Arshaan mai maganar, tai karamar kwafa da tabe baki," Arshaan kenan, idan kana ganin Kanada mafitar da zata iya kwabemin ne ma,dan har da kai sai dai ka shirya mu duka zata kwabe Dar harda kai, idan har ban tsira ba da ga yarda ka maida Jasim kaima zan bude maka aiki ne. Zan kuma tabbatar maka na fika iya makirci dan mace sunana idan ka manta".


"hhhhahh! Ni kike tunanin zaki iya budema aiki Haifah? to ina baki shawarar fita a hanyata da ga yau, in ba hakaba why zan kasheki na binne gawarki a cikin masarautar nan kuma na kashe banza".


 "Oh really? To Dan ALLAH ko zaka gwada ne? Nace ko zaka gwada kashenin muga!!!". 


Tai maganar cikin tsananin hargowa tana wani hahhankada kirji a gabansa. Wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa nayi, dama a wuya yake, a fusace ya kaima wuyanta wani irin shegen shaka na tashin hankali. Cikin kankanin lokaci manyan idanunta suka sake yowa waje ruku-ruku, ga kakarin mutuwa da ta fara da mutsu-mutsun ganin ta fisge hannunsa da ga kan wuyanta. Sai dai kuma hakan ya gagara, dan karfinsu ba daya ba. Tafiya ya dingayi da ita cikin rufewar ido har jikin bango, ya kara matse wuyan da karfi tare da wajigata ya buga kanta jikin bango. Wata irin wahalalliyar kara ta fasa da ta jawo hankalin Jasrah dake daki kwance ta farka tana nemansa, dan su suna'a falon baki ne kasancewar cikin shigar badda kama Ameera Haifah tazo a nufin bako tasa amintaccensa imata iso saboda baya daga mata waya yanzun. Sai da yazo yaga itace. Gaba daya idon Miran Arshaan da alama ya rufe, dan tuni ya sake jijigata ya buga a bango, jini ko ya samu hanya ya balle.


lya karfi da budewar murya Jasrah ta daddage ta kwalla wata irin kara na firgita, dan ganin jini ya wanke fuskar Ameera Haifah ga Mijinta shake da wuyarta sai ta dauka ta mutu.Wani irin wancakalar da Haifah Miran Arshaan yayi yana duban Jasrah data yanke jiki ta fadi. Har rige-rigen shigowa hadiman masu tsaron sashin keyi, ganinfa abinda ke faruwa tuni wani ya firgita ya kyalla a guje ya sanarma jami' an tsaron gidan dan wannan faninsu ne...✍️

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post