Daudar Gora book 2 page 65

Daudar Gora book 2 page 65

DAUDAR GORA 

Book2

Chapter: 65


A gajiye tibis ta shigo sashen, yana zaune a falo harde kamshinsa ya karade falon. Da sauri amintaccensa da ke gefen kafafunsa zaune da ga kasa yana ware masa wasu takardu da suka barbaza ya sake kasa da kansa yana gaisheta.Da hannu ta amsa masa idonta akan zakinta da ke mata kallon kasan ido ta yanda ita kawai ke fahimtar hakan. A hankali ya motsa lips dinsa ya Bama amintaccensa umarnin tafiya. Zaram kuwa ya mike dan dama abinda yake jira kenan. Saboda a yanzu kam shigowarsa wannan falon sai da notis saboda yanda iyayen gidan nasa ke manne da juna akoda yaushe suna baje kolinsu yanda suka gadama. Shifa har mamaki yake da jin anya kuwa ba'a samu canji da ga Shahan- shan din nasu ba zuwa waninsa. Shifa yasan abinda yake gani kawai.

   

       A hankali ya bude mata hannayensa alamar tazo garesa idanunsa kyam akan kyakykyawar fuskar ta dake a shagwabe kamar zata saki kuka. Kafada tadan noke tana tura baki, sai kuma ta fara takawa a hankali zata wucesa, a hankali ya riko hanunta da dan murmushin iya lips din nan nasa. Gaba dayanta ya jawo ta fado jikinsa. Wani irin sakin ajiyar zuciya sukai a tare.Tare da rungume junansu tsam-tsam kamar masu tsoron a rabasu.

 

   K ta dabance".


    Ya fada a hankali cikin kunnenta yana sake kankamta.


       "Kai ne na daban a cikin daban ai Zakina". Ta fad itama tana sakar masa manya-manyan sumba a kan kirji. Sai kuma ta dago kanta suka zubama juna ido cike da kewar juna kamar ba da safe suka rabu ba. Cikin motsa lips dinsa da kyar ya ce" "Kin gaji ko?".


     Kanta ta jinjina masa tana marairaice fuska, sai kuma takai hanunta kan kyakykywar fuskarsa tana shafa kwantaccen gashin wajen dan tana matukar son sa. "Amma tunda aikin lada ne banajin gajiyar". Dan sumbatar lips dinta yay a fisge ya ce, "Da gaske?"


"Yap".


    Ta fada cikin fari da kashe masa ido daya.Murmushi ya dan saki da lakace mata hanci, sai kuma ya maida bakin nasa kan nata ya shiga bata kyakykyawar sumba, ba' a barta a baya ba ta shiga taimaka masa cike da nuna kwarewar haddace dukkan karatunsa. Kafin akai wani dogon labari gaba daya yanayinsa ya canja. Dan shifa Tajwar Eshaan bai san wani yaren dandani haukaci ba. In har aka fara sai an kai karshe.Sannanake iya samun kansa dari bisa dari kuma dalibar tasa da alama dai irinsa ce, dan zuwa yanzu duk da ta kasa zama mai juriyar mika wuya yanda yake so saboda rashin sabo tana kokarta kamantawa musamman a bashi hadin kai a duk sanda yace kule takance cas. Da ga baya kuma ta dawo tana masa raki da shagwaba, Shiko yay ta mata murmushin miskilancin nan na..


      Bayan sun samu daidaito ta lallabasa yay mata kiran su Babiy, sun jima suna hirarsu dan a yanzu kullum ne sai ta saka ya kira mata su, sai dai kuma duk sanda za'ai wayar yana dakin, bai kuma taba yarda shi sun gansa ba ko tayi wata magana a kansa, tayi-tayi ya barta suna gaisawarsu ita bazatace komai a kansa ba yaki bata damar hakan, ya dai yarda ya kira mata su su gaisa suma jima suna hira yana da ga gefenta yana saurare da jin komai.


    Bayan sallar magriba ta samu sakon kiran Malikat Bushirat da ga wajensa. Dama dai suna da shirin zuwa mata sallama, dan insha ALLAHU ana kai azumin farko a gobe zuwa dare jirginsu zai daga zuwa Saudiyya. Sanin abinda ta kullama ranta tace ya barta to ta fara vin gaba yazo da ga baya tunda zaije ya ma Malikat Haseenat ma sallamar, ita kuma da safe Insha ALLAHU sai tayoma su Malikat Haseenat din sallama. Bai wani kawo komai a ransa ba yace taje, dama yana bukatar yin magana mai muhimmanci da Mammah din kuma akantane baya kuma bukatar taji.




       Tunda ta fito a mota hadimai ke fama zubewa gaisheta. Kafin ma ta karasa ciki an kaima Malikat Bushirat labarin zuwan nata. A zahirance dai batace komai ba har Iffahn ma ta karaso. Gaba daya hadiman dake zagaye da ita ma wani irin zubewa sukai bisa gwiwunsu lokaci guda, dan wani irin kwarjini Iffah'r ta musu naban mamaki, sannan koba komai ita din dai Zawjata-almilk ce. Hannu kawai ta dan daga musu dai-dai tana kaiwa cikin kujera da wani irin salon zaman kasaita na kafa daya kan daya. A hadiman babu wanda bai girgiza da salon Iffah'r ba, dan kowa yasan duk da take matsayin Zawjata-almilk a gaban Malikat Bushirat dole ta risina kuma kasa ne wajen zamanta. Sunta satar kallon Malikat Rushirat din da tunanin ko zatace abu, amma sai sukaji shiru, hasalimal sau daya bata motsa da ga zamanta ba balle a karanci wani abu da ga gareta.


       Wani irin kallo Iffah ta watsa musu da masu alamar fita da yatsunta. Har ko rige-rigen fitar suke duk da sun so ganin yaya wasan zai kare. Falon ya dauki shiru na tsawon lokaci batare da wani cikinsu ya motsa ba, hasalima ita Iffah ta maida hankalintane ga wayar Tajwar Eshaan da ke a hannunta tsabar rainin hankali ma browsing abu takeyi hankalinta kwance kamar ta manta gaban wanda take. 


    Malikat Bushirat ta dago idanunta da sukai wani irin kadawar bacin rai ta zuba mata, tsahon sakanni kafin ta nisa da kyar cike da zafin rai. "K har kina ganin kin kai wani matsayin da zaki iya jayayya da ni kenan?".


      Duk da sarai Iffah ta jita sai batako motsa ba tsahon wasu sakanni. Kafin ta motsa lips dinta batare da ta daina abinda take a wayar ba ta ce,"naga ai bakya bukatar amsa tunda har kin fahimci hakan Mother in-law. Kuma duk abinda kikaga Iffah tace zatayi sai ta yishi ki rubuta ki aje, dan hakan halitata ce bana manta gabar daukar fansa musamman akan jini na".


      "Humm ki taka a hankali, na fiki hatsabibancin yariya. Ki kama kanki kodan cigaba da rayuwar ahalinki a doron kasa".


     14:24

cigaba da rayuwar ahalinki a doron kasa".


*murmushi mai sanyi Iffah ta saki tare da dagowa ta dubeta ido cikin ido. "Barazana ne hakan in-law? To in barazana ce ki sanarma bokanyar taki bata iya aiki ba tunda har bata sanar miki ahalin Iffah sararin samaniya ne ba ganinsu sai da ga nesa akan yaro da babba. Ki fada min miyasa kika kirani da ina da yan ayyuka a gabana masu muhimmanci, idan kuma kin kirani din ne dan kawai ki jajjadamin karfin ikon naki da kasancewarki damisa da bata da banbanci da damisar takarda a wajena to".


      Ba karamin dukan zuciyar Malikat Bushirat kalmar (Bokanya) nan yay ba, dan maganganu ma da suka biyo baya sam bata jisu ba ko fahimtarsu, amma sai ta dake ta basar kamar shima bataji ba. Sai tama saki wani murmushin kasaita cike da izzarta tana ma Iffah'r kallon ke karamar kwaruwa.


        "Bazan hanaki wasa da Zakanya ba, koba komai zan ajiye darasin da zai zama izna ga yan baya gareki yarinya. Ina son sanin dalilinki na shiga hurumin da ba naki ba kan shiga bital mali ki fidda kayan azumi".


      Dan murmushi Iffah tayi yanzu ma, sai kuma ta ajiye wayar hannuta ta sauke numfashi mai nauyi. "Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan iya sa ki rissina ji inki ta zama sarauniya bisa karfin ikon Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki. Bana son cigaba da jayya da ke ko nuna karfina akan karfin ikonki da har mutane zasu kalla gazawarki ko kaskancinki a cikin idanunsu saboda daraja. Eh tabbas daraja, darajar abinda kika haifa ya zama mai daraja a cikin al'umma badan yafi kowa ba a wajen ALLAH ko ke da kika haifesa kinfi wani. Ammie why inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci. Sai dai bazanyi hakan ba, bazanyi ba saboda mutunci da kimar danki har sai in kin bijirema hanyar da nake son ki dawo. Kwana biyar da suka wuce naci karo da bakon ganyen shayi mai hadari matsayin wanda Shahan-shan zai sha. Na kuma cin karo da madara itama, dana bincika sai na gane da ga sashenki madarar take, ba kuma na raba dayan biyu shima ganyen shayin naki ne. Na gagara fahimtarki ko inda kika dosa a zahirance. Kowa dai ya kalla fuskar Maleek da taki basai ya sake kallo ba yasan jininki ne shi,dan kamminku a bayyane suke ta abubuwa masu yawa. Kema a karan kanki kin fada kin kuma maimaita shi din danki ne. To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar. Na rasa mikike nema? Mikike bukata? Mi kekike son zama bayan abinda kike a yau dinki da har in kika rike zata jagoranceki zuwa gobanki cikin salama kamar yanda Jaddah take a yau ga kowa". Taja numfashi mai nauyi tare da dafe kai cikin kunar rai, sake dagowa tai tamkar bataga kallon wutar bala'i da tsanar da Malikat Bushirat din ke binta da shi ba ta cigaba da fadin………✍️

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post