Daudar Gora book 2 page 66

 

Daudar Gora book 2 page 66

DAUDAR GORA 

Book 2

Chapter: 66


."UBANGIJI ya halicceki mace bayan akwai maza da yawa dake kwaikwayo son zama macen amma basu isa komawa ba. Ya halicceki kyakykyawa, bayan awai wasu da yawa da kyawun da bai kai naki ba suke fafutukar nema ta hanyar sabama UBANGIJI suna amfani da abinda yace haramunne garesu. Ya baki lafiyar jiki babu ta inda kika nakasa. Bayan ga dubunki can su nakasar itace jarabawarsu. Ya baki lafiya

matsayinki na yar adam. Bayan ga dubunki can kwance a asibitoci da gidaje basu da kudin shan magani, masu kudin ma basu isa iya sayawa kansu lafiya ba koda sun kai karuna dukiya. Ya azurtaki cikin nagartaccen addini, bayan ga dubunki can na bautar wanin ALLAH cikin batan da su a karan kansu basu san bata bane ba. Ya azurtaki da tarin dukiya. Bayan akwai dubunki da abincin yini daya ma gagararsu yake ci saboda basu da kwabo na saya. Ya azurtaki a cikin katon gidan aure dana haihuwa, karkashin kyakykyawar nasaba bayan akwai dubunki da a kan titi ko cikin bukka suke rayuwa badan kin fisu ba. Ya azurtaki da karfin iko na mulki, bayan akwai dubunki da su wanna matsayin naki suke kwadayon kaiwa, ke wasu ace ma su din hadimanki ne kawai farin ciki yake sanyasu. Ya azurtaki da ilimin addini dana zamani, bayan akwai dubunki da suke zagaye da jahilci, wasu ko suna son karatun rashin mai tallafa musu Yasa suka hakura suka zama masu aikata miyagun laifuka koda zukatansu basa so, sai dai basu iya banbance abinda ya dace da wanda zai dace da tasu rayuwar. Ya azurtaki da da daya tilo tamkar da dubu da nagartaccen mijin da duniya bazata taba mantawa da su ba, bayan akwai mata da yawa da su jarabawarsu mazajen aurensu ne da yayan da suka haifa. Duk da ya miki wadannan abubuwane badan kinfi sauran halittun duniya ba. Badan bazai dandana miki mutuwa ba. Badan bazai iya jaraftarki ki kasance su ba. Badan kinfi karfinsa ba. Sai dan kawai ya miki talala har zuwa ranar da zaki tabbatar ke din bakomai bace a cikin komai. Ke din yar adam ce, yar adam din nan da aka halitta da ga yunbun kasa, yar adam din nan mai rauni, mai barci, mai kashi, mai ciwo mai jiran kwanakin mutuwa. Badan kiyi alfahari da duk wadan nan abubuwan ba kuma ya halicceki, ya baki su ne domin jarabawaki itace su, kamar yanda ya bama wasu sabanin naki domin jarabawa suma. Dan ALLAH mi kike bukata a bayan duk wadannan? Minene burinki da fatanki da fafutukar ki da har halaka rayuwar yayan wasu ke sakaki a farin ciki amma baki son ko kuda ya rabu daya naki tilo da sunan cutarwa? Ke uwa ce, ya kamata kiyi hasashen zafi da ciwon da zaki iyaji dan akace babu wannan tilon dan naki kafin idonki ya rufe ki zama sanadin hana wasu. Ni Fhareedah bint Zayyan b yafe daukar fansa ki shaida haka, bakuma zan gajiya da fada miki na, amma ke uwa ce ina mutuntaki da wanna matsayin, dan ba'a bani tarbiyyar raina koda wanda ya girman da kwana daya ba a duniya balle ke da nasan zaki iya haihuwar wanda ya haifan musamman ace Maleek mace yazo ba namiji ba. Sannan koba komai kin haifamin gwarzo kuma barden miji da tun kan bakina ya tabbatar da alfahari da shi gabbaina isarwa suke. Shi mutum ne adali, mai addini, mai yawan bautar ALLAH da mika masa lamuransa. Baya jin wani alfahari da matsayin da ALLAH ya bashi kamar ke face takatsantsan dan yana kallonsa a matsayin jarabawarsa. Akwai tarin abubuwa masu dunbin yawa da nake bincikawa akanki da alakarki da halaka yaran mutane, idan kikace zaki cigaba da bina da izzarki why why Ammie baza'a ganeki ba. Ki bini a sannu-sannu ni zan kaiki inda kike son zuwa bake zaki kaini ba. Kamar yanda ni na kawo kaina masarautar nan bake kika kawoni ba. Kamar yanda ni nai amfani da Arshaan da Jasim da Haifah basu sukai amfani da ni ba, ke shaidace kuma ga irin makomar da suka kasance duk da somin tabi ne ma na fara musu.Kamar yanda ni na bama Shahan-shan din da kike takamar da shi garkuwa bashi ya bani ba har kike hakilo da hura hancin wai ya janyeta gareni.Kin san ALLAH kiyi maza ki dawo hayyacinki ina tsoratar miki shiga jerin mutanen da zan kwancema zani a bainar nasi cikin Masarautar nan dank kuma ya musu hukunci, kiyi azamar ajiyewa ki labe bayan mutuncin danki hukuncina ya kasance tsakanin ni da ke ne kawai. Dan saura kiris a fara bankada, idan kuma aka fara akwai gagarumar matsala, dan na fahimci ke kanki har yanzu baki gama sanin wanene danki ba da ainahinsa, kinama rogo kallon kitsene kawai, sannan kina kallon kasurgumin Zaki ne da fatar mage" ta saki murmushi tare da takawa gabanta a hankali. Hannunta ta kamo ta daura saman cikinta, "Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law". Ta dan kyalkyale da dariya da sakin hannun, yako tafi yaraf alamar duk wata mahada mai motsi a jikin Malikat Bushirat din ba aiki take ba a yanzu. A hankali ta koma kasa kusa da kafafunta ta zauna, tare da hannu ta dago afar ta fara matsa mata. Zabura Malikat Bushirat tai kamar wadda aka kodama mari ko ta suma aka zubawa ruwan sanyi drum guda, sai hakan kuma yay dai-dai da shigowar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed. Yar dariya Iffah tai kamar bata san da shigowarsa ba ta cubi Malikat Bushirat din. "Ammie irin wannan zabura haka na sake tabo wajen da yay dayin kenan?".


     Idanun Malikat Bushirat ne suka sauka akan Tajwar Eshaan din dake takowa a nutse idonsa a kansu fuskarsa da dan sakewa. Sai dai kafin ta iya cewa komai da ga daurin goro ko makircin Iffah zatace mane oho Tajwar Eshaan din ya karaso yana dan gyaran murya. Dagowa Iffah tai ta kallesa har yanzu fuskarta da murmushi. Cikin yar shagwaba ta ce, "Yauwa ai garama da kazo, Ammie na nan zata kasheni da dariya, tace fa na matsa mata kafarta ya mata dan nauyi saboda zaman waje daya amma da nayi- nayi sai ta fara fadin ya isa a bari ta huta".


    Wani dan moso yayi iya lips yana dauke idanunsa da ga kallon da yakema Iffah'r na kasa-kasa ya maida kam Malikat Bushirat da mamakin duniya a makircin matsiyaciyar yarinyar ke neman dauke numfashinta. A hankali

cikin dan sanyin nan nasa da kamewa ya ce,

Ammie shiyyasa nace ki dinga motsa jiki tun last year, wannan zaman waje dayan da kuke ai ba gata bane, gashi nan shi ya kashema Jaddah kafafu anata fama".


   Da kyar ta iya dannewa ta dan saki murmushin karfin hali da yafi kuka ciwo ta ce.

  "To ya za'ayi Saiful-malik, mizamuyi da wani motsa jiki a wannan shekarun namu?".


    Kafin ya bada amsa Iffah ta amshe da fadin, "Ai Ammie kike da motsa jiki kuwa, dan motsa jikin nada amfani sosai, kuma ya kamata ko dan cikin badda kama kuna fita kwamaga yanda talakawan kasa ke yan sabgoginsu, sannan koba komai ai hakama karin imani ne da lafiyar jikin harma da ta zuciya".


      Wani irin ji Malikat Bushirat tai kamar ta shako wuyan Iffah, dan ta fahimci maganace cikin ta jefa mata. Itakam ta farama tunanin anya yarinyar nan mutumce kuwa ba aljanaba a sufar mutane? Ya kamata a bincika mata kam dan al'amarin ya fara girman tunaninta. Amma a zahiri sai ta cije tai dan yake. Tajwar Eshaan da ke dan jinjina kai batare da ya fahimci komai ba shi kam a zancen idanunsa dake akan Iffah ya lumshe kadam da budewa lokaci guda. "Ammie shawaran nan nata mai kyau ne, ni kaina naso na miki tayin hakan tuni sabgogina basu barni na zauna ba. Amma Alhamdullah tunda gata yanzu bayan ni da Aunt kin sake samun diya daga ALLAH nasan zata kula mana da ke kamar mu din. Sannan kusantar al'ummar mu yanda ya kamata a zahirance zai kara saka mana son su da kaunar su a zukata kamar yanda ta fada. Zakiji dadin hakan, ki samu lokaci ki fara gwadawa koda tare da itane ni mai yarje muku ne".


    "Uhm kai dai. To ALLAH ya shige mana gaba kawai".


     Amin suka fada a tare shi da Iffah, sai dai a ransa yasan bata amshi lamarin ba. Dan haka ya basar da zance ya dakko mata na tafiyarsu.Cikin mamaki take kallonsa sai dai batace komai ba. A ranta kam wani irin zafi takeji mai kuna. Har itace sai yau Saiful-malik ke sanarma zaije Umrah, Umrah din ma na azumi baki daya. Kai anya bata fara rasa danta ba kuwa? Bata fara rasa danta daga jikinta ba kuwa? Jifa maganganun da yarinyar nan ta fada mata a yanzu, irin wanda ko mahaifiyarta sanda tana a raye bata jin ta taba fada mata su, amma shi ya hau ya zauna Kamar ma bai fahimci manufarsu ba. Tabbas akwai matsala, matsala babba da uwa sam bata lissafo ba a lissafinta. Yanda fa rawar take neman canjawa dole ne shima kidan ya canja inba hakaba zata kona Masarautar nan ne baki daya why, dan bazata dauki faduwa a saman nasararta ba. Never for ever……..✍️

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post