Kyalkyalin Kauna page 2 Hausa Novel

 

Kyalkyalin Kauna page 2 Hausa Novel

✨KYALKYALIN KAUNA✨     ✍🏻M SHAKUR 
AMMNUR APHRODISIAC is home of lafiyayyun kayan mata na ban mamaki, kayan matsi, kayan gyaran nono, kayan gyaran amarye dana maijego da abubuwan mallaka kome kikeso zaki samu awajensu. 

Chat them up by clicking on this link; 

wa.me/+2349080070762EPISODE 2️⃣
Wuraren 4:22 wata mota yar daidai kiran toyota Camry tai parking gaban wani babban gida haka da kana ganin ginin kasan asalin ginin da ne daya kwan biyu saidai kofar gidan fes fes babu wani makusa awajen ko datti, parking motan akayi aka bude kofan aka fito anatse wani babban mutum ke fitowa daga motan dake sanye da kayan polisawa dasuka nuna asalin natsuwan shi dakuma manyantan shi acikinsu dan akalla mutumin bazai wuce shekaru 45 aduniya ba dan baida wani jikin tsufa hakanan he look young and fit sosai sai natsuwa da rashin wasa akan fuskanshi, from mere appearance kasan irin strict men din nan ne, maida kofan motan yayi yarufe sannan ya tsaya chak yana bin ko’ina da kallo, gabas yamma kudu da arewa kaman kai nazarin wani abu sannan ahankali yasa hannu yatura kofan gate din gidan yashiga cikin gidan, Babban gida ne sosai da cikin gidan nema zai kara maka confirming cewa old gida ne wannan, babban gida ne  mai katoton compound asalin irin ginin da dakunan ajere suke bawai flat flat bane, sai katoton bishiyan kashu dake tsakar gidan dakuma wata yar karaman yarinya yar kimanin shekaru 4 zuwa 5 dake zaune a tsakar gidan ita kadai kan tabarma ga plate na tuwo agabanta da ba’a zuba miya ba tana kallon tuwon tana kuka mara sauti tana goge hawayen da bayan hannunta kanta babu dan kwali sai gashi dake mata lilo sabida iska dake kadawa yarinyar black beauty da ita kana ganinta kaga bakar bafulatana, anatse yake tafiya harya karasa gaban tabarman ya tsaya akanta, cikin kuka yarinyar ta kalli bakin cover shoe dake gabanta dake kyalli shinning mai wankin takalmi sannan tadago fuskanta ahankali sama takalleshi dasauri tace “Babaa” saikuma ta tashi dasauri tana ture tuwon ta rungumeshi awani kalan shagwabe, for the first time mutumin yasaki murmushi yasa hannu yadauketa yace “Nanan Baba yaya jikin”? Cikin magananta irin na yara amman tana fita tsaf tace “na warke Baba” hannunshi yakai yakama habanta yana kallonta yana kara kallon kwayan idanunta dasuke jikeda hawaye yace “mesa kike kuka”? Sake fashemai da kuka tayi kaman jira take ashagwabe tace “Baba ni baranci tuwo ba ni yoghurt zansha” dan murmushi yayi yaduka yasauketa ahankali yace “dauko hulanki kizo muje to nasiya miki” wani kalan tsalle tayi tareda shiga dakin wajen da gudu yabita da kallo yanadan murmushi ko second daya batayi ba tafito rikeda dan karamin hijabinta tana bashi karba yayi yaduka yana saka mata yace “ke kadai bakije islamiyya ba Allah kaimu gobe zakije dan kinji sauki” yana maganan ya idasa saka mata yadauketa yajuya da ita suka fice daidai nan wata mata da kana ganinta kasan ita ta haifi yarinyar da dan sandan ya fitada ita sabida yanda sukai kama ta leko daidai suna fita murmushi tayi ta koma kitchen din tana kallon wata yar dattijuwan mata dake tuka tuwo a babban tukunya tukunya Lamba biyar kaman na gidan biki irin family pot din nan tace “hala ubanta yafita da fitinanniyan”? Yar dariya Matan tayi tace “kaman kin sani Yaya” dan dariya matan tayi tace “tunda Nana tai yar kyandar nan gabaki dayan mu bamu huta gidan nan ba ai Allah kaimu gobe wlh kobaku turata makaranta ba ninan zan dauketa na kaita da kaina dan bata zama mana agida gobe fitinanniyan yarinya kawai mai hali irin na ubanta” dariya dukansu sukayi, Yaya tace “wai kin sake kiran Yasmeen kuwa? Kemadai kinsan idan mahaifinta yasan har yanzu bata dawo gida ba balle taje islamiyya yau kene zakisha fadanshi Ammi” dan yatsine fuska matan da aka kira da Ammi tayi tace “to nakira nakira bata dauka ba nasan duk yanda akayi tana hanya wani abun ne halan ya tsareta, akanme zaihau yimini fada shi da kanshi fa yadauketa yakaita wajen matan abokinshi dan takoyi girke girke sai yahauni da fada dantai latti” baki Yaya tasaki tana kallon Ammi tace “ohh ba shakka jibi yanda kike magana Ammi saikace bakisan halin mijinki akan yaran nan nashi ba, mutumin da yake tsaye kan yaranshi koke uwarsu baki isa ki gwadamai kinfishi sanin wani abu game dasu ba nidai sake kiranta dan wlh yau yafara masifan nan nashi na yan sanda babu abinda yashafeni wlh, ban lekowa ma balle nasa baki nabada hakuri, itakuma Hajjo bazata dawo daga gidan suna bane tadaisan yanzun nan da Malam da mijin nata zasu dawo daga kasuwa ko”? Ammi data fito da waya tana kokarin kiran number datai saving da Yasmeen ne tace “ai yanzun nan zakiga Hajjo dazu da muka leka mata gidan batace ana la’asar zata dawo ba” wayan takai kunne yagama ringing still shima ba’a dagaba cikeda damuwa tace “wlh bata dagaba” baki Yaya ta tabe tace “nidai turomin kwanukan nan kigani mu kwashe tuwon nan na shige daka” turamata kwanukan tayi tashiga kwashewa ita kuma Ammi na kwasa tana fito dasu tana ijiyewa kan tabarma daidai an bude gate an shigo tadaga kanta, mijin nata ne yashigo da Nana a hannunshi dake rikeda goran yoghurt din Habib, shikuma yarike wata yar leda da yoghurt guda uku keciki yakaraso bata ledan yayi yace “gashi kirabama yara idan sun dawo” murmushi tayi tace “sannu da zuwa Baban Nana, ya aikin” ahankali yace “Alhamdulillah” takalli Nana dake kiciniyar bude yoghurt din tace “kawota na bude miki” makema Maman nata kafada tayi tabama Babanta tace “ni Babana ne zai budemin” kwafa Ammi tayi tace “nida kene agidan nan” murmushi Baban kawai yayi yabude yabata wani kalan zama ta gyara tanasha hakan yasa yakalli Matar tashi yace “Yasmeen da Farida fa suna islamiyya”? Dan kallonshi tayi itadai tunda yake bata taba ganin uba da baya wasa da lamarin yaranshi irin mijinta ba, anatse tace “Farida dasu Sa’a duka suna islamiyya” dasauri yace “Yasmeen fa”? Ahankali tace “har yanzu bata dawo daga wajen Maman Intee ba, kuma ina kiranta bata dauka, maybe basu gama aiki dawuri bane” take yanayin fuskanshi ya chanza, duk wani walwala da annuri na kan fuskanshi bacewa yayi bat, hannunshi yatura cikin aljihu dasauri yaciro wayanshi kiran Infinix zero number dayay saving da Yasmeen yay dialing saidai harta katse ba’a dagaba, dasauri yamaida wayan aljihu yajuya hakan yasa Ammi tabishi dasauri tace “ina zaka kuma Baban Nanah ko kayan aiki baka cire ba fa”? Batare daya juyo yakalleta ba yace “zanje gidan Maman Intee, nagayamata anything 3:30 tasallami Yasmeen sabida kafin hudu tadawo gida ta shirya tawuce islamiyya” hannu yasa zai bude gate karaf Ammi tarike hannunshi hakan yasa yajuyo yakalli fuskanta,  anatse tace “dan Allah calm down, nasan ko’ina Yasmeen take yanzu haka tana hanyan dawowa gida ko kaje zakusha bambam ne, you are being over protective dayawa over this girls Baban Nanah, Yasmeen is a big girl remember?” Tai maganan tana kallon kwayan idanunshi Anatse trying to calm him down tace “Yasmeen is 20 yanzu, she’s not more yarinyar 12yrs old da zaka kasa ka tsare akanta haka please kadawo gida ka chanza kaya nakawo maka tuwo kaci Yasmeen zata dawo yanzun na. Besides yaune rana na farko data makara tunda tafara zuwa koyan su cake din nan awajen Maman Intee da kaine da kanka kasata please kazo kai wanka kahuta” tunda take maganan kallonta yake kaman mai nazarin wani abu kaman kuma baraiyi magana ba sai chan cikeda ihu dakuma fada ya nuna kanshi yace “are you telling me nazo na zauna na natsu y’ata daya kamata tadawo gida since bata dawo ba har zuwa yanzu kusan 5:15 yanzu? Kin zaci yanda baki sonsu baki damu da su ba haka nima nake? Diyarki daya kamata 3:50 ko 3:45 tana gida baki ganta ba baraki saka hijabi kibi hanya ba kin zauna agida ko ajikinki yanzu zanbi sahun ta kuma kinaso ki hanani what is your problem Hajara?” Yay maganan da tsawa cikin fushi da saida Yaya ta leko daga kitchen ta tabe baki takoma ciki abinta ita daman tasan za’ayi haka, cikin fushi yace “kina banzan tar mini da yara kina wulakanta mini su, nashigo gida na tarar da y’ata my sick little girl da duka duka yaushe taji sauki daga kyanda tana kuka she wants yoghurt baraki iya siyamata ba idan ma baki da kudin ne baraki ara ba in yaso nadawo saina biya amman no kin barmin ita tana kuka ita kadai a tsakar gida ke kina kitchen ko ajikinki, tun yanzu da raina da lafiyata kina neman maidamini da yara marayu” baki Ammi tasaki tana kallonshi takasa cewa komi kawai ganin ta inda yake shiga batanan yake fitaba balbaleta kawai yake da masifa, hannunshi ya fizge yace “when it comes to yarana don’t ever, I mean it don’t ever try to tell me wat to do or wat not to do” yawuce azuciya yabude gate yafita, sanin duk inda take yanzu tana hanya kuma bayaso yasha bambam da ita yasa yashiga tafiya da kafa bai dauki motanshi ba zuwa bakin junction na anguwan su yana kallon titi.Wata yar yarinya ce yar doguwa kadan dan bawani tsayin kirki ne da ita ba at the same time kuma ba gajera bace kana ganinta kasan bazata wuce shekaru 20 aduniya ba, wani kalan coffee skin ne da ita irin wayanda ake cema glass skin dinan, kana ganinta kaga mahaifiyarta Ammi saidai Ammi tafita duhu ita batakai Ammi duhu ba, tana sanye da hijabi dark blue mai hula daya kaimata har kasa anma hijabin hannu data fito da hannun data rike wata yar simple jaka da shi baki, wani flat takalmi ne akafanta baki irin na yan 1500 din nan masu hanci daya kara haska kananun kafanta da babu safa, dudda hijabinta mai hulane kana ganin tulin gashin kanta da some suka kwanta agoshi ta sabida dan zufan datayi na tafiyan datakeyi akasa, tanada wasu kalan manyan idanu da kwayan idanunta are complete gray kaman idanuwan yar tsuntsuwa, ga cikan bakin gashin gira dana idanu sai dan karamin dogon hancinta da lips dinta yan dis so pink dasu kaman na jiririyan da aka haifa yau, tana tsaye akan titin  tana juye juyen da kalle kalle da kai trying ta tsallaka titi dan titin is so busy gashi two sided titi ne kasancewan yamma kowa na kokarin komawa gida.“Yasmeen!” Kaman daga sama taji muryan Babanta na kiranta dasauri takalli saitin inda taji muryan gabanta nadan faduwa tana zaro idanunta fiki fiki kaman wata zabiya looking so calm and scared atare, hannu Baba yadaga mata alamun ta tsaya inda take hakan yasa anatse ta gyadamai kai tana hadiye miyan dataji ya katse abakinta kirjinta na bugawa still ganin Baba, tsallaka titin Baba yayi ahankali yakarasa daidai inda take yana kallonta ahankali dakuma sauri tana dari dari tace “Baba ina wuni” batare daya amsaba yakai hannunshi yakama hannunta kaman wata yar karaman yarinyan 5yrs yashiga dadduba titin sannan ya tsallako da ita yana tafiya da ita suka shiga layinsu ko kunyan jama’an anguwan su baijiba gam yarike hannunta yanda kasan yasaki hannun zaa dauketa ne suka shiga tafiya tana binshi ahankali kanta akasa har zuwa gida. Bude gate yayi tashiga sannan yashigo shima tareda sakin hannunta yamaida kofan yarufe sannan yace. Yace “ya akayi kikayi latti baki dawo ba” wani kalan ijiyan zuciya tasauke kana ganinta kasan itama duk atsorace take yanda kirjinta ke bugawa har a idanunta kake gani lips nata har rawa rawa suke tace “Baba bansamu keke bane kwata kwata shine nadawo akafa” cikin fushi kaman zai rufeta da duka yace “maisa baki kirani kingayamin baki samu keke ba?” Dan hawayen datake rikewa ne ya sauko mata dukta rude tashiga tura hannunta cikin jakan hannunta taciro wata yar techno phone rakani toilet tanunamai tace “Baba wayana yafada cikin zobon damuka yi ne, shine Maman Intee tace nabude naje nasa a shinkafa, saida zan tafi nadauko nahada na kunna ta kunnu amman anata kirana bana iya dauka har Mama ma takirani ban iya na dauka ba Baba kayakuri dan Allah” takarashe maganan tana sauke kanta kasa hawaye na saukowa daga idanunta yana sauka akasa gabanta faduwa kawai yake sabida tsoro, dan ijiyan zuciya Baba yasauke yana kallonta still yace “bani wayan” dasauri ta mikamai, karba yayi yace “wuce kije kicire kaya kiyi wanka kici abinci” gyadamai kai tayi tajuya ahankali tawuce, dakinsu tashiga Nana tabiyota dan aduniya Nanah nason Yasmeen sama da kowa na gidan, dan Yasmeen nakawo mata kayan dadi dasauri tace “Anty Yasmeen sorry Baba yasa kinyi kuka, nace kidawo ni kidaina kuka idan ana miki fada” wani kalan murmushi Yasmeen tayi takai bayan hannunta  tagoge fuskanta da sauri tace “nadaina” sannan tazauna kan katifar su dasauri itama Nanah tazo tazauna kusada ita tace “Anty Yasmeen Baba yasayamini yoghurt kuma narage miki nawa bari nakawo miki” ganin zata tashi yasa Yasmeen dasauri tarike mata hannu tace “tsaya tukunna” tace “yajiki kin warke nakawo miki cake da zobo” dasauri Nana tasauka dagakan gadon tana tsalle sosai Yasmeen tabude jakan data dawo dashi taciro cupcake guda daya tabata da zobo na gora daidai nan Ammi tashigo dakin ganinsu yasa Ammi tace “sai yashigo yaga baki wankan dayace kije kiyi ba kika zauna kika biyewa Nanah” dasauri ta tashi hakan yasa Ammi takalli Nana data shiga bude ledan cake din tace “kidaici ahankali dan kika fara zawo da ubanki zan barki nasan bazaiji kyashin wanke kashin yaranshi ba” dariya Nana tahauyi tana kallon Ammi cikeda yarinta tace “Ammi ai Baba na wankemin kashi idan nayi a po yakuma je bayi ya zubar tuntuni” tsaki Ammi tayi tawuce tafita daga dakin itakuma Yasmeen tadaura zani tasa hula akai tafito waje bucket tadauka na ruwa takai bayi sannan tadawo dakin Yaya tashiga tasameta zaune a tsakar falo tana cin tuwo tace “Yaya ina yini” kallonta Yaya tayi tareda washe baki tace “sannu yar nan jibi duk kinbi kin zuru zuru sabida fitinar ubanki Allah dai ya kyauta, Allah yakawo miki karshen fitinan mahaifin nan naki kisami miji ki aure ki barmai gida sai muga zai dinga bikin gidan mijinki ne yana bibiyan lamarinkj, jeki wankan ki kafin yafito yamiki wani sabon fadan” murmushi tayi tamike tsaye tafice Yaya tabita da kallo yarinya har yarinya amman fitinan ubanta yasa har yau ko mashinshini batadashi saisa ita tayi alkawari duk iskancin Baba yayi amman wlh barata bari yahana Sa’anta sakat ba, idan saurayinta yazo zance turata zatayi Sa’adatu ce kadai diyarka mace dan haka barata bari ya cuci rayuwanta ba shidai nashi yaran Yasmeen da Farida da Nanah karama yacigaba da musu haka sukai kwantai yakada su a nono yasha atoh, tana cikin tunanin taji sallaman yaran gidan an dawo daga islamiyya hakan yasa ta leko, yaran Hajjo ne agaba dan sune kananun yaran gidan dama su hudu manyan biyu maza sai mata yan shekaru 7-7 yanbiyu Hasana da Husaina, sai yaranta biyu maza Aliyu da Bashir dasuke nan sa’onnin Farida 15 yrs, sai Sa’adatu data girme Yasmeen da shekara daya ita she is 21, dukansu anatse suke ganin motan Baba awaje ansan yana gida, gabaki dayansu dakin Ammi sukayi dan zuwa gaida Baba.
Yana zaune a falo bayan yayi wanka dan shi adakinshi akwai bayi yana sanye da farar jallabiya suka shigo atare dukansu sukace “Baba sannu da zuwa ya aiki” binsu yayi da kallo one by one kaman mai nazarin abu kafin yayi murmushi yace “Alhamdulillah” kafin ahankali yace “kuje Ammi taraba muku yoghurt dinku sai ayi shirin salla” atare dukansu suka tattashi karaf idanunshi yasauka kan jelan gashin Sa’a daya fito dan kitson gaba ne akanta babu wasa akan muryanshi yace “Sa’adatu” adan daburce tajuyo tace “Na’am Baba” wani kalan mugun kallo yamata yace “me gashin nan ke nufi daya fito” dasauri takai hannunta tana maida gashin dukta rude tace “wlh Baba bansan yafito bane bazan karaba” mugun kallo yamata yace “next time kisaka hula kafin ki daura hijabi akai, gashi suturce shi ake kinajina” dasauri tace “eh naji Baba” “tafi” yafadi ahankali.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post