Kyalkyalin Kauna page 1 Hausa Novel

 

Kyalkyalin Kauna page 1 Hausa Novel

✨SPARKLES OF AFFECTION ✨DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI


NOTE: INTOXICANTS ARE BAD FOR THE HEALTH, THEY CAUSE A LIFE FULL OF MISERY, SAY NO TO DRUG ABUSE.
EPISODE 1️⃣
Wuraren 1:30 na dare yay parking motanshi wata mahaukaciyan faran Benz gaban wani babban club wanda da kyar yasamu yay parking motan kasancewa yau Friday yau mutane na zuwa club sosai dan weekend start yau gobe ba aiki hakama jibi, dudda girman wajen parking na club din yayi girman wani kauye hakan baisa yasami space ba tsabagen motocin dasuke nan sa’a ma yayi yana zuwa wani mota na fita saisa da awajen street din layin zaiyi parking, kashe mota yayi yafito, wani kyakkyawan dan saurayi ne fari dashi mai suffan fulani fulani da akalla zaiyi 34-35 years yana sanye da jeans da riga masu kyan gaske designers, yamaida motan yarufe yafara tafiya yana duba wayanshi dayaji sako yashigo yana dubawa yana tafiya zuwa entrance din shiga dawasu jibga jibgan security hudu ke wajen da bindigogi da bakaken kaya zaka dauka basamudaye ne suna ganinshi kai tsaye suka mammatsa suna gaidashi. “Welcome sir” gyadamusu kai yayi yawuce yashiga ciki, wani lafiyayyen security door ne awajen dakana gani kasan wannan ba anyhow ur common club bane dan ita kanta kofar abin kallo ce. Security door din ne yay magana yace “welcome ur access card please” dan gajeren tsaki yasaki yana tura hannunshi a aljihu yace “I hope ban manta da card dina a mota bama” yay maganan yana karasa tura hannun aljihu luckily yaji katin yaciro ya manna jikin kofan da nan da nan tai acknowledging katin kofan tace “Welcome to Xperince” kofan yabudu yashiga ciki, wani kalan hadadden club ne da gabaki daya baimada naija settings, kashiga ciki zaka dauka kana asalin kasar waje ne, duk wani wanda ya isa a club din nan zaka ganshi har yau ba’ayi irinshi a Abuja ba, matane a tsaye a stage strippers suna poll dance waka na tashi, ga maza ga mata wasu a zazzaune wasu a tsaye ana rawa ana spraying dollars kowa na having good time kawai, masu shan giya nayi, masu shakan cocaine nayi, ga customize azul na yawo ta ko’ina ana kaiwa wayanda sukai ordern su, gawasu kalan shisha da babu irinsu a nigeria anan xperince ne kawai ake samu, ga vape anasha suma, idan kashigo club din nan kai karan kanka kasan ana barin kudi, ga security guys daban daban in different corner and spot tsaitsaye da communicative devices a kunnensu kagansu zaka dauka gumaka ne kaman basa numfashi sabida yanda suka tsaya kikam akwana daban daban, wucewa yayi yahau lift zuwa second floor, direct gaban wani office yayi da wasu kattin security guda biyu ke tsaye awajen kai tsaye yakallesu yace “Pablo na ciki?” Cikeda girmamawa sukace “yes sir yana ciki” direct hannu yasa yabude kofan yashiga ciki batare dayay knocking ba, wani kalan mahaukacin office ne dayake nan kaman nawani shugaban kasa ga sanyin AC dake tashi aciki kaman kankara, wani kyakkyawan guy ne zaune akan kujeran cikin office din yana sanye dawani Armani white shirt da short nashi daya tsayamai iya knees nashi, kafanshi sanye dawani white nike socks mai tsayi yasaka wani black customize Dior sandals na maza dayay complimenting kayan jikinshi yana aiki da Mac book din dake gabanshi yana typing dasauri dasauri yatsunshi kaman machine idanunshi nakan laptop din har lokacin bai dago yakalli wanda yashigo cikin office din ba, hakan yasa wanda yashigo yaja kujeran dake facing nashi yazauna yana kallonshi kaman wanda yaga wani abu dabai taba gani ba, tundaga kan kafafunshi dayake iya hangowa dan transparent glass office table ne awajen yake kallo harzuwa kan yatsunshi dayake typing dasu, Pablo nada wani kalan yatsu dogaye masu kyau yanda yakeda tsawo haka yatsunshi keda dan tsayi, dogone shi sosai fatanshi baki ne irin baki sidik din nan, ko kadan baida rama wani kalan full gallant man ne dayakeda jikin every women dream, yanada broad fashashen kirji da abs kana ganinshi kasan wannan gym product ne dan he’s really working out and it’s so obvious, yanada wani kalan lips pink yirrrr sosai abin sai yawani kalan haska black face nashi ga dogon hanci kaman kan biro daya bama face nashi wani kalan definite look, yanada manyan fararen idanu dakuma cikan gashin gira black sosai, yanada gashin saje gyararre mai kyau dayakai zuwa gemunshi dayadan tara gashin gemun kadan kuma acike black dake shinning tsabagen jin gyara, yanada cikan gashin suman kai dasuke nan a kwance kanshi wani kalan wavy hair ne dake shinning sosai suka karamai kyau sai kunnenshi daya a huje yasaka wani dan karamin circled earring na gold guda daya, shi kanshi dan saurayin dake kallonshi wani zubin mamaki yake dan inda ace Maheer mace ne yanda samari zasu dinga layi hala tundaga gidansu har bakin anguwa gashi Allah yamai wani kalan mahaukacin farin jini da kwarjini sai kuma uban bakin hali da murdadden hali da Allah yamai.Batare daya janye idanunshi dagakan abinda yakeyi ba cikin wata kalan murya dake nan adikile irin muryan nan na no nonsense person ba wasa kokuma fara’a yace “how is my shipment Nas?” Firgigit saurayin daya kira da Nas ya farga daga duniyan tunani dakuma kallon Maheer dayake yadan sosa kanshi yace “I spoke to the captain gobe around 1500hrs zasu iso port na lagos so anything jibi shipment dinmu zai iso nan I assure you Escobar!” Sai a sannan yadago kanshi ahankali yadaurasu akan Nas tareda folding hannunshi a kirji kaman mai nazarin wani abu, murmushi Nas yayi yajaye idanunshi da dan sauri daga kallon da Maheer kemai yakalli about 40grams na cocaine dake kan table din da akai packaging ga wata yar karaman farin roba da aka zuba cocain yar kadan aciki taster yakai hannunshi yadauki yar roban yana budewa yace “coke din nan fa Pablo? Na waye”? Danne hancinshi daya yayi yashaki cocaine din jikinshi nawani kalan tsuma yana kyarma yace “Ya Allah!” Ya maida roban yarufe ya ijiye yana dan mika yace “amman wannan coke din wacce ta iso jiya ne daga Mexico ko dan wlh tayi dadi, har cikin bargon kashina najita, Wallahi tasa kyankyasan kwakwalwata sun watse dukansu sun fara tafiya suna gudu kaman an watsa musu fiyafiya” yay maganan yana murmushi yana daukan roban yana kokarin kara bude roban ya shaki na biyu Maheer yamai wani mugun kallo dayasa ya rufe ya maida ya ijiye roban dasauri yace “you don’t get high on duty nasani Oga!” Cikin wani kalan karisma Maheer yace “good” sannan yacigaba da aikin dayake yi daidai nan wata waya kirar iphone 14 pro max amman customize na gold dake kan table na wajen tashiga ruri kallon screen din Maheer yayi saikuma yadauke kanshi yacigaba da aikin dayakeyi hakan yasa Nas da kanshi yadan fara juyawa sabida yar kankanuwan coke din daya shaka yakalli screen din dan murmushi yayi yakalli Maheer yace “wai yaushe Boss zata dawo ne”? Batare da Maheer yakalleshi ba yace “bakada number ta ne”? Dasauri Nas yace “amman ai the whole empire ansan kaine favorite nata dan haka nasan tafada maka” batare daya kalleshi ba yace “tashi kabarmin office dina” dasauri Nas yace “Boss is obsess with you wlh, you yelled at her, imagine you even Bosses her around Pablo kaman kaine Mai empire dudda dai nasan you guys are partners in business yanzu but ai ita takawoka kaman yanda takawomu muma what’s so special about you dakai kadai takeji take kuma gani dudda akwai maza dai dai sama da maza dari biyu dake mata aiki banda external ones dake kawo Mata hari”? Yay maganan yana kallon Maheer dayay kaman baimasan wani na magana awajen ba, jaye idanunshi yayi yana kara kallon wayan da kusan this is the fifth call yake shigowa wayan kenan daga same number dayay saving da Hajiya, knocking kofan akayi hakan yasa Maheer yadago kanshi batare dayay magana ba yadanna wani boturi akan kujeranshi hakan yasa aka bude kofan aka shigo Manager club din ne yashigo yana sanye da suit black looking smart, cike da girmamawa yakaraso cikin office din yagaida Maheer yace “Sir we need XTC (Ecstasy akafi kiranki, ko methylenedioxymethamphetamine MDMA) saikuma Liquid X (Gamma-hydroxybutyrate GHB)

duk angama da wayanda aka fito dasu yau, kusan guest namu na yau yafi na kowani Friday” dasauri Nas yace “ba last dose of Liquid X aka fito dashi yauba”? Ahankali Maheer yamike tareda jaye kujeran dayake zaune kai baya, bindigar dake kan kujeran kiran Glock 17 Gen 4 yadauka yasoke abayan wandonshi sannan yafara tafiya kaman wani sarki da isa da takama dasauri suka biyoshi abaya kaman fadawa bude office din yayi yafita yahau stairs duk suna biyedashi zuwa sama wanda nan ne supply room na komi yake a club din dakuma kitchen,  kwali biyun XTC yabawa manager yace “lemme make the Liquid X come back in the next 30min” dasauri Manager yace “da kanka yallabai zaka hada mana yau”? Murmushi Nas yayi yace “chemist kake gani anan” murmushi Manager yayi yawuce yafita shikuma Maheer yay wani kitchen dakeda fadi sosai kana ganin kitchen din kasan kwayoyi kawai ake hadawa awajen wani black apron yadauka yadaura asaman kayan dake jikinshi yadauki tukunya yana tara ruwa hakan yasa Nas yasami waje yazauna kan kujera yanabin Maheer din da kallo danshi ko zaa kasheshi dudda shima ya dade a harkan amman bai iya hada daidai da burkutu nan nan ba, Maheer, Maheer sheggen yaro kake gani awajen nan saisa baya ganin laifin Boss data gama mutuwa akanshi dudda suna boyewa but yasan akwai something that is definitely going on tsakaninsu zai iya rantsewa cin juna suke dan Boss tai Kane kane akanshi saisa har yau baitaba ganin Maheer da wata budurwa aduniyan nan ba dudda kusan 30yrs kenan dayasan Maheer, bayama mata magana apart from Boss, ga yaron shegen kwaro ne duk randa Maheer yabar business din nan to empire din nan ta tashi aiki wlh dan kasuwan mutuwa zatayi mut ko abinda yasa Boss keji dashi kenan oho dan Maheer shine business din nan business din nan shine Maheer, ba abanza akamai lakabi da PABLO ESCOBAR ba the biggest drug lord in history, zai iya fadin this aduk inda yashiga ayanzu dai the biggest Drug lord in the whole Africa as a continent is Maheer Escobar na Africa!!!Yana cikin tunanin wayanshi yay kara hakan yasa da sauri yakai hannunshi gaban aljihun riganshi yazaro wayan ganin Boss yasa dasauri yakalli Maheer da hankalinshi kekan abinda yake dafawa a kitchen sannan yakai wayan kunne cikeda girmamawa yace “ranki shi dade Boss, Hajiyar mu Maman mu kuma gatanmu” dan shiru yayi yana sauraron maganan da akeyi daga ta dayan bangaren sai chan yadago kai yace “eh gani nan tareda shi yana dama Liquid X ne a kitchen” yay shiru yana sauraron maganan da ake saikuma yatashi yataho cikin kitchen din bama Maheer wayan yayi yace “gashi za’ayi magana dakai” kallon wayan Maheer yayi awulakance kaman baiso yay magana, kaman wanda magana kemai wahala yace “waye”? Wani kalan murmushin kunma rainamin wayau Nas yayi yace “Boss ce Oga takira, Hajiya ce” cikeda halin wulakancin nan nashi yadauke kai yacigaba da juya substance din dake wuta, baki Nas yasaki yana kallon Maheer, almost 1min yabata tsabagen wulakanci sannan yace “tell her am busy” maida wayan kunne Nas yayi yace “Boss kinji shi ko” dan shiru yayi saikuma yace “okay” zaro wayan yayi daga kunnenshi yadanna speaker sannan yace “Boss wayan na speaker” wata muryan yar matace da bazata wuce 45-46yrs ba dan tadan manyanta dagajin muryan authoritatively tace “Naseer ijiye wayan kawuce kafita inaso nai magana dashi” dasauri Nas yadan juya idanu yace “okay Boss” Nas yafada da girmamawa sannan ya ijiye wayan kan table dake wajen yajuya yafita daga kitchen din yarufo kofa.


Kusan 1min da fitanshi sannan matan ta sauke ijiyan zuciya ahankali cikeda asalin lallashi tace “wai Pablo so kake kahaukatani kai mesa kacika mugun hali ne? Tunda nasa kafa nafita nabar garin nan kaki kulani, kaki amsa WhatsApp message, text massage dakuma calls dina wai mesa kake wahalar dani ne eh, kanamin fizge fizge kana ciccimini magani agaban su Nas so kake su rainani kaman yanda ka rainani sabida babu abinda baka sani nawa bako” tai shiru tana sauke ijiyan zuciya jin still baiyi magana ba kuma tasan yana jinta rass maganan ce dai bazaimata ba, kaman zata haukace dan kanajin yanayin maganan ta kasan she’s really pain tace “wai mema namaka ne kaketa shareni? Damuwan ka tahanani sukuni nazo Las Vegas nama kasa natsuwa nayi finalizing deal din danazo yi dasu El Chapo, Maheer!” Takira sunanshi da karfi dayasa ahankali ya tsayar da juya liquid na tukunyan dayakeyi for the first time yakalli wayan batare dayace komi ba, cikeda lallashi kaman zata fashe da kuka tace “nine fa your Mami tunda nake dakai nataba offending naka? Kataba fadamin kanason wani abu ban maka ba? Komi nawa dana rayuwata na hannnunka there’s nothing dabaka sani game dani ba, I love you so much babyna dan Allah kayakuri kadaina fushi dani wlh zuciyata zata buga Mah…….” Saikuma tafashe da kuka sosai dayasa yadauke kanshi danshi ya tsani yaga anamai kuka abin na kashemai jiki ahankali yakai hannunshi yakashe gas din yawuce ya wanke hannunshi tsaf gaban tap sannan yadawo gaban wayan yana kallon wayan yanajin sautin kukanta kaman bazaiyi magana ba akufule yace “I hate cry” cikin sigan kuka dasauri matan tace “Toh you refuse to talk to me saisa nakemaka kukan” kaman bazaice komi ba cikeda isa yace “wat am I doing now?” Dan murmushi matan tayi mai sauti tace “miskilin yaro kawai Allah ya shiryamin kai, sabida nacema nadawo yakamata muyi aure shine kake wannan fushin” shiru yayi kaman bazaiyi magana ba yana juye liquid din awasu fancy goruna, idan da sabo tasaba da shariyan shi  dan halinshi ne saida yagama juyewa tass sannan yajuyo yakalli wayan anatse yace “I hate marriage cus it’s nonsense and kinsan da haka” dasauri Hajiya tace “kwarai nafi kowa sani, amman inaso kagane wani abu, kar abinda iyayenka sukama yasa kazo ka tsani aure gabaki daya I love you Maheer tun kana dan kankanin ka nake sonka you know that, na raineka da so, soyayyanka yasa naki aure dudda inada manyan mutanen dake nemana nadinga rainon ka harka girma kawowa yau, nasan bazaka taba so wata ba wannan tunanin ma baya raina dan I know who u are Maheer, I groom you kazama abinda kazama yau nasanka ciki da bai kawai inaso kazama mijina ne sunana should be link to yours forever, I want to bear your child dudda nawuce menopause yanzu but zamuje muga Dr a dubai he knows wat to do, please Maheer help me banson in mutu ba yaro ban aje maimun addu’a aduniya ba, inaso na haifi yaro ko yarinya da jininka ke gudana ajikinta this is my only wish”  dan gajeren tsaki yaja mai kara dan conversation din wani kalan mugun batamai rai yake adikile yace “this will be the last time I will say this to you Maryam!” Yakira sunanta direct da saida taji gabanta yafadi ahankali yace “bazan taba aure ba! And I don’t want children! Infact I hate babies, I hate children, idan kika shiryamin wata magana daban you can call but for now kije kisha iska”. Batare daya katse wayan ba yanaji tana hello hello yashiga cire apron na jikinshi ya yar akasan wajen yawuce yay hanyar kofa bude kofan yayi yafita Nas dake zaune awajen wajen yace “kai ina wayata?” Wucewa Maheer yayi batare daya kalleshi ba sanin halinshi yasa yakoma kitchen din yadauki wayanshi yasa a aljihu sannan yadauki liquid X din daya hada yafita dashi dan kaiwa manager yasan anachan clients na nema.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post