Kyalkyalin Kauna page 5 Hausa Novel

Kyalkyalin Kauna page 5 Hausa Novel

 ✨KYALKYALIN KAUNA✨




EPISODE 5️⃣



✍🏻M SHAKUR


Saukowa yayi daga stairs ranshi duk abace daidai gaban office dinshi ya tsaya batare dayama security wani kyakkyawan kallo ba yace “tell my driver to get the car ready zan fita yanzu” yana maganan yabude office nashi ya shiga, security daya yabiyoshi cikin office din, wasu keys yadauka a drawer da wayanshi yawuce akufule yace “get the coke let’s go” daukan cocaine nakan table dinshi security yayi yakashe wutan office din sannan yafito daga office din yabi bayan Maheer dake tafiya kaman sarki yashiga lift fita sukayi daga club din already wata arniyan bulletproof Chevrolet Suburbans  jeep na kampanin Inkas baka na gaban entrance din danshi kwata kwata baya hawa motan daba bulletproof ba for security, ga wasu bodyguards dake sanye da suit su hudu tsaye gaban motan suna ganin Maheer budemai bayan motan akayi kaman wani gwamna yafito hakan yasa yashiga dasauri ya zauna aka maida kofan aka rufe shikuma security ya tsaya kikam yana jiran Maheer da coke a hannu, kusan 1min Maheer yadauka kafin asauke glass din bayan leko da kanshi Maheer yayi hannunshi rikeda Cuba Aliados cigar wanda kudin shi kadai ya ishi mutum yasai manyan filaye kusan guda goma dan irin tulikin designers taban nan ne da turawa kesha mai Aromas na creamy oak, leather, fresh brewed coffee, tobacco, earth and sweet bread emanate from the wrapper, along with a small amount of citrus peel buso da hayakin yayi awaje ahankali yace “you see those two guy over there” yama security pointing gaban wani Brabus jeep dawasu samari biyu ke tsaye suna magana yace “give it to them” cikeda girmamawa yace “yes sir” ahankali yakoma cikin motan tareda jinginar da bayanshi ajikin motan yana lumshe ido yana huro hayakin taban, almost 2min yayi ahaka kafin murya chan kasa yace “what says the time Dan”? PA dinshi dake gaba kusada direban ne shima yana sanye da bakin suit yakalli agogon hannunshi calmly yace “is 3:45AM Sir” ahankali yace “and what is my schedule”? Wani iPad bodyguard din yadauka tareda dannawa sannan Anatse yace “kanada meeting da wannan senator by 4:15AM” wani kalan gajeren tsaki yaja har lokacin bai bude idanunshi ba, kaman wanda magana kema wahala yace “then what”? Bodyguard dake kallon pad din yace “1hr dama kace zaka bashi, immediately after that kuma kanada zoom meeting da head na distribution department namu na Lagos dakuma Delta, sunce akwai shortage na staff dan yanzu end users sun soma yawa” kaman wanda zaiyi bacci yace “can I cancel the meeting Dan”? Dasauri bodyguard kuma PA din daya kirada Dan yace “no sir you can’t, meeting din is very important unless zakai flying gobe kaje duka state din kai magana dasu” yatsine fuska Maheer yayi yace “naaah I can’t” dan ijiyan zuciya yasauke yace “I guess I will take the meeting then, let’s go” yay maganan yana zaro taban daga bakinshi daya gamasha anan kasan mota ya yar ko ajikinshi idanunshi a lumshe kusan tafiyan 40minutes sukayi, sannan suka yanki wani daji almost 20min drive sukayi kafin su kai wani babban gida gari guda Mai bala’in kyau,  gate wani soja yabude musu sukaja motan ciki, wasu motoci guda biyu wanda suke pake abangaren wajen parking na baki yasa yagane senator yazo.


Babban gida ne sosai da ta ko’ina security kawai kake gani da bindigogi a hannunsu suna zagaye babban compound din da akalla sunkai su 15, kashe motan driver yayi Dan yasauko dasauri yabudemai kofa saukowa yayi ahankali yakalli Dan yace “you know wat to do” dasauri yace “yes sir” hanyar main entrance Maheer yayi yashiga asalin babban flat na wajen, shikuma Dan yajuyo zuwa wani different flat dake opposite wanda Maheer yashiga, direct bude kofa yayi wani babban daki ne that’s more of office ga kujeru arnaye dakasan money lives here, wani mutum ne babba zaune kan kujera ga men dinshi tsaitsaye abayanshi tsayawa Dan yayi akanshi kaman Soja yace “nan bada jimawa ba Oga zai ganka” gyadamai kai senator yayi hakan yasa Dan yajuya yafita daga ciki.


Almost 20min Maheer yayi aciki sannan yasauko cikin wata beige cotton suit na Cesare Attolini one of the world most expensive suit brand

mai shegen kyau yana zuba wani kalan kamshi dasaika lumshe idanu, yasa wasu covershoe dake kyalli na tomford hannunshi daure da wristwatch na damier graphite race na LV, Dan na tsaye acikin falon dawasu security guda uku ganin yasauko yasa sukai gaba yana biyedasu abaya suka fita tareda budemai kofa, fitowa yayi yana gaba suna biye dashi daga dakin zuwa dayan bangaren, budemai kofa sukayi hakan yasa senator yadago kanshi da sauri yakalli kofan cikin wani isa da cika idanu Maheer yashigo yana tafiyan nan kaman king, kallo daya yama senator Ya watsar yawuce direct zuwa kujeran dake gaban table dake cikin office din yazauna tareda daura kafa daya kan daya sannan gently yajuyo yazubama senator idanu batare dayace kala ba, Sosai senator ke kallonshi dama Pablo Pablo dayaji kowa nafadi bawani babba bane yaro ne matashi dake ganiyan samartaka but still jibi yanda yacikamai idanu, yaron dakowa shakkan shi yake babu wani hukuma data isa ta taba kayanshi, da hannu yama Men nashi magana kan su fita, saida suka fita sannan su Dan suma suka fita daga dakin tareda maida kofan suka rufe sannan Senator yajuyo yakalli Maheer yace “yau gani ga the African famous Pablo Escobar, I heard a lot about you bazanyi karyaba ganinka yamafi jink……..” hannu Maheer yadagamai no chills kawai no nonsense kai tsaye yace “you’ve been bugging my management for the past 3months kenan kanason ganina amaka arranging meeting, so can you skip the talk and get to the chess you have just 15min left in one hour dana baka” durun uwa! Senator yafadi aranshi cikeda mamaki, idan haihuwa ne zai iya cewa ya haifi Maheer dan yanada yaro dake 40yrs amman jibi yanda wannan yaron dabazai wuce 30something ba idan yay wuta yabashi 35 ke mishi magana, he sha must give him this yaron is damn charismatic kana ganinshi kasan yasan abinda yakeyi, ga shegen kwarjini which dudda ya haifeshi but still bakaramin kwarjini yamai ba, dan murmushin yake yayi hakanan yaji kawai gabanshi nafaduwa wani shakkan Maheer na tsiro aranshi, washe baki yayi yana kallon Maheer din daya kafeshi da idanu yana kallon kwayar idanunshi bayako kyaftawa yace “inaso na shigo harkan nan ne, naga shine harkan dayafi komi kawo kudi yanzu aduniya kakap, da power dakuma matsayi, amman inaso na kafa tawa fadar a Chadi ne, da Cameron dan basu da abubuwa, abinda yasa nazo wajenka naji kayi suna awajen supplying kaya masu kyau da inganci sannan kwata kwata ba’a samin matsalan shipment dakai duk garin dakaso kai kaya kayanka na shiga saidai in bakaso ba to shine nakeson naji yaya za’ayi” tunda yake maganan Maheer ke kallonshi saida yagama maganan tsaf ido cikin ido Maheer yace “zaka iya business dani”? Dasauri Senator yace “kaman ya zan iya business dakai? Ba son aiki dakai yasa harnazo wajen ka ba” tsareshi Maheer yayi da mayun thug eyes nashi, irin kallon real criminal din nan yakemai yace “I said zaka iya business dani”? Wani kalan shakka Senator yaji ya diran mishi arai na Maheer, cikinshi nawani kalan hadewa kaman zawayi na shirin kamashi tsabagen yanda gabanshi kefadi, baki yabude zaiyi magana yaji muryanshi ta dishashe, gyaran murya yayi dasauri yana kallon Maheer still kafin ahankali yace “zan iya aiki dakai Pablo, I assure you bazaka taba samin matsala daga wajena ba, koda wani abu zai faru to dagata sama bakada matsala” lumshe idanu Maheer yayi yabude, kafin ahankali yamika hannunshi yadauki kwalin cigar dinshi dake kan table din yabude yazaro kuttubi guda daya yasa abaki sannan yadauki lighter ya kunna kafin ya ijiye lighter ya zuko tabar tareda cireta abakinshi yakalli Senator in the eyes sannan ya bursar da hayakin taban saitinshi a natse yace “for you to join my organization kadai akwai sum of money dazaka biya na registration which a Euros € zaka biya, all products dazaka saya you have to pay kafin mubaka payments are being done in dollars bana harka da nigeria dollars, saikuma bayan nabaka kaya ka saya duk wani profit dazakai making from my product zaka dinga bani 5%, sai last but not least i kill duk wanda yay betraying dina kodako kaine, I will waste your life and that of your family down to your great grand kids that’s if akwai, idan ka shirya my assistance and lawyers will put you through everything kuyi signing papers, nagama dakai you can excuse me” Maheer yay maganan yana nunamai kofa kallonshi Senator yayi yadauka kodan hannu Maheer zai bashi su gaisa amman ina, ashe dai duk labaran dayaji hakane, yaron akwai wulakanci da rashin mutunci sannan harka dashi akwai bala’in tsada just imagine fa bayan yabiya kudi yasayi kaya sannan still zai kawo 5% a profit dayay making na kayan daya saya but still haka mutane ke rushing nashi sabida kayanshi akwai kyau baka taba saya kafadi ba saikaci riba saisa zakaga kaman 5% daga profit din daya demanding is nothing compare to kalan riban dakake samu, tashi yayi ahankali yana gyara malummalum din jikinshi yace “to godiya nake Pablo zan karasa dasu kaman yanda kace” saida yakai kofa sannan kaman barawo yasake juyowa yakalli Maheer daya lumshe idanu yadaga kanshi sama yana huro hayakin taba in circles yadaura kafa daya kan daya sannan yajuya tareda bude kofan yafita Dan dake wajen yace “are you in or out sir”? Dasauri senator yace “in” wani kofa awajen Dan yabude yace “to come with me”.


Kusan 10min Dan yayi adakin daya kaisu sannan yafito yana daddana IPad saida ya knocking office din da Maheer keciki sannan yabude kofa yashiga yace “Sir is time for the meeting” kallon Dan yayi dayake tsaye a tsakiyan dakin, da yatsu yamai alamu daya karaso ya kawomai iPad din gabanshi sannan yakarashe zuke ragowan taban ya ijiye karan kan ashtray yakalli IPad din da wasu maza guda biyu kekan screen din daya Inyamuri daya bayerabe shikuma Dan yajuya yafita daga dakin.



Sai wuraren 9 yagama meeting din tashi yayi harzai fita saikuma yakalli kofan bathroom na dakin ahankali yakarasa zuwa wajen yabude kofan yashiga alwala yadauro yafito dadduma dake cikin drawer desk din shi yadauko ya shimfida yayi sallan asuba yana sallamewa yamike yafito daga dakin su Dan da securities nashi na tsaye gaban dakin suna gadinshi cikin gida yawuce direct bude kofa yayi yashiga falon Nas yagani a falo zaune dagashi sai gajerren wando da singlet ajikinshi yahada cereal a bowl yanaci yana kallon AIT, ganin Maheer yasa dasauri ya ijiye bowl din yace “Escobar gaskiya ayi hiring chef agidan nan nagaji da yunwa bansan mesa Boss tace kar adauko chef mace ba ita batason mata agidan nan, to tunda har yan aiki maza garemu akanme chef dinma bazamu dauko namiji ba, tunda maza ma yanzu sun kware a girki eh Pablo” yay maganan yana kallon fuskan Maheer ganin idanunshi nakan tv kyam yana kallo a tsayen yasa dasauri Nas shima yajuya yakalli tv yace “ohh wai kaji IG yacire tsohon CP yau ana nada sabo wannan Ibrahim Ibrahim din nan, he’s 45, dan Bauchi ne fulanin Bauchi amman girman nan Abuja ne achan dutse, ance he’s a very stubborn strict man but banwani damuba tundadai yaron CP da aka cire ne I am sure yasanmu da CP bazai bamu matsala ba ko Pablo” wucewa Maheer yayi yafara hawan stairs saikuma ya tsaya chak kafin yajuyo yakalli Nas dake kallonshi yana tauna cereal na bakinshi yace “if he dares mess with me i will mess with him right back” yana maganan yawuce sama murmushi Nas yayi yace “idanma baisan waye Pablo ba zaka gwadamai” kallon Dan yayi dake tsaye kikam yace “kaje kahadamai cereal ka kaimai” cikin gurbataccen hausanshi Dan yace “ba lallai yaci ba Oga, abincin wannan small eatry din kadai yake iyaci, sai anjima zamuje mu sayo” cikin son kokarin tunawa Nas yace “ohh wannan eatry nagane shi yama sunanshi I think ahhhhh” yasa hannu aka yana kokarin tunawa yace “something kaman Maman In….” Dasauri Dan yace “Maman Intee’s bite” nunashi da yatsa Nas yayi yace “yes correct, kai matan nan ta iya girki koni I love komi datake dafawa kusayo dani idan kunje”.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post