Kyalkyalin Kauna page 6 Hausa Novels

 

Kyalkyalin Kauna page 6 Hausa Novels


✨KYALKYALIN KAUNA✨
    ✍🏻M SHAKUREPISODE 6️⃣FREE PAGE

Ganin yanda ya tsaya kikam yasa Nas yace “zauna mana tunda kasamu yadan shiga ciki, kabiye ta Pablo you will die fa, baya bacci kwata kwata shi I think yanada insomnia, lumshe idanun yan mintinonin nan biyu dazakaga yayi idan yanashan taba shine baccin shi, dan haka kadinga bacci idan kasami sarari, karkazo kasami matsala” murmushi Dan yayi yace “a’a ko kadan I love serving Oga yanada kirki, I was born to serve him, kuma I was a military personnel so all this training nayisu” murmushi Nas yayi kawai he loves how loyal Dan is yace “good” yay maganan yana daukan wata alluran kwaya dake kusadashi yace “kaga ni yanzu zanma kaina shot ne bacci zanyi nida natashi sai 4 ko 5 sai nawuce basement inga how far aikin” gyadamai kai Dan yayi, wani yellow allura ya chakama kanshi a jijiyan hannu yajuye ruwan yana lumshe idanu yace “wayyo Allah na, wannan IV din duka Africa babu masu saida mai kwalitin tamu” wani kalan lumshe idanu yayi yana zaro alluran yana yarwa akasa cikin magana irin na maye yace “kaji yanda jikina yadauki sanyin dadi kuwa Dan? Har akaciyata nakejin sanyin nan washhhhh kaman natashi sama” wani kalan bugewa Nas yayi anan kujera idanunshi najuyawa yana shafa kirjinshi abuge yake kafin kaceme wani kalan lafiyayyen bacci yay awon gaba dashi.Wuraren 11 daidai yashiga saukowa daga sama, tundaga kan bene yake kallon Nas dayay wasting anan kankujera ga alluran dayama kanshi akasa yana bacci kan sofa, dauke kai Maheer yayi daga kallonshi yayi kofa da Dan yabudemai yana jiran zuwanshi saida yazo daidai wajen yace “what’s my schedule for now”? Anatse Dan yace “zamuje basement ganin Indian hemp din da yasauka jiya, akalla zakai awa daya awajen daganan kuma sai kaci abinci before next appointment” duk suna tafiya zuwa mota Dan ke sanarda shi abubuwan nan suna kaiwa mota da driver yariga yabude musu yashiga, maida motan yayi yarufe sannan da Dan da direban suka shiga gaba suka wuce.

Wani hadadden private asibiti suka wuce, parking sukayi kusada wata katuwar mota datai parking a filin asibitin da aka rubuta Medical supply aciki ga wasu ma’aikata maza na kwasan wasu manya manyan kwalaye na asibiti suna shiga ciki dashi ciki ahankali yasauko ya tsaya yabi motan da kallo kafin yazare dark shades dake kan idanunshi na Burberry yakalla abubuwan da ake shiga dashi ciki sannan yamaida glass din kan idanunshi yawuce,  Dan biyedashi zuwa cikin asibitin just few patients ne zaune anan reception din suna jiran ganin likita, hanyar theater yabi Dan yabudemai kofan theater din yashiga, wani likita ne dake sanye da kayan likitoci yafito daga wani daki ganin Maheer yasa cikeda girmamawa yace “sannu da zuwa Oga, har yanzu ana kan aiki ne baa gama sauke kayan ba zaka iya shiga ka duba” dakin da likitan yafito daga ciki Maheer yashiga akwai wata kofa aciki dazaka dauka kofan bayi ne budewa sukayi suka shiga saiga wani kofan basement dayake nan bude akasa kaman rami ga staircase aciki shiga ciki yayi idan kunga girman wajen zaka bude baki duk iya tunani ka bazaka taba kawowa acikin asibiti ne mutanen nan keda asalin basement nasu na kayayyakin su ba, ka shiga kasan zaka dauka wani gari kake daban daga ganin ginin kadai kasan nakashe kudi, bangare daban daban, bangaren coke, bangaren kodin, bangaren duk wasu kwayoyi daban daban ga bangaren allurai dasu suna a fridge.

Kusan 1 and the half hour yabata awajen dan saida ya tabbatar komi are in place sannan yabaro wajen direba yaja motan zuwa eatry da abincin kadai Maheer keci.
Eatry ne mai dan girma kadan wanda yake attached to gida, bawai eatry dazaka shigo kaci abinci bane, wanda kawai zaka shigo ka karbi abinci ne harkan order suke duka duka ma kujeru biyu ne acikin shagon, babu kalan abincin da Maman Intee batayi tundaga kan local dishes da international dishes da snacks wani abin ma kobatadashi idan kanaso zaka kira kasa amaka kabiya.


Bude kofan kitchen din akayi wata babban mace dakeda dan jiki dan akalla zatai sa’an Ammi tafito dauke da tray na samosas dasuka gama soyawa, tana sanye da irin rigunan Chef din nan da aka rubuta Chef MI ajiki, gaban showglass ta tsaya tana jera samosas din daidai nan ta hango wata bakar jeep tai parking agaban wajen wani kalan murmushi tayi tace “Alhamdulillah cinikina yazo yau, nidai kosuwaye mutanen nan Allah yamusu albarka kai Alhamdulillah, aduniya ayanzu banda customers kaman su jiya hardan zazzabi nayi da basuzo ba abincin saidai narabama yara da almajirai” duk tana maganan tana jera samosas dinne a showglass tana lekan motan dataga an bude gaba as usual Dan yafito yana gyara zaman suit nashi sannan yataho yashigo shagon, murmushi Maman Intee tayi sosai ganinshi tace “Jallabai barka da rana nace jiya bakuzo kunsayi komiba” ba yabo ba fallasa yace “Oga ne yay busy bamu samu chance nacin abinci ba” gyadamai kai Maman Intee tayi tana mamakin wani kalan busy zaka shiga dazaka manta da cikinka, tace “to me za’a saka muku yau”? Anatse yace “wanda kika saba sakamana” sake gyadamai kai tayi dasauri idanda sabo harta saba gasudai customers amman baka taba ganin dariyan su ko ayi hira dasu dama Dan ne yawanci ke shigowa ko direba siyan abincin, hanyar kitchen tayi saikuma tajuyo tace “wai yallabai nace mai gidan naku bayacin abincin gargajiya ne irin su tuwo, Inayin wani tuwo da miyan kuka da wlh idan mai gidanka yaci bazai karajin sha’awan su fried rice din nan ba” shiru Dan yayi kaman mai nazari yace “Akwai tuwon akasa ne”? Dasauri tace “a’a amman idan yanaso minti sha biyar yayi yawa nagama komi” shiru yayi saikuma yace “yanzu dai samana order bari naje natambayi Oga naji koyana so” wani kalan washe baki Maman Intee tayi tabude kitchen tashiga shikuma Dan yajuya yafita, baya yaje yay knocking hakan yasa Maheer yasauke glass na motan kadan yana yatsine fuska dan rana yamai rawa, ahankali yace “Oga matan tace atambayoka ko kanason tuwo da miyan kuka that she makes the best, but it will take atleast 15mins” shiru yayi yana kallon Dan gamamakin Dan Maheer yace “inada any meeting in the next 15mins”? Dasauri Dan yace “no daganan har zuwa 1hr u are free babu any schedule” komawa yayi ya jingina da motan tareda daukan wayanshi yafara dannawa ayangance akuma gadarance kaman wanda yake ciwon magana yace “ok” juyawa Dan yayi yana murmushi Oga is full of suprises wlh, dole ma kasoshi kazauna dashi murdadden hali ne dashi at the same time kuma complicatedly sweet, komawa ciki yayi ganin babu kowa yasa yace “Hajiya” dasauri Maman Intee tafito tana kallonshi ganinta yasa Dan yace “amai” washe baki tayi tace “Aiko bazaiyi regretting cin tuwona ba” juyawa Dan yayi yakoma mota itakuma takoma ciki, Yasmeen takalla dake hada takeaways na abincin dasukai order a leda dasauri Maman Intee tace “Yasmeen yimaza hadamin special miyan kukan nan naki yar kadan ta daidai cikin mutum daya Ogansu yace amai, tayi mugun dadi Yasmeen dan Allah kicikamai nama da kifaye nikuma bari na tuka tuwon” murmushi Yasmeen tayi idan kana tareda Maman Intee dole ma kasan yanda takeji da wayan nan customer nata ita bamata taba ganinsu ba dan kullum tana cikin kitchen Baba yace shi bai yadda yarshi ta saida abinci ba kawai girke girken yakawota takoya saisa tana kitchen koda yaushe ko Maman Intee zatai aike saidai wasu students din saidai student nata Monday, Wednesday da Sunday ne suke zuwa classes Yasmeen ne ke zuwa kullum rannan dazataje FCE ne kawai bata zuwa, Yasmeen nada saurin aiki da girki kafin kaceme sanwar yar kadan na kukan yafara tashi lumshe idanu Maman Intee tayi tace “nidai yar nan har mamaki nake irin baiwan dadin abincin da Allah yama hannunki Yasmeen, jibi yanda miyan ke kamshi” murmushi Yasmeen tayi tana zuba tafasassun naman dasukeda shi na kaji, tazuba kifi, Maman Intee kuma tashiga tuka tuwo saida tagama tarufe tukunya sannan tashiga karasa parking musu order, Chinese rice, coconut rice, fridge rice, porridge na yam, duk wani abinci datake dafawa suna saya, kusan 50 take away ne dama order dasuke kullum as usual hadawa tayi tashiga fito dasu waje, sannan takoma kitchen takarasa fito da sauran shigowa Dan yayi yakwasa yafita dasu yasake dawowa yace “tuwon fa”? Murmushi tayi tace “yanzun nan zaiyi kada kadamu basaika kara shiga rana ba zansa student dina takawo muku” Gyadamata kai yayi anatse yace “nasan kudin order mu but plus tuwon nan nawa kenan everything”?Ahankali Maman Intee dake lissafi daka tace “daman normal order ku is 175k ko kowani abinci is 3500 sau hamsin takeaway hamsin, special tuwon danama Oga is 7k yakama 182k kenan”  gyadamata kai yayi yajuya da ragowan abincin yafita yakai mota ya ijiye, dawowa yayi da bandir na yan 500 naira sababbi guda hudu yace “gashi asha ruwa da chanjin inji Oga” wani kalan washe baki tayi tama kasa magana sabida dadi Dan yace “ina jira a mota idan an gama a aiko mana dashi” gyadamai kai tayi tace “Allah yasaka da alkhairi Allah kara girma, atayani yima Oga godiya” badadan Baban Intee yahanata ba data fita tama Oga godiya da kanta, kwasan kudin tayi tashiga kitchen tana murmushi daidai Yasmeen na kwashe miyan awani take away dasauri Maman Intee tace “tsaya tsaya ina bansama Oga abinci a normal takeaway bari na dauko wayan nan imported take aways din kiga” fita daga kitchen din tayi tashiga tsakar gidan su zuwa dakinta tafito dawasu hadaddun take away takarbi miyan ta juye tasa man shanu itama ta kwashe tuwon tai packaging zokaji kamshi, cikeda farin ciki tace “Yasmeen taimaka mini kije waje kibasu suna cikin mota dan Allah ninece su zauna, yaron Alhajin yafita yadawo yakai sau goam saisa nace su bari dalibata zata kawo musu tuwon”, dau hijabinki kisa kiga” ahankali Yasmeen takai hannunta taja pink hijabinta dake sagale jikin kofan kitchen din tasaka ta karbi takeaways din da Maman Intee tadaura mata akan wani disposable cute tray abin looking so fancy tajuya har zata fice Maman Intee tace “tsaya nasa mishi special zobon dakika hada yasha yaji nasan wlh sai gobe yadawo still yay order abincin nan dan koni bantaba shan zobon dayakai naki dadi ba Yasmeen tunda nake aduniya” murmushi Yasmeen tayi akunyace tace “aike kika koyamin” Maman Intee dasauri tace “nasani but still nida nakoya mikin nawa baikai haka dadi ba, wanna wani sirri ne da Allah yama hannunki” murmushi takarayi maganan yamata dadi, for the first time in her life ga abinda akace ta iya! Maman Intee takawo gora daya na zobo dayay bala’in sanyi yama fara kankara amman ba sosai ba tadaura kan tray sannan tasa hannu tabudema Yasmeen kofan kitchen din tace “jeki kikai” fita tayi daga kitchen din ahankali tana tafiya, har zuwa entrance door dazai sadata da waje, gently tadaga right foot nata tafito dashi waje wani kalan sanyi taji kaman ta taka ice tundaga kan yatsan kafan nata har zuwa kai dayasa takasa motsi, ko kadan daga Dan har direba basu lurada itaba sabida waya dasuke dannawa, Maheer na baya idanunshi a lumshe ga waya a kunnenshi hakan yanuna waya yake saidai baya cewa komi wanda hakan halinshi ne, ahankali yakai hannunshi yadaura akan heart dinshi dayaji yabada wani single beat mai karfi dat is so unusual da saida yajishi har brain hakan yasa yasauke ijiyan zuciya ahankali, kusan 20secs tayi ahaka sanan ta iya tafito da second leg din nata tafara tafiya tana dumfaro motansu ahankali da bata iya ganin kowa na ciki motan baka kirin da ita, jikinta namata wani iri tsayawa tayi agaban motan tareda sauke ajiyan zuciya takai hannu kenan zatai knocking Dan yaga inuwanta hakan yasa yabude gaban motan da sauri ya mika hannunshi yakarba yace “har angama”? Batare data kalli fuskanshi ba cikin yar muryanta dakeda ratsa zuciya ahankali tace “eh!” Tareda juyawa at the same time, gently Maheer yabude idanunshi dake alumshe yana waya sabida wani kalan sweet voice daya daki dodon kunnenshi data furta “eh!” Wayan na kunnenshi yajuyar da kanshi yakalli waje ta glass din, bayan wata yarinya yagani matsakaiciya da hijabi pink har kasa ajikinta tajuya tana tafiya ahankali akuma natse takoma cikin shago, dudda baiga fuskanta ba but kalan hijabin yay kyau kodan hasken rana ya haskashine oho but sha dai yamai kyau kalan.  Dan yatsine fuska yayi ahankali yace “nagaji da magana talk to you later” zare wayan yayi batare daya katse ba ya yarda wayan akan kujeran wanda hakan yazaman mishi habit, direba ya kunna motan suka bazama titi suna gudu, ahankali yasake kai hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji bai dawo daidai ba yanamai wani iri daya kasa tantancewa to kodai baida lafiya ne, basu wani dade ba sukakai gida sabida yanda suke gudu.


Budemai kofa akayi yafito yayi ciki Dan yabiyoshi rikeda tuwonshi a tray dakuma takeaway daya na Chinese rice for Nas, sauran takeaways kuma na duka ma’aikatan gidan nan tundaga kan sojojin su masu gadi kusan maza 49 ke rayuwa agidan idan kahada da Nas da Maheer about 50 of them kenan, a dinning yawuce ya ijiye na Nas sannan yahau stairs yay sama, gaban wani babban daki yasaya da kofan ke akulle knocking yayi ahankali, almost 3min yabata sannan yace “shigo” bude kofan Dan yayi yashiga ciki dakin kaman wani empire na sarki komi fari sai kyau kaman dakin basarake babu kowa adakin hakan yasa yagane yana bayi, ijiye komi yayi kan kujera sannan yafito.Baya wani dadewa abayi wanka yayi yafito daure da towel a waist nashi sai karamin towel a hannunshi dayake tsane kanshi, kaga Maheer ahaka zaka kusa cinyeshi gawani damanmen ciki dayake dashi, gaban madubi ya tsaya yana goge kanshi da towel din ta madubi ya hango abincin yatsine fuska yayi ya ijiye karamin towel din sannan yadauki some bodyspray da cologne na maza masu tsadan gaske ya feffesa sannan ya ijiye komi yataho wajen kujeran ahankali yazauna yana kallon abincin kaman wanda ake roka da Allah da annabi yaci, da kyar yamika hannu yadauka yadaura akan cinyanshi, he’s not really a food freak abinci bai dameshi ba Sam sam, rabon dayaci abinci tun lunch na jiya da rana, bude take away yayi ahankali wani lafiyayen kamshi ne yadaki hancinshi kaman magic wani kugin yunwa cikinshi yayi, tuwo da kukan looks damn appealing to the eyes, ahankali yadauki spoon da aka nannade a ya warware, yabude tuwon yakai spoon din ya gutsuro kadan sannan yakai cikin miyan yadebo agadarance dan hakan is part of him yakai bakinshi Ya Ilahal Alameen, wani kalan kaikayi kaikayi yaji kunnenshi yafara hakan yasa ya girgiza kanshi dasauri yana hadiye abincin yasake gutsuro tuwon for the second time yakai bakin shi, abincin eatry din dama has always been nice saisa dudda wajen is not fancy bawai wani continental restaurant bane but he always choose abincin su but then again, tunda yake baitabacin abincin dayaji dandanon shi suit his palate and his stomach like this tuwo dake gabanshi ba, ijiye spoon din yayi ganin bayamai da kyau yasa hannunshi yashiga cin tuwon kaman bashiba within 5min yacinye duka uban tuwon nan tas da nama da kifin abin nabashi mamaki, kaman akaromai yakeji, zobon dake kan tray yakalla he hardly take zobo he don’t like it sabida kalan amman samin kanshi yayi da mika hannu yadauki goran bude sealed marfin yayi yakai bakinshi ya kurbi kadan kaman mai tsoron sha, lunshe idanunshi yayi dasauri Oh No! Kafin yadaga goran yakafa abaki saida ya shanye tassss sannan ya sauke goran dagakan bakinshi OMg roban zobon da takeaway ya kalla saikuma ahankali yakalli cikinshi yana mamaki shine yaci abinci haka yakuma sha zobo, it’s unbelievable.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post