Kyakyalin Kauna page 21

Kyakyalin Kauna page 21

✨KYALKYALIN KAUNA✨

     ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣1️⃣

KINASON MAGANA DANI M SHAKUR DIRECTLY click on this link


wa.me/+2347012181461

Sake rushewa Farida tayi da kuka jin tambayan da Baba yamata tace “nima bansani ba Baba” ganin yanda ake kallonsu yan layi dake wucewa yasa Baffa yace “muje gida tukunna” gida suka wuce Ammi na zaune a tsakar gida akan tabarma tabuga tagumi ga tuwo agabanta amman takasa tabawa babu abinda yashiga bakinta tun jiya, jin an bude kofa yasa ahankali ta dago kanta, Nanah dake hannun Baffa wani kalan dirkowa tayi kaman wacce tai shekaru bataga Maman ta ba tawani kwasa da gudu tace “Ammi Ammi Ammi na oyoyo” unbelievably Ammi ke kallon Nana batasan lokacin da itama ta taho dasauri ba tana zuwa wani kalan rungume Nana tayi tana kuka, itama Farida ta taho dasauri Ammi tahadasu ajikinta ya rungume kowa ya tsaya yana kallonsu abin gwanin taba rai, sakinsu Ammi tayi tadago kanta tana leka wuraren gate ganin bataga Yasmeen ba yasa tadawo da kanta takalli Farida tace “ina Yasmeen”? Shiru Farida tayi tana kallon fuskan Ammi takasa magana hakan yasa Ammi tadago kanta ahankali ta zubama Baba wasu kalan idanu sai kawai tasake fashewa da kuka ta kankame su Farida da Nanah ajikinta suma suka fashe da kuka, itama Yaya zuwa tayi tazauna gefensu tahau matsar kwalla tace “mudai muna ganin jifa’i kala kala Innalillahi wa innailaihi raji’un, Ya Allah, Ya Allah kabamu ikon cin jarabawan nan, Ya Allah ka tsare Yasmeen aduk inda take aduniyan nan” juyawa Baba yayi yace “zonan Farida” ahankali tasaki Ammi ta tashi tabi Baba da yashiga daki tambaya yamata tabashi tundaga farkon abinda yafaru har karshe tass, anatse Baba yace “kinga fuskan Ogan nasu da kyau?” Girgiza kai tayi tace “a’a ban gani ba mutane uku naga fuskansu, dawani baki mummuna dakuma yan sandan dasuka zo school namu” shiru Baba yayi kafin anatse yace “zaki iya kwatanta su”? Girgixamai kai tayi hakan yasa ya shafa kanta kawai anatse yace “sun muku wani abu”? Girgixamai kai tayi alamun a’a saikuma ahankali tace “Baba maisa basu saki harda Anty Yasmeen ba” shiru Baba yayi baice komi ba sai chan yace “itama zasu saketa, jeki wanka kici abinci kiyi salla” gydama Baba kai tayi Baba ma yabata tausayi duk kamanninshi ya chanza daga gani baiyi wanka ba, yana zaune anan Baffa yayi sallama yashigo wani kallo yama Baba anatse yace “Ibrahim daman duk nuna soyayyan dakake ma yaranka na karyane eh”? Baffa yamai maganan cikeda tsananin fada dayasa Baba ahankali yace “menayi Yaya”? Cikin fushi Baffa yanunashi da yatsa yace “kada ka kara kirana da Yayanka dan baka nuna mini na isa Yaya agareka ba, kabama Pablo abubuwan su kabasu rabi yanzu gashi sun rike Yasmeen so kake su bata rayuwan yarinyar nan? Did you even know the effect of abinda kayi Ibrahim” hannu Baba yasa yakama kanshi tareda sauke kanshi akasa dan kanshi kaman zai fashe ana neman 48hrs kenan baiyi bacci ba koya kulle idanuwanshi, sai yanzu yagane Aliyu ne yagayama Baffa komi, cikeda damuwa batare daya dago kanshi ba yace “Yaya kayakuri” cikin fada sosai Baffa yace “dukanku a family nan are my responsibility, hakki nane ku gabaki dayanku Ibrahim, nace maka kai abu bakayiba kabasu rabin abu, sun baka kaima rabi, Fatima nachan sun rike, what is your problem bari kaji nafada maka” Baffa yay maganan cikeda tsananin baccin rai yace “inhar aikin nan naka zai zama danger akan rayuwan iyalina ina nufin dukanku tatas yan gidan nan wlh wlh zakabar aikin nan I don’t care cewa kayi shekara da shekaru kana dan sanda zakabar aikin ne dukanmu muhadu mukoma kasuwa, and listen listen very well if anything happens to Fatima!” Baffa yanunashi da hannu cikeda mugun baccin rai yace “wlh wlh sainai fushin daban tabayi dakai ba tunda iyayenmu suka kawomu duniya” Baffa yajuya fuuuu yafita daga dakin, Baba yakai kusan minti ashirin zaune awajen yakama kanshi dake sarawa sannan yaciro wayanshi number su Pablo yay dialing amman bata shiga an kara cireta daga kan network ijiye wayan yayi agefenshi yasake kama kanshi daga bisani yamike yatashi yafita daga dakin ko kallon inda su Ammi suke baiyiba yawuce yafita Aliyu ne yama su Baffa sallama sannan yabi bayan Baba da sauri yana zuwa yashiga mota Baba yaja motan zuwa police station.Yana shiga parking yayi wajen parking sannan yajuyo yakalli Aliyu dake kokarin bude kofa yafita hakan yasa Aliyu ya tsaya batare dayace komiba, anatse Baba yace “jeka sallame su sutafi” gyadamai kai Aliyu yayi dasauri yace “Alhamdulillah” yabude kofan yafita da sauri yamaida kofan yarufe, wani kalan dukan kujera Baba yayi zuciyanshi namai zafi sosai kafin yayi huci anatse yace “you won this time Pablo but trust me next time I will be the one that’s gonna win”.

*****Taba kofan tayi da sauri tareda bugawa tace “dan Allah kubude ni ku komarda ni wajen Kannaina” bude kofan taji an shigayi hakan yasa takoma baya dasauri ta tsaya kirjinta na dukan uku uku tana kallon kofan, tura kofan akayi aka shigo, wata faran mata ce kaman ma shuwa ce matan tashigo dakin tana sanye dawani lafiyayyen lace purple mai shegen kyau yaji duwatsu da flowers anyi dinkin riga da skirt, batada wani kiba dan yanayin jikin matan kaman na Ammi, matan nada boobs sosai da katon ass, tana rikeda wani birkin bag wanda ake saidawa miliyan sha biyar sha uku din nan mai shegen kyau da jimmy choo heels da duwatsun saman are diamonds, dawani dan karamin mayafi data yana kanta dashi wanda babu dan kwali akai gashinta a gyare anyi parking an zubo dasu har tsakiyan bayanta, sai kamshi take sosai kana ganinta kaga kudi, kudi sun zauna ne Alhaji!, yanda Yasmeen ke kallonta haka itama ke kallon Yasmeen din tundaga kai har kafa ta hade rai kaman bata taba dariya ba arayuwanta, wani wulakantaccen kallo tama Yasmeen sannan tajuya batare datacema Yasmeen ci kanki ba zata koma waje dasauri Yasmeen tace “Anty Please ki kaini wajen kannaina” wani abune Hajiya kawai taji yatokare mata wuya sabida yanda taji muryan yarinyar dakeda bala’in dadi gashi da sanyi mai bala’in ratsa zuciya kaman tana shagwaba, Juyowa Hajiya tayi tamata mugun kallo kafin awulakance kaman taga kashi tace “namiki kama da wacce zaki aika?” Dasauri Yasmeen ta girgixa kanta ganin matan batada mutunci murya chan kasa tace “yakuri” wani kalan tsanan ta kawai Hajiya taji yashiga ranta shigowa tayi cikin study din takai hannunta gaban rigan Yasmeen cikeda wani kalan wulakanci ta fincikota tajawota waje tana tafiya da ita suka fito daga dakin dasauri Yasmeen tashiga binta bata wani damu ba da yanda take janta kaman baiwa danta dauka wajensu Farida zata kaita, cikin wani babban falo taga Hajiya ta bullo da ita ga su Nas zazzaune suna shan XTC, ta tsakiyansu tabi da ita zuwa wani babban kitchen tana shiga tawani kalan jefata tsakiyan kitchen din saida kanta ya bugu da bango takoma baya dasauri tareda kai hannunta kan goshi ahankali tace “wayyo kaina” azuciye Hajiya tace “arrange this kitchen tass sannan I don’t care ki dafa abinci for maza na  55, yau biyar bazaa kashe siyo abinci ba, daga yanzu kin dawo slave agidan nan harsai ubanki yagama bamu abinmu dake hannunshi, kinyi kadan kice zaki rayuwa in peace in our house” tajuyo azuciye takalli su Nas daduk sun mike tsaye tace “ku tsare gaban kitchen din nan kartai attempting guduwa” sannan tasake juyowa takalli Yasmeen dake liliya goshinta da hannu dahar ya kumbura tace “bazaki fara abinda nasaki ba” Gyadamata kai Yasmeen tayi dasauri dan hakanan taji Allah yasamata tsoron matan sama da kowa na gidan”.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post