Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 29


❤EX-PRISONERS❤

"Ke! Meye sunanki"! Ta jefa ma Batul tambayar, muryarta na rawa ta furta"BATUL"! ta6e baki ummi tayi tare da ɗaura idonta kan Angel"ke fa"?

  Ɗaure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace"UNAISAH" 

  "Me kuke nema ne"?

Angel ce tayi ƙarfin halin bata amsa da cewa"ɗan uwana ke jin yunwa, shine na fito don in sama mashi abun da zai ci"

 Ta6e la66a ummi tayi"An shirya maku breakfast din ku a dining, dama ku nake jira ku farka" ta faɗa tana nuna masu dining room da hannunta, atare su ka kai idonsu ita da batul suka kalli ɗakin.

  "Ku koma ku tada sauran ƴan uwan naku, su fito mu yi breakfast, idan mun kammala inaso zanyi magana da ku"

   Amsa mata su ka yi da toh, da sauri suka juya suka nufi bedrooms din ƴan uwansu, tana a tsaye tana bin bayansu da kallo, bakomai yafi bata mamaki da yaran ba face doguwar sumar kansu data lullu6e bayansu kamar hijabi, aranta ta ayyana ɗawainiya da yaran nan ba abune mai sauƙi ba, gyaran gashin kansu kaɗai wata wahalar ce mai zaman kanta, gashi an faɗa mata babu shige babu fuce balle tace zata kai su saloon, kuma babu damar a gayyato masu yi din suyi masu, dole sai dai ita ce za ta gyara su.

Daya bayan ɗaya suka bi ɗakunan yan uwansu suka shiga domin tada wadanda basu farka daga bacci ba, saida suka taimaka ma Azeeza da jamimah suka wanke fuskokinsu da bakunansu, tukunna suka fito daga ɗakin, Kayan jiya ne a jikinsu sai mayafin da suka yafa akansu, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, musamman azeeza tun da tayi tozali da ƙwan fitilun falo jikinta Ya hau yin kerma, duk ta firgice, Parveen kuwa baki yaƙi rufuwa kamar lefen sakarai sai faman zazzare idanuwa suke Yi, saboda yanzu ne suka samu damar ganin ko'ina na cikin gidan dakyau, Hanna kuwa daƙyar take taka tiles din floor, da takalmi ta fito amma saboda tsabar ruɗu a hannu ta ruƙe takalman ta rungumesu a ƙirjinta, gani take kamar in ta taka ƙasan da takalman zai fashe, Naufal da Javed har tuntu6e suke yi garin yin kalle kalle gidan yayi matuƙar ruɗar dasu, shi ko Haris jiki sai kerma yake yi basa ban ban, shima crystal Chandelier din ceilling ne Ya ruɗar da shi ga sanyin A.c da yayi mashi yawa, hatta gabriel dake da wayewa yau dai an ƙure shi, sai faman jinjina kai Yake yi yayin da yake bin katafaren falon da kallo, abunda zai baka mamaki jamimah hankalinta kwance babu abunda ya ruɗe ta koya tsoratar da ita, sai faman washe baki take Yi komai ta kalla saita nuna shi da yatsa tace"menene wancan" ta ishe su da tambaya kamar rainon ɗan jarida, Ummin america dake a tsaye bakin ƙofar shiga dining room din, lamarin ya ɗaure mata kai, tayi matuƙar yin mamakin ƙauyancin su, gasu dai a halitta kamar ƴa'ƴan masu kuɗi, tafiya suke yi tamkar suna jin tsoron taka floor, sunƙi maida hankali su shigo su ci abinci, sai faman ƴan kalle kalle suke Yi kamar wuyansu zai cire.

   Mutum ɗaya ce babu acikinsu, Angel da ta tafi bedroom ɗin Danish, Batul dai tana atare da su Haris.

  Gyaran muryar da ummi tayi masu ne ya janyo hankalinsu ga kallonta.

     Da hannu ta nuna masu ƙofar shiga"ku zo ku shiga" ba tare da sun tanka mata ba, suka nufi ɗakin cin abincin, koda suka shiga sai suka koma suna bin ko'ina da kallo, Parveen ce ta furta"La'ha'ilah! Wannan duk namune"? Ta jefa tambayar tana nuna kayan breakfast din dake a jere saman zungureran table.

  Ummi ce ta bata amsa da cewa"naku ne, kowa ya samu wuri ya zauna" su parveen anga banza, tuni taja kujera ta zauna, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya samu wuri ya zauna, sai faman baza ido suke Yi suna bin komai da kallo, jamimah tana jinjina kai tace"Yau zamu ci daɗi, wallahi munji daɗi muma mun zama ƴan gayu, gidan daddyn genie akwai abinci da kayan wasa" 

 Azeeza taƙi ɗagowa dakai, ta ƙanƙame jikinta saman kujera, ita kwan fitila ne damuwarta, na ɗakinsu bai kai  na falo dana dining room girma ba, sun hanata sakat, Gabriel dake kallonta cikin muryar raɗa ya ambaci sunanta"My azeeza" ɗagowa tayi da ido tana kallon shi sai faman yamutsa fuska take Yi


  "Meke damun ki"?


Da index finger ta nuna mashi saman ceilling ba tare da ta kalla ba, muryarta ƙasa ƙasa tace"zai Iya faɗowa saman kanmu"

  Murmushi ya sakar mata"ki kwantar da hankalin ki, ba zai ta6a faɗowa ba, idan ma zai faɗo sai na tare maki shi, hakan yayi maki"? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi jin abun da yace ta jinjina mashi kai alamar eh.

 Parveen sai faman haɗiyar yawu take yi ta ƙosa su fara ci, sai dai sun gaza sanya hannu ganin yadda Ummin america ta tsare su da ido ko kyaftawa ba tayi, tana daga tsaye bakin glass door din dakin, ta lura basu cika ba shiyasa ta tsaya tana jiran sauran su ƙaraso don su fara ci.

  "Menene wannan abun" jamimah ce tayi tambaya tana nuna wata roba


 Kallon robar Gabriel yai a jikinta an rubuta Honey.

   "Zuma ce a ciki, kin ta6a sha"? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a, ta kuma nuna dafaffan ƙwai tace"wannan luluyayyan abun fa"? Harara ya dan jefa mata"Ƙwai ne, pls ki daina yi min tambaya baki ga ana kallon mu ba"? Ta6e mashi baki tayi"to aini inason in sani ne ko," har tayi shiru can kuma kamar an cikare ta tace"Gabriel kace ƙwai ne, to shima kamar ƙwan fitila mai bada haske Yake"shiru yayi yana kallonta ba tare daya furta komai ba, 

(abun da yasa take tambayarshi saboda bakomai ne suka sani dangane da nau'ikan abinci, ko a kurkuku snacks da nama suke ci da kayan marmari, haka zalika a asibiti da suka zauna bakomai ne suka sani ba yawanci duk kalar abunda suke ci a prison ne, yau sunci karo da wasu nau'ikan abincin dana sha wanda basu ta6a yin tozali da su, shiyasa jemimah ta tsare shi da tambayoyi kamar ƴar jarida)

Batul dai sai satar kallon ummi take yi ita kanta ummin ta lura da kallon ƙurullan da Batul take Yi mata, shiyasa ta tsaida idonta akanta, tunda tayi hakan batul ta saddar da kanta ƙasa cikin jin kunyarta.

   Abun da Ya faru, Lokacin da suka kammala tada ƴan uwansu Angel ta nufi ɗakin Danish, shigarta keda wuya ta taras dashi atsaye gaban mirror Yana faman yin haki Ya dunƙule tafukan hannayensa kamar wanda zai yi dambe, Kafin ta buɗe baki ta tambaye shi lafiya, idanuwanta suka sauka akan madubin daya fasa, ƙwaƙƙwaran naushi ya kai mashi gaba ɗaya ya zube ƙasa ya tarwatse.

  Rass taji gabanta Ya faɗi, a tsananin tsoroce ta furta"Na shiga uku! danish meyasa zaka fasa masu madubi? Kasan kuwa tsadar dake gare shi? Wai meke damunka ne? So kake kaja mana bala'i daga zuwa gidan mutane har ka fara yi masu 6arna" hankalinta atashe tayi maganar tana duban bayanshi.




  A hankali Ya jiyo yana kallon cikin sanyin murya ya furta"mutun na gani aciki Yana kallona, shiyasa na naushe shi" Zaro ido waje tayi can kuma ta tuntsire da dariya hada dafe ciki, ɗaure mata fuska yai ganin tana yi mashi dariya.




 Nuna shi tayi da yatsa tana fadin"mutumin da ka gani acikin madubin kaine ba wani ba, ai saida naso in nuna maka kanka a mirror amma kaƙiya, ka nuna baka son kallon shi gashi nan Yanzu ka fasa masu madubi mai tsada, Ni dai ba ruwana" ta faɗa fuskarta da murmushi.




   Kallon rashin fahimta yake binta da shi, ya rasa gane me take nufi, kamar bata fahimci abunda ya faɗa mata ba.




  Gudun kada wani ya shigo ya taras da 6arnar da Danish yayi yasa tayi saurin juyawa tana yan dube dube cen idonta ya sauka kan wani abu yayi mata yanayi da tsintsiya da sauri ta ɗauko ta tattara broken glass din ta turasu kasan gadon shi dan bataga dust bin a dakin ba ajiyar zuciya ta sauke




  Kafin ta ɗago tana dubanshi"kai kaɗai muke jira, zamu yi break fast, ka shiga toilet ka wanke face dinka da bakinka, idan mun gama cin abincin sai kayi wankan" toilet door Ya nufa, har ya kusa kaiwa ƙofar ta tuna da madubin toilet, da karfi ta furta"dakata danish" cak ya tsaya da tafiya, da sauri ta nufi ƙofar toilet din ta buɗe ta shige ciki, towel ta ɗauko ta rufe madubi, saboda tsaro tasan zai Iya Fasa shi kamar yadda ya fasa na room dinsa.




  Fitowa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya ta dubi fuskarshi"nasan idan ka shiga ciki zakaga towel na lullu6e wani abu dashi, kada ka buɗe shi, madubi ne bana so ka fasa shi kamar yadda ka fasa na ɗakin ka, Idan ba haka ba zasu ce saika biya su ne kuma kaga bamu da kuɗi, kai ba kama san menene kuɗi ba, Ni zaka bari da aikin biyansu" ta faɗa tana yamutsa mashi fuska, bawan Allah yayi tsaye yana kallonta.




  "Ina jiran ka, kada ka daɗe ka yi sauri ka fito suna jiran mu"




  Amsa mata yai da toh, kafin ya bude kofar ya shiga, Ƴan mintuna ya fito  daga ciki, har yayi brushing teeth dinsa, daga kasa har sama take bin shi da kallo, a ganinta basai ya tsaya sanya kaya ba tun da ba wanka yayi ba, Ruƙo hannun shi tayi acikin nata kamar wani ƙaninta"muje ko"? Ta faɗa  tana ƙoƙarin janshi.




   Adai dai lokacin da suka sauko falon, ƙofar shigowa cikinsa ta zuge a hankali, atare Angel da Danish suka juya baya jin takun tafiyar mutun.




    Basu san wanene ba, amma saida taji gabanta Ya faɗi, ganin kakin dake a jikinshi na baƙaƙen Kaya, kuma ya rufe fuskarshi da face mask, 6oyewa tayi bayan Danish ta ƙanƙame shi tana leƙen mutumin da ke tunkaro su.


     Bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zai fasa ƙirjinta.


  Miƙa ma Danish hannu yai da niyar su gaisa, Danish Yaƙi bashi hannu saboda rashin yardar da shi, gyaran murya ya ɗanyi kafin ya soma magana a tsanake"zaku Iya kira na da Boss man, ina ɗaya daga cikin masu kula da ku," ya faɗi hakan ne don su saki jiki da shi.

  Ajiyar zuciya Angel ta sauke, jin muryarshi ta kamilallun mutane.

  Dawowa tayi daga gaban shi ta tsaya tana dubanshi, ido cikin ido suke kallon juna ba tare da ƙyaftawa ba.

 Tsawon mintuna kafin ta furta"Ina kwana," ya amsa mata"lafiyalou Angel, kin tashi lafiya? Ya kuma gajiyar tafiya"

 Tace"lafiyalou, gajiya tabi jiki, mun gode da kulawa" da alamun jin daɗin maganarta ya furta"Naji daɗin ganinki da ranki da lafiyarki, ina fata baki da wata damuwa" maganarshi taɗan so ta ruɗar da ita, amma sai ta basar tace"nima haka" da ƙyar ta furta ganin irin kallon da yake binta dashi, duk saita sha jinin jikinta, ta rasa gane kallon menene yake yi mata, dauriyace kawai yake yi, yaso ace zai iya bayyana mata kanshi a yanzu sai dai bazai yiwu ba.

  "Ciki zamu shiga Ni da Danish, suna jiranmu a dining" ta fada don ta samu damar guduwa daga kallon da mutumin yake binta da shi.

  Ɗagowa yai da ido ya dubi fuskar danish, har saida yaɗan ji gabanshi ya faɗi ganin yadda ya ɗaureta tamau babu annuri, dama tunda ya shigo falon yake mamakin kyawunshi da body structure dinshi don shi sai yanzu ya samu damar ganin shi, abakin abokan aikinsa yaji suna zuzuta kyan yaran da kamanninsu da Chief dinsu.

  "Ɗan uwan naki bai magana ne? Yaƙi bani hannu mu gaisa" murmushin yaƙe tasakar mashi"rashin sabone, Yana da wuyar sha'ani amma idan kuka saba zai saki jiki da kai"

  Jinjina kai boss man yai"okey, mu shiga ciki, Nima can zanje" a fakaice ta yamutsa fuska, aranta ta ayyana wannan mutumin zai takura mata ga shi da kallon tsiya kamar zai lashe mutun" a fili kuma taja hannun dashi suka nufi dining room din, Boss man na abiye da bayansu, kwata kwata babu alamun ƙauyanci atattare da Danish, sai dai jefi jefi yake satar kallon kayan alatun dake acikin katafaren falon.

  Lokacin da suka shiga dining room din da sallama abakunansu, gaba ɗaya hankulansu Baful Ya dawo kansu, Ummin america tuni ta samu wuri ta zauna, ganin Angel da suka yi da danish nan fa suka fara sakin murmushi kamar wasu zautattu, kujera taja ma danish ya zauna Yana fuskantar ummi, ita kuma Angel ta zauna daga gefen shi, Sai daga bisani su Gabriel suka lura da Boss man daya shigo, kallon juna suka yi da alama sun ɗan tsorata da ganinshi saboda dressing din jikin shi yayi shige dana Giants din kurkukun ƙaddara.

  Sai da Angel tace"ku gaishe shi, sunan shi Boss man, Yana ɗaya daga cikin waɗanda zasu dinga kula da mu" har suna haɗa baki wurin furta mashi gaisuwa, a mutunce ya amsa masu yaji daɗi yadda Angel tayi masu bayanin wanene shi.

   Ummi ta dube shi awayance tace"barka" ya amsa mata da"yawwa ya kike fatan kin wayi gari lafiya" a yayin da yake ƙokarin zama gefen kujerar dake a kusa da ita, wadda ke fuskantar Angel, don yaji daɗin kallonta.

Ummi tace "Lafiyalou," daga haka ta miƙe ta soma yin serving dinsu, a plates ta zuzzuba ma kowannansu abinci, ta dauki cups ta tsirara masu tea dake acikin flask, Bayan ta gama ta koma ta zauna"

 Yatsun hannun parveen har karma suke yi wurin ɗaukar cup din tea, duka ta kur6e shi, ta soma cin wainar kwai hannu baka hannu ƙurya.

    Batul kuwa wani sabon salon ƙauyanci, tunda ta dafi plate din noodles tasha romo da kayan haɗi, da hannu take ɗaukar indomie din tana Jujjuyata kafin ta turata abaki, ɗaya bayan ɗaya Angel ke kallonsu, Kunya duk ta kamata,  koda ta daura idonta kan Jamimah robar zuma ta ɗauka ta dinga matsata a tafin hannunta ta sanya harshe tana lasa hada tanɗar baki, Angel ji take kamar ta fasa ihu.

 Ummin america da boss man duk suna kallonsu sai faman sakin murmushi suke Yi.

 Gyaran murya ya yi masu jamimah ta dago tana kallon shi yace"kidaina shan zumar ita kadai, ga mahaɗinta nan ki zuba asama sai ki ci" ya faɗa yana nuna mata plate din pancakes da robar yougurt' washe mashi baki tayi tana fadin"wallahi zaƙi gareta, kunnuwana har motsi suke yi" gaba daya suka sanya dariya, Ummi kamar zata shaƙe  tsabar dariya, Angel dai abin duniya ya isheta, ita ala dole mai aji kada a zubda mata mutunci su kuwa ba ruwansu bayin Allah basu san ma menene ƙauyancin ba.

  "Malama, ki dauki spork da shi zakiyi amfani ki ci noodles din ba hannu ba" ummi ce tayi maganar tana nuna batul da spoon din hannunta, bata Iya cin abinci da cokali ba cos sunfi sabawa da hannu, jiki asanyaye batul ta ke faman ƴan kame kame ta rasa ina zata ɗauki cokali, Angel ce ta ɗauko shi ta miƙa mata, ta kar6a ta tsoma shi cikin indomie din batasan yadda zata kwasota ba, ganin yadda ummi take yi masu dariyar shaƙiyanci yasa ran Angel ya 6aci ta haɗe rai, muryarta aƙula tace da batul"idan bazaki Iya ci da shi ba, Ki ajiye shi ba dole" kallonta ummi tayi aikuwa ta galla mata harara, mamaki ya kama ummi ganin abun da Angel tayi mata.

 Batul kuwa ta ajiye cokalin taci gaba da ci da hannunta,

 Maganar Angel ta burge boss man, sai ƙara dubanta yake yi, abinci yake ci amma hankalin shi na akanta.

    Haris dai tun da ya dafi chips babu maijin motsinshi, sai idan anyi magana ya ɗago da ido Ya dube su.

 Mutun ɗayane baya cin abinci, Ya rasa sukuninsa, saboda mutun biyu dake zaune acikinsu, bayason baƙuwar fuska, uwa uba ummi dake ta kallon shi jefi jefi take bin shi da kallo kamar zata haɗiye shi.

 Sam Angel bata lura da yanayin da yake aciki ba, sai da Boss Man ya furta"meyasa baka cin abinci ne"? Tukunna ta ɗago ta dubi Danish don ta gane dashi yake magana.

  "Bakomai yake iya ci ba, danish me kake son ci"? Ta jefa mashi tambayar, shiru bai bata amsa ba, kamar tayi magana da kurma.

 Ummi tana yamutsa fuska tace"ai na lura kamar mune muka takura mashi,  ƙwarama ka saki jikin ka, saboda atare zamu cigaba da rayuwa acikin gidan nan"

Boss man yace"baya son baƙin fuska ne, amma tunda naga yafi sakewa da shi, Ki jaraba bashi wannan muga idan zaici" yai maganar tare da ruƙo plate din farfesu ya miƙa mata, bayan ta kar6a ta furta mashi"thank u" ta tura plate din agaban Danish.

  Cikin muryar raɗa tace"pls ka saki jiki ka ci, tunda gani atare dakai, banason kana damuwa" jinjina mata kai yai alamar toh, duk don ya saki jikin shi yasa ta sanya hannu a plate din ta soma ci shima ya sanya hannun shi suka cigaba da ci atare.

Sun dauki lokaci suna cin abincin, sunyi kulu wash rabu hani'an kafin daga bisani ɗaya bayan ɗaya suka fara miƙewa,

 Masu aikin gidanne suka tattara kayan abinci, bayan sun kwashe komai suka gyara dining room din tamkar ba'a ta6a 6ata shi ba.

 Falo suka koma, kowannansu ya zamu wuri saman sofa ya zauna, kamar yadda Man Ya basu Umarni, yana daga zaune shida ummi suna fuskantar su, sanyin A.c sai ratsa fatar jikin su ya ke.

 Sun natsu suna jiran jin me zaice"da farko dai Ina yi maku barka da zuwa gidan nan, ina fata kunji daɗin kasancewa acikin shi" ya faɗa yana dubansu.

  Amsa mashi suka yi da eh, yace "good, ina fata zaku bamu haɗin kai, mu zauna peacefully babu faɗa babu cacar baki," ɗaga mashi kai sukayi alamar eh.

  Ya ƙara da cewa"na fahimci bakomai ne kuka sani ba, to duk abunda baku gane ba kada kuce zakuyi gamon kanku, hakan zai iya haifa maku matsalar da bama fata, idan kunga abu kunaso kuyi amfani dashi baku san yarda akeyi ba, Ga auntyn ku nan yai maganar yana nuna ummi dake zaune saman sofa ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya.

 "Ku tambayeta zata koya maku, kada kuji shakkar komai, ku ɗauke mu tamkar iyayenku ko yayyanku, ina fata kuna jina"? Jinjina mashi kai su ka yi, Angel tayi shiru tana kallonshi, muryarshi ta tsaya mata aranta, ji take kamar tasan me irin muryar sai dai takasa gano komai.

  "Zaku Iya tambayar Ƴar uwarku Angel itama, don na fahimci kamar tafi ku sanin wasu abubuwan" amsa mashi su ka yi da toh.

 "Sannan duk abunda kuke buƙata ta 6angaren aike ni zaku yi ma magana, in sha Allah zanyi maku shi, Idan time din sallah yayi zanzo in tafi da mazan dake acikin ku muyi sallah akwai wurin da muke yin ibada acikin gidan nan, ina fata gaba ɗayan ku musulmai ne" ya faɗa yana dubansu

 Parveen tai karaf tace"banda Danish da Gabriel sunƙi kar6ar shahada" zaro ido ya ɗanyi yana duban fuskar Danish daya haɗe rai babu annuri.

 Gabriel Yace"nifa ƙarya take yi min, Nima musulmin ne"

 Da zolaya boss man yace"idan har dagaske kai musulmi ne to ya akai naji sunanka bana musulmai ba"?sunnar dakai ƙasa Yai yana faman sakin murmushi.

 Angel tace"nice namanta ban biya mashi shahada ba, ya faɗamin yana so ya musulunta shima" jinjina kai boss man yai, ya dawo da dubanshi gareta"shifa danish? Wani addini yake yi"?

 "Bashi da addini" dafe kai boss man yai"Eyyah banji daɗin jin hakan ba, kuma bashi da ra'ayin ya musulunta kamar Gabriel"? Girgiza mashi kai Angel tayi"bayasoma anayi mashi maganar ai, ranshi 6aci yake yi, shiyasa muka ƙyale shi"

 "Okey, kada hakan ya dameku, in sha Allah asannu zamuja ra'ayin shi" ta6e baki Danish yai jin abunda boss man yace.

  "Gabriel na dawo gareka, tunda kana so ka musulunta, babu buƙatar 6ata lokaci, Zan biya maka kalmar shahada saika maimaita da kyakkyawar niya" murmushi gabriel yasaki  bashi ba hatta sauran ƴan uwanshi sunji daɗi, ba tare da 6ata lokaci ba, Ya biya mashi kalamar shahada, wani irin daɗine ya lullu6e su Angel, shima Gabriel din daɗin yake ji sai faman washe baki yake yi.

 "Ina taya ka murnar shiga addininmu, ko kana buƙatar na canza maka suna? tun kafin gabriel ya bashi amsa su Batul su ka yi saurin cewa"Eh wallahi acanza mashi, sunan shi wahalar faɗi yake yi mana," dariya boss man yasaki jin abunda suka ce.

  "Okey, daga yau zamu dinga kiranshi da....."bai ƙarasa sunan ba yai shiru yana kallon fuskar Gabriel duk sun ƙagara da suji wani suna za'a sanya mashi.

  "SAJEED" wani irin ihun farin ciki suka saki, Sunan yayi bala'en yi masu daɗi musamman Azeeza.

      "Ina fata sunan yayi maka"? Jinjina mashi kai Gabriel yai"eh, nagode sosai"

 Boss man yace"okey, daga yanzu sunan da zaku dinga kiran shi da shi kenan wato Sajeed, Kefa Angel meye asalin sunanki" farfari tayi mashi da ido kafin ta bashi amsa da cewa"Unaisah"

 Tamkar baisan sunan ba yace"wow suna mai daɗi, mai zai hana kema mu dinga kiranki da asalin sunanki" zumbura mashi baki tayi ba tare data furta komai ba, tana son asalin sunanta sai dai tafi son sunan Angel saboda daddynta ne ya za6a mata shi.

  "Dan Allah Angel ki amince mu dinga kiranki da Unaisah Yafi daɗi Allah" Batul ce tayi maganar, Hannah tace"nima nafison Unaisah din yana da daɗi"

  Haris ma yace"nima shine za6ina, Unaisah"

 Ta6e baki Angel tayi tare da kallon fuskar Danish don taji me zaice, batasan boss man na kallon ta ba, Ya fahimci tafi ƙaunar Danish akan sauran ƴan uwanta, saboda yadda take bashi muhimmanci.

  Da ido tayi mashi alamar ta amince da sunan ko kuwa"? Ɗaga mata gira yai alamar eh.

  Dawo da dubanta tayi akan fuskar Boss man"shikenan na amince, adinga kirana da Unaisah"

 Murmushi ya saki ba tare da sun gani ba saboda mask din fuskarshi.

  Javed ne yace "um sallah ma Angel ta koya mana amma bamu taba yi ba dama tace in muka zo zamu rinqa sallah da karatu"

Jinjina kai yayi tare da fadin "karku damu zamu rinƙa karatu tare in sha Allah komai zaku iya wanda ya shafi addinin muslunci" Da alama sunji dadin maganar 

Jemimahh tace"wai kai ba zaka cire abun fuskarka ba"?

  Girgiza mata kai yai"a'a" tace "to meyasa baka son mu ganka? Ko dai mummuna ne kai baka da kyau"? Dariya ce ta kubce mashi.

  Azeeza tace"bakya jin magana jemimah ina ruwanki da shi? Ke komai sai kin nuna zaƙewa" harara jemimah ta watsa mata"Ni ki ƙyale ni," ta faɗa tana duban shi"dan Allah ka cire muga fuskarka"

  Javed yace"nima inason naganka, tun da kace atare zamu rayu agidan nan, please ka cire mu ga fuskar ka.

 Girga mashi kai yai"Ku yi haƙuri ba yanzu ba, tunda muna atare wata rana zaku ganni"

 Angel tace"babu komai, Allah ya nuna mana lokacin, Ni sai na ke jima kamar nasan muryarka don dai kace ba yanzu zaka buɗe fuskarka ba ni kuma da saina gane wanene kai" hakanan ta faɗa bada wata manufa ba, tasan batasan shi ba.

  Murmushi yai ba tare daya tanka mata ba, kallon Ummi yai, tun da ta zauna tana sauraron su bata ce komai ba

  "Ba abunda zaki faɗa masu ne"

Yamutsa fuska tayi kamar bata son furta magana tace"naso yau in taimaka masu su gyara kansu, amma nabari sai zuwa gobe ko jibi, idan na ƙara hutawa"

 Yace"okey, ku tashi mu tafi inaso zan nuna maku ko'ina na cikin part dinku, duk abunda kuka gani wanda kuke neman ƙarin bayani akanshi Ni zaku tambaya" suka amsa mashi da toh.

 Miƙewa sukayi Ummi ma ta miƙe don tana son itama ta ƙarema ko'ina na part din kallo, cikinsa da wajensa.

  Yinin Ranar sunsha yawo, Sunga abubuwan ban mamaki dana Al'ajabi, ido ya samu abinci, kamar karsu dawo cikin gidan, Boss man yasha tambayoyi kamar ƴan jarida, duk abunda basu gane ba sai sun tambayeshi ba ƙaramar wahala yasha ba, itama ummi tana taimaka mashi wurin amsa masu tambayarsu, duk yawon da suka sha basu leƙa wajen gidan ba, kuma basu shiga sauran part din ba. 

JOS CITY

Idan muka koma 6angaren Alhaji ubaid, tunda garin Allah Ya waye da sassafe Benazir ta farka tana sambatu akan mijinta da ƴarta, Alhaji ubaid Ya jira kiran Dr.shureim sai dai shiru, har kiran layin wayarshi yai amma bai ɗaga ba, ya kira Alhaji musa akaci sa'a kiran ya shiga kusan sau goma tana ringing ba'ayi picking ba, gashi lokaci yana ta tafiya babu alamun zuwan Shureim, daga bisani suka kira likita domin duba lafiyar benazir, bayan ya duddubata ya faɗa masu cewa lafiyarta ƙalau, sai dai akwai abun da ta ƙwallafa rai akanshi yaji tana fadin mijinta da ƴarta yace to kada su kuskura suce zasu faɗa mata zancen babu su, don a halin da take aciki yanzu bazata Iya jurewa ba, zata Iya samun ta6in hankali, zaifi suja baki suyi shiru, sannan suci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da zata samu natsuwa sosai, tukunna su faɗa mata, sunji dadin shawarwarin da likitan ya basu, bayan tafiyarshi cikin ikon Allah, Benazir ta dawo hayyacinta a lokacin da basu yi tsammani ba, ganin Iyayenta a gefe da gefen gadon da take akwance yasa ta rushe da kukan farin ciki tana ambaton sunayensu haɗi da roƙon yafiyarsu akan babban laifin da ta aikata na guduwar da tayi ba tare da sanin su ba, tayi mamakin jin suna kwantar mata da hankalinta, sukace su basu ruƙeta aransu ba, sun yafe mata, ta daina kuka komai ya riga daya wuce, tuna baya baida amfani tun da ya riga da ya faru, ƙaddarace da babu wanda ya isa ya canza ta, haƙiƙa taji daɗin kyakkyawar tarbar da ta samu awurinsu tayi tsammanin zasu koreta ne idan sun ganta, saima suka koma suna lallashinta haɗi da tarairayarta, abinci ma abaki hajiya layla ta bata shi, duk bayan ƴan mintuna sai ta tambayesu ina mijinta da jinjirar data bari a cikin kwamin wanka? tana son tagansu, idan suna agida dan Allah su taimaka su kaita wurin su, hajiya layla ta bata haƙuri da cewa sunyi tafiya basa a ƙasar amma tana da tabbacin sun kusa dawowa, sai lokacin tace toh ita yarinyar ta rayu? Waye ya rene ta harta girma? Kuma ya sunanta"?

 Hajiya layla tace"ta rayu mana, kyakkyawar budurwa ta ɗauko hasken fatarki, kamannin fuskarta ne dai ta ɗauko na daddynta, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, tana ta faman sauke ajiyar zuciya tace"baki faɗa min sunanta ba? Kuma tasan ni? An faɗa mata sunan mahaifiyarta? Kuma Kuna nuna mata hotona"? Shiru hajiya layla tayi don batasan amsar da zata bata ba, ita kanta ba zumunci take yi da tajuddeen ba, saboda bada son ranta ya auri Benazir ba, shiyasa ko zuwa gidan bata ta6a yi ba, tun lokacin da suka koma dubai da zama, a hotone ma ta ta6a ganin Angel din, taji nauyin amsar da zata ba benazir, daƙyar ta Iya furta mata sunanta Angel, tana faman murmushin yaƙe tace ai tasanki ya za'ai mu ƙi nuna mata hotonki, duk in tajudden ya kawota gidan nan sai mun nuna mata hotunanki, Yarinyar tana sonki sosai, kullum maganarta ina mamanta take? Yaushe zata dawo? Meyasa kika tafi baki waiwaye ta ba' jin hakan yasa benazir ta fashe da kuka, Hajiya layla duk tasha jinin jikinta, fargabarta ranar da Allah zai haɗa benazir da ƴarta idan har tana araye tabbas zaiyi wuya yarinyar ta amince da ita, ga kuma ƙaryar data faɗa mata.

Cikin shessheƙar kuka benazir tace"amma dai baku fada mata a yanayin da na tafi nabarta ba ko"? Hajiya layla tace eh bamu faɗa mata ba, mun dai ce mata kin 6ace ne ba'asan inda kika tafi ba, to dayake yarinyar tana da tawakkali kuma tana samun kulawar tajo da kuma kulawar da muke bata hakan bai dameta sosai ba"

 baiwar Allah benazir jikinta duk yai sanyi, tace Ina aneelerh da mijinta"?

Hajiya layla tace ai mijin aneelerh baya nan shima tare suka yi tafiyar, ta matsa lamba akan tana son akaita gidansu Aneelerh don taganta, Alhaji ubaid ya sanar da ita cewa ai basa garin jos sun koma abuja da zama, badan taso ba ta haƙura, damuwar hajiyar laila ɗaya kada tace su nuna mata hoton ƴarta saboda babu maishi acikinsu, har ƙwara Alhaji ubaid wata'ƙil asamu hutunanta na yarinyata saboda yana son yarinyar, cikin ikon Allah benazir bata tambayesu game da hoton Angel ba, saboda halin damuwar data shiga gani take kamar bazata ta6a ganin mijinta da ƴarta ba, duk da mommynta ta kwantar mata da hankalinta.

Masu gadin gidan kusan sau uku suna shigowa cikin gidan domin duba lafiyar benazir, duk sun damu da ita, haka zalika zainab takasa samun sukuni duk bayan ƴan mintuna saita leƙo ta dubata, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba ganin yadda kowa ya damu da ita.

  Tana akwance saman gadonta, hajiya layla tana a gefenta, a lokacin Alhaji ubaid Ya koma dakinshi, damuwar duniya ta ishe shi, tun da ya jaraba kiran layin shureim dana Alhaji ubaid basu ɗaga ba, ya rasa sukuni, sai faman yin zarya yake yi acikin ɗakin shi, kaf family dinsu babu wanda yasan da dawowar benazir, saboda bai sanar da su ba, hatta mutanan da suke zumunci da su bai faɗamawa ba, saboda mai gemu ya basu shawarar su dan jinkirta tunda ba'asan wanene yai silar yi mata asirin ba, zasu Iya ƙara cutar da ita idan suka ji cewa tana araye kuma ta dawo gida, da ace Iyayensu na araye da kuwa sune mutun na farko da zai fara sanarmawa donsu taya shi murna sai dai babu su, mutum biyu ne yafi yarda dasu ƙanin shi Alhaji musa sai ƙanwarsu autar gidansu Hajiya Laurat, second wife din mai girma sharafuddeen obinna, itama ya jaraba kiran layin wayarta bata yi picking ba, abun duniya duk ya ishe shi.

  tunda tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa rigar shan iska bata ƙara saukowa daga saman gado ba, ta tsare hajiya layla da tambayoyi 

  "Mommy shifa yaya shureim ko baya kasar ne"?

 "Yana agidan uncle dinki"

  "Baku faɗa mashi na dawo ba ne?

"Mun faɗa masa tun jiya da daddare shima yayi farin ciki hada kukanshi, yace ma yau zaizo saboda ke' murmushi tasaki"naji dadi Allah ya kawo shi lafiya, nayi missing din yayana"

Hajiya layla ta amsa mata da ameen.

Kafin benazir ta ƙara furta wani abu, Alhaji ubaid ya shigo da sallama abakinshi, atare suka ɗago suna kallon shi, da sauri benazir ta miƙe zaune tana ambaton sunanshi

  Murmushin yasakar mata kafin ya zauna daga gefen gadon yana dubansu yace"Bansan meya faru ba, Ina ta kiran layin shureim dana musa babu wanda ya ɗaga acikinsu, Har laurat na jaraba kira itama bata ɗaga ba" kafin wani ya furta magana acikin su ba zato ba tsammani, sautin ringing din wayarshi ya daki kunnuwansu, hajiya layla tace"wata'ƙil wani daga cikin su ne yake kiranki" da sauri ya ciro wayar daga aljihun shi ya duba sunan me kira, murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi

  "Wanene"? Layla ce ta tambaya ganin yadda ya saki fuska

 "Musa ne Ke kira" ya faɗa tare da picking call din Ya kara a kunnan shi

  Saboda ji da kai na Alhaji musa sai da Ubaid Ya fara yi mashi sallama tukunna ya amsa mashi da cewa"wa'alaikum salam, ina kwana yayana fatan kun wayi gari lafiya"

 Alhaji ubaid na faman washe baki yace"lafiyalou, ya iyalin naka"?

"Suna lafiya" atakaice ya amsa mashi, tun da ubaid ya fara waya, layla da benazir suka zuba mashi ido suna kallon shi duk da basa Iya jin me alhaji musa yake fadi

  "Shureim bai faɗa maka zancen dawowar benazir ba"? Ya tambaya ne don yaji baya da niyar yi mashi maganar

  Da gadara Ya furta"ya faɗa min, tun ɗazu da safe, na tayamu murna, Ina fata tana lafiya"

 Alhaji ubaid yace ai gatanan ma zaune kusa dani, Ko in bata wayar kuyi magana ne"?

  Da sauri yace"No need, basai munyi magana da ita a waya ba, dama dalilin da yasa na kira naga missed call dinka ne, ɗazu da safe shureim ya shirya zai taho nan jos, Ni na hana shi, nace mashi ya bari zanyi maka magana kuzo nan abujan gidana" da mamaki Alhaji ubaid yace"amma dai wasa kake yi min ko? Tayaya zakace min in kwaso iyalina inzo gidan ka? Ni dakai waye ya dace yazo gidan wani? ai nayi tunanin idan na fada maka dawowar benazir jiki na rawa zaka kwaso iyalinka kuzo nan domin tayani murna sai kuma naji akasin hakan" 

 Alhaji musa yace"bazan Iya zuwa jos din bane, saboda Ina da ayyuka dayawa da zanyi, shiyasa nace kuzo nan ɗin,"

  Mamaki da al'ajabi ne akan fuskar hajiya layla, don taji martanin da alhaji ubaid Ya bashi.

  "Baikamata kace min haka ba, yanzu ayyukanka har sunfi ganin ƴata da za ka yi  muhimmanci? 

 Babu alamun damuwa a muryarshi yace"yaya kasan banason jan magana, meye aciki don nace kazo gida na? Laifine? Alfarma nake nema bawani abuba, idan ba zaka yi min ba zan aje waya"

  Gyaɗa kai alhaji ubaid yai"shikenan, zamu fidda lokaci mu shigo abujan"

 Ya amsa da yawwa, sannan bana buƙatar ku zo a mota, Ni zan shirya maku komai na tafiyarku" amsa mashi yai da toh, daga haka Alhaji ubaid yayi rejecting call din, yana mai mamakin Halin Alhaji musa.

  "Me ku ka tattauna ne"? Layla ce ta jefa mashi tambaya

 Muryarshi a raunace ya furta"yace bazai samu damar zuwa nan ba, shine ma ya hana shureim zuwa saboda yafi son muje can gidan shi"

 Ta6e baki hajiya layla tayi"shine kai kuma sai ka ce mashi zamu samu lokaci muje can din ko? 

 Jinjina mata kai yai alamar eh, masifa ta soma zazzaga mashi"kasan Allah babu inda zamuje sai dai kai daya gama asirce ka kama hanya ka tafi,Ni ban ta6a ganin mutun mara kunya irin shi ba, yarinyar ta 6ace tsawon shakaru sai jiya tsakar dare ƙarfe shabiyu tadawo bata ahayyacinta shine zaice mu kwasa mu tafi gidansa saboda muke son yaganta? Kwata kwata bashi da tunani kuma baida hankali, kaida kakeyi mashi biyayya gayanan shi bai damu da ƴarka ba, 

..." tun da tafara faɗa, jikin benazir yai sanyi duk sai taji ba daɗi, Cikin sanyin murya tace"mommy dan Allah ki yi haƙuri, kada hakan ya dame ki, Ni banga laifin shi ba saboda ai ni na gudu da kaina ba korata akayi ba, wata'kil Yana jin haushin abunda na aikata shiyasa yace muje can...."

 Katseta hajiya layla tayi"benazir ba abunda kike tunani bane, mutumin nan baya ƙaunarki, saboda bai damu dake ba, tun lokacin da kika 6ace bai ta6a magana akanki ba, Mune kaɗai muka damu dake munyi nemanki har mungaji mun fidda rai da kina araye, amma musa bai ta6a sanya baki akan maganar 6atanki balle har ya taimaka wurin bada gudummuwar mu nemo ki....." Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mata maganarta"kidaina faɗa mata wannan maganar, bai dace ba, taya zakice kawunta ƙanin mahaifinta bai sonta? Akan wani dalili? Shiya furta maki da bakin shi"

 Harara layla ta watsa mashi"alama nagani shiyasa nace haka"

  Idanuwan benazir ne suka cicciko tab da ƙwalla, cikin sanyin murya tace"Ni ban damu ba, koda ace baya sona, tun da Iyayena suna sona Alhamdulillah, soyayyarku kaɗai ta ishe ni sai kuma ta mijina da ƴata, da kuma Yayana, sannan Ni na amince zanje abujan bawai don saboda shi ba, saboda inason ganin Aneelerh"

 Girgiza kai layla tayi"bafa zan ta6a bari ki je gidan mutumin nan ba, Saboda Ni ban yarda da shi ba, Idan kuma kika takura akan kinason zuwan bazan hanaki ba sai dai ki sani bazan biku ba" babu alamun wasa akan fuskarta tayi maganar.

 Magiya benazir ta dinga yi mata akan ta amince suje da ita, don ita batason suyi nesa da juna, daƙyar layla ta amince zata bisu abujan, da wata manufa a ƙasan zuciyarta don taci alwashin idan sukaje gidan Alhaji musa saita fada mashi baƙaƙen maganganun da zasu hana shi sukuni, yanzu dai sun tsaida magana zuwa jibi zasu yi tafiyar.

  Aranar shureim ya samu damar kiran Alhaji ubaid ya fada mashi uzirin daya hana shi ɗaga kiran shi, bayan sun gama magana, har benazir yace abata waya su gaisa, sun jima suna waya da ita kusan awanni suka kwashe, kafin daga bisani yayi masu sallama.

Idan muka koma 6angaren zahra tun bayan da ta koma gida, babu mutunci a tsakaninta da Aneelerh ko gaisuwar arziki bata haɗa su, ta canza mata bata sakar mata fuska ba kamar yarda suke ada ba, aranar mahboob yai mata maganar motar ta da wayarta yace dama jingina yabada su, idan tana so zata bada kuɗin adawo mata dasu, farin ciki kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha dama bada Son ranta ta bada su ba, ta haɗa mashi kudin ta bashi, a daren ranar ya dawo mata da su, tuni ta fara amfani da wayarta bayan ta mayar da sim dinta.

 A washe garin ranar laraba suka fara shirye shiryen fara aiki a Obie estate tare da sauran Interior designers dake aiki a ƙarƙashin company dinsu, tuni kaya sun iso daga dubai, Hankalin zahra ya kwanta bata da sauran  damuwa yanzu, ta ƙagara gobe tayi don suje su fara gudanar da aikinsu saboda gagarumin taro ne zasuyi idan obie zai yi birthday kamar shagalin biki saboda dukiyar da suke kashewa wurin ƙawata gidan, shiyasa zasu fara yi masu aiki tun alhamis kafin Juma'a da za'a gudanar da shagalin

 *✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426, 

 Bature Hafsat Muhammad

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post