Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 32


EX-PRISONERS

Sam ya kasa ƙarasawa gare ta, slowly yake bin jikinta da kallo, tun daga kan fararen ƙafafuwanta har izuwa saman gwiwowinta da suka kasance jawur da su kamar bata ta6a yin rarrafe ba, ɗagowa yai da eye balls dinsa zuwa saman Waist dinta da ya faɗaɗa, ganin irin mayataccen kallon da yake binta dashi ne yasa ta juya da gudu ta nufi can cikin dakin wurin closet dinsu, har sai da yaji gabanshi yaɗan faɗi lokacin data watsa da gudun mazannanta suka girgiza rigar ta bayyana shape dinsu, yawu ya haɗiya adam's apple dinsa Ya motsa sama da ƙasa.




  Yaɗan ji shock ganin baƙon al'amari ajikin Babe unaisah dinshi, bai ta6a ganin girmanta ba sai yau da yai tozali da ita cikin short gown, Kayan arzuƙa sun fara ha66aka.




   Cikin sanɗa take tafiya tana tunkaroshi, idanuwanshi akan fuskarta, still shu'umin murmushin nan take sakar mashi, hatta Yanayin tafiyarta ya canza, dogon wandon bacci ta zura a jikinta duk don Ya daina kallon mata jikinta.


  Dab dashi ta tsaya tana duban backpack din hannunshi, har cikin ranta taji dadin ganin jakar, daɗi kamar zai kasheta, haɗa ido sukayi da shi, mutumin duk ya susuce kamar wanda aka zare ma laka, sam babu kuzari a jikinshi tunda yai arba da hips dinta.




  Harara ta jefa mashi haɗi da murguɗa mashi soft pink lips dinta, muryarta da shagwa6a tace"kallon ya isa haka, bani jakar nagode" ta faɗa tana ƙoƙarin ruƙo hannun backpack din, da sauri ya ƙanƙameta a wide chest dinshi, alamar bazai bata ba, ɗaure mashi fuska tai"wai meye haka? Baka ga dare yayi ba, yakamata kaje ka kwanta, ni bansan ma ya akai boss man ya baka back pack din ba, ai daya sani shiya kawo min da kanshi" bada wata manufa ta furta maganar ba, amma da yake jarabar kishi ce dashi, sai yaji kamar tana nufin tafi son ganin boss man akanshi shiyasa tace haka, aikuwa nan take Ya haɗe rai, babu annuri ko misƙala zarratin, ganin ya fusata yasa tace"meye faru my man"? Wurgar mata da jakar Yai ƙasa, da sauri Ya juya Ya nufi ƙofar fita kamar zaiyi tuntu6e, Jiki na rawa tabi bayanshi tana ambaton sunanshi"My man! Dan Allah ka tsaya muyi magana, Ni ce na bata maka rai ko? Pls am sorry bazan ƙara ba, Ka yafe ni pls, bazan Iya bacci kana fushi dani ba" 




Har ya kusa fucewa daga ɗakin, Can kuma sai ya dakata kamar mai tunanin wani abu, Ba zato ba tsammani taga ya juyo a sukwane, ƙiris Ya rage ta hade kirjinta da nashi, gadan gadan Ya tunkarota hakan da yai ba ƙaramin tsoro yaso ya bata ba, Juya tayi da niyar ta faɗa toilet, ta 6oye sai dai kafin ta kai ga shiga taji Ya damƙi waist dinta da ƙarfi Ya ɗaga ta sama kamar ɗiyar roba, tadinga ihu tana fadin Am sorry my man dan Allah kada ka 6alla ni"




 Batul dake a kwance tana sharar bacci, koke koken Angel ya fara takura mata sai faman mutsu mutsu take Yi alamar zata farka.




  ya tsareta da reddish eyes dinsa da launinsu Ya ciza tamar zallar red, da kakkausar murya ya furta"meyasa kike son 6ata min rai"? Ya fada batare daya sauke ta ƙasa ba,


 Jikinta na kerma tana faman wutsil Wutsil da ƴan ƙafafuwanta tace"danish dan Allah ka ƙyaleni, kaga Batul dake bacci tafara takura da surutunmu, kuma ni bansan laifin me nayi maka ba, amma ina baka haƙuri ka tafi ɗaki ka kwanta"




  Ta6e la66ansa Yai alamar bai damu ba, kafin ya sassauto da Voice dinsa"Kin hana zuciyata sakat, tunda safe da kika rungume ƙaton nan Hankalina ba akwance yake ba, nakasa samun sukuni, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji, ke ko ajikinki, baki leƙo dakina kin duba halin da nake aciki ba,saboda ke banci dinner dina ba, baki damu dani ba, ko nema na bakiyi ba, saboda kin samu wanda yafi ni ko"




  Runtse idanuwanta taɗanyi, hadi da dafe kai da hannu ɗaya, dama saida ranta ya bata bazai ƙyaleta ba, saboda jarabar kishinshi, shiyasa yau ta hana shi ganinta, duk dan ta tsira daga fushin shi.




  Shirun da tayi mashine Ya ƙara 6ata mashi rai, Baisan sa'adda Yai zazzafan taku Ya nufi Saman shimfidedan gadonsu, Ya jefar da ita Ta faɗa saman lallusar mattress din, da sauri ta juyar da jikinta tai kwanciyar rubda ciki, gudun kada Gyaran gashin da akayi mata ya tarwatse, Cikin shessheƙar kukan ƙarya Take Fadin"Nifa bada son raina ya rungume ni ba, Hijab din jikina ce ta taɗiyoni na tafi zan kife ƙasa shine Ya tarbeni na faɗa chest dinsa, kaima ka sani bani marmarin kasancewa da wani ɗa namiji idan bakai ba, dan Allah kadaina tayar da hankalinka akaina, saboda Ni taka ce kai kaɗai, shi mutumin ma da kake Yin kishi akanshi babbane ba matashi ba, Ya isa ya haifemu nida kai"




 Tun da ta fara yin magana, Ya rasa sukunin shi, Gyaran gashinta Yai matuƙar jan hankalin shi, kamar princess, twisting din da akayi mata guda biyu saman gashin ya ƙara mata kyau, sam bata ji motsinshi ba, ta dage sai haƙuri Take bashi, jin hucin numfashinsa a jikinta Yasa tai wuff Ta juyo Tana fuskantar shi, har saida gabanta Yaɗan fadi ganin Yadda yai mata rumfa, tuni tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta"meye haka"


 Lumshe mata ido yai tare da waresu saman fuskarta, abun ya ɗaure mata kai, Yana neman ya rikitar da ita.


  Ganin dagaske kamar wani abu yake so yai matane yasa ta fara canza mashi fuska, zuwa ainihin true colour dinta, runtse ido tai da masifa tace"danish ka tashi ka tafi ɗaki, wallahi kada ka bari na buɗe ido na ganka ranka zai Iya 6aci" saida ta gama zazzaga mashi faɗan ta buɗe ido a hankali don taga idan ya tafi, ko gizau baiyi ba yana nan yadda yake, Cikin zafin nama ta daddage ta ɗaura hannayenta saman ƙirjinshi da niyar ta ingije shi, sai dai takasa yin hakan sakamakon wani abu daya tayar mata hankali, a ruɗe take kallon shi ayayin da take kokarin mikewa zaune ta jingina bayanta jikin headboard na gadon, Cikin sanyin murya ta furta sunanshi"My man"




  Idanuwanshi tuni sun fara canza launi, numfashinshi na fita da huci hucin zafi.




  "Faɗamin meke damunka? Baka da lafiyane? Meyasa naji zafi ajikinka"?


  Da wata irin kasala Ya kwantar da kanshi saman mattress dinsu, kasancewar Gadon Yana da fadi Batul tana daga can 6angare guda.


  "Kayi shiru baka bani amsa ba, kasan bana so Ina magana kana shareni,"


    Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta"am sorry idan na 6ata maki rai, yanzu zan tafi na kwanta" ya ambaci hakan tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon, da sauri ta biyo bayanshi tana ƙwala mashi kira, sai dai kafin ta isa gare shi, tuni Ya fuce daga ɗakin, ƙofar tayi locking, kwantar da kanta tayi saman glass door Din, Jikinta yai mugun yin sanyi, hankalinta Ya tashi ssai, ta girgiza da jin zafin jikinshi tamkar hucin garwashin huta, taya zata iya runtsawa bayan bata da masaniya akan halin da yake aciki? Gashi ya faɗa mata baici dinner ba duk don saboda da ita! Ruwan hawaye ne suka taru acikin idonta, da sauri ta juya tana duban hadaddiyar wall clock din dakin ƙarfe 10 na dare, badan taso ba ta haƙura da bin bayanshi amma taci alwashin da asuba zata je ta dubashi, kamar yadda taga rana haka taga dare, bacci ya ƙaurace ma idanuwanta, sai faman juyi take Yi saman gadonsu, duk ta takura kanta ta hana zuciyarta sakat.




*FRIDAY MORNING🥳💃💃💃*




Bayan tasowa daga sallar asuba, dattijon arziƙi Ya nufi Sashen da bedroom dinsa Yake hannun shi ruƙe da sanda, Farar Jallabiyace a jikinshi, lokacin daya ƙarasa bedroom dinshi, da sandar hannun shi Ya tura ƙofar shigar shi keda Wuya kafin ƙyaftawar ido Hasken ɗakin Ya ɗauke, duhu Ya mamaye idanuwanshi, Abunka ga tsoho duk Yabi ya ruɗe, muryarshi Adabarbace yake fadin"subhanallah, Waye ya kashe min hasken ɗaki? jazz bana son shaƙiyanci nasan kai kaɗaine zaka Iya min haka? Wai jazz baka ji Ina magana" ya fada Yana cigaba da yin tafiya cikin duhu, Ya daura hannu ɗaya jikin bango Yana laluban Switch don Ya kunna hasken dakin, Cikin 6acin rai Yake Fadin"Jazz wallahi kada ka bari in kunna hasken ɗakin nan, ranka zai 6acine, wato raini Ya fara shiga tsakanina dakai shiyasa har kake Yi min shegantaka ko"?




 Daƙyar Ya samu Ya shafo switch din, a harzuƙe Ya danna button din, A hankali Hasken ɗakin Ya soma gauraye ko'ina, tamkar da rana, Juyawar da zaiyi unexpected Yaga abunda Ya bashi mamaki da al'ajabi, wato gaba ɗaya furannine launin ja da yellow tun daga saman head boad har izuwa saman zanin gadonshi, An ƙawatasu masu kyan gaske har ƙyalli suke Yi, tamkar a mafarki Yake kallon ikon Allah, A hankali yake dogara sandarshi Yana tunkarar gadon tamkar maijin tsoronshi, saida Ya matso kusa Ya ƙura ido Yana so ya gane rubutun me akayi da furannin, karantawa yai




  *"HAPPY 80TH BIRTHDAY TO OUR BACKBONE"*




  Lokaci daya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, Farin ciki mara misaltuwa ya lullu6e shi, Sai faman sakin murmushi yake yi kamar wani zautacce, daga end bed din Ya zauna, Yana ƙarewa furannin kallo, ranshi yana bashi cewar ƴa'ƴanshine suka shirya mashi furannin, tabbas sune, Yayi mamaki babu wanda ya sanar dashi zasuyi mashi hakan, Kuma atare dasu ya dawo daga masallaci, tun a babban falon gidan suka rabu da juna kowa ya kama hanyar part dinsa.




    Yayin da yake bin adon furannin da kallo, cikin sa'a idanuwanshi suka yi mashi tozali da birthday cards birjik aka ajiye mashi don Ya karanta, kusan guda bakwai daga saman kowani card an ɗaura fure, hayewa yai saman gadon har zuwa gaban cards din Ya ɗago dasu a hannunshi kowanne yana da tittle dinsa da kuma sunan mamallakinsa, Card din farko Sunan senate lateef ne, buɗewa yai ya soma karantawa kamar haka.


   


_"To my dear father, thank you for always being there for me, guiding me, and making me the person I am today. Your support, love, and encouragement have made me who I am, and I'm so grateful for that"_




 tuni idanuwanshi sun cicciko da ƙwallar farin ciki, Ajiye card din lateef yai, ya buɗe card na biyu mallakin Sir mubarak Yana duban sakon cikin shi




  _"From the bottom of my heart, I want to wish you a very happy birthday, Dad! Your wisdom, kindness, and sense of humor have always brightened my days" annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake Yi, haƙiƙa sunyi matuƙar faranta mashi da daɗaɗan kalamansu, Yana matuƙar ƙaunar ƴa'ƴanshi.




  Ajiye card din sir mubarak Yai, ya buɗe Na Sharafuddeen calmly ya ke reading dinsa


   "Happy birthday, Dad! You are the best father in the world and we are so lucky to have you. May your day be filled with happiness and love." hawayen da suka taru acikin idanuwanshi tuni sun jiƙa fuskarshi, sumbatar card din Yai, kafin Ya daura shi saman wadanda ya karanta, Ya duba sakon Prime minister 




   _"I'm so glad to have a father like you, who has been a rock of support through the ups and downs of life. You've always encouraged me to be the best I can be, and that means the world to me. On this special day, I just want to say thank you for everything you've done for me. Happy birthday Baba tsoho much love"_ 




Dariya ya saki har fararen haƙoranshi suka Bayyana, Kalmar ƙarshe ta saƙon Hateem ne Ya bashi dariya daya ce baba tsoho.


  Lumshe idanuwanshi yaɗanyi yayin hawaye ke cigaba da wanke fuskarshi, abu ɗaya ne yake fargaba a duniyar nan ranar da zai barta saboda ƴa'ƴanshi, bai sani ba tsakanin shi da su wanene gawar fari, bai fata ma Wani daga cikinsu Ya riga shi tafiya, bazai Iya jurar rashinsu ba, Ya ƙwammace mutuwa tafara Yin awon gaba dashi.




  Sumbatar card din Hateem Yai, kafin Ya buɗe na saratu


   


- On this special day, I want to let you know how much I appreciate everything you've done for me, Dad. You've always been my biggest fan and supporter, and I can't thank you enough for that. Wishing you a very happy birthday, with lots of love My Baba, Allah yabarmun kai, madubin dubawata" manna ma card din kiss Yai kafin Ya duba na sauran ƴa'ƴan nashi, waɗanda basu kaiga ƙarasowa Gidan ba, suma sun bada saƙon da aka rubuta masu a cards dinsu.




  Farin cikin duniya ya cika Obie, kwanciya yai saman furannin idanuwanshi na fuskantar ceilling.


  Ba zato ba tsammani Yajiyo sautin muryoyinsu acikin kunnuwanshi, Suna faɗin"Happy Birthday To You, Happy birthday to You, Happy birthday to our Baba" zumbur Obinna Ya yunƙura ya miƙe daga saman gadon Yana duban ƙofar room dinshi.


  Dr. jazz ne Ya fara shigowa hannunshi ruƙe da madaidaicin Cake mai hawa huɗu daga saman shi an jera candle, ga cake knife gefe ɗaya.




  Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa'ƴan shi suke shigo ajere kowannansu sanye da hadaddun jallabiyoyi, Mutun Na farko Sir mubarak ne daga bayanshi Senate lafeef ne, wanda ke abiye dashi His excellency Abdul Razak ne Gomnan Jihar lagos, baisan Yaushe Suka shigo garin abuja ba, Yayi mamakin ganinsu, zuwan bazata suka yi mashi, ga kuma His excellency Deen Obinna Na jihar kaduna state, Daga bayanshi mai girma sharafudden Obinna ne, Hannun shi ruƙe dana ɗan uwanshi Prime minister hateem obinna, abun gwanin ban sha'awa, bayansu sai Saratu data shigo itama jallabiyarce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Fuskar kowannansu ɗauke da annurin farin ciki, maimakon Ya taso Ya karaso garesu, sai kawai su ka ga ya fashe da kuka, haɗi da sanya tafukan hannayenshi biyu Ya rufe fuskarshi.




Jikinsu duk Yai sanyi, duk da ransu yana basu cewar kukan farin Cikine Ya ke yi, gefe da gefen gadon kowan nan su ya zauna kamar masu neman gafara, Senate lateef Ne Ya fara magana


  "Baba meyasa ka yin kuka? Dan Allah kada ka karya mana zuciyoyin mu, munci burin mu faranta maka a wannan ranar mai albarka rana mafi daraja agaremu, ranar da abun alfaharinmu Yazo duniya" ta tsakankanin yatsun hannunshi Yake satar kallonsu, Muryar saratu da shagwa6a tace"baba please kadaina wallahi bamu jin daɗin ganin hawayenka masu tsada suna zuba ƙasa"


  "Baba idan baka daina kukan nan ba, muma zamu fara" acewar Sir mubarak


  Mr.president sharafudden Yace"Daddy ka bamu dama mu share maka hawayenka da hannayenmu please"


 His excellency Deen Ya kar6e da cewa"daddy saboda kai, muka kamo hanya tunda duku duku muka shigo abuja, saboda muhimmancinka agare mu, dan Allah ka buɗe fuskarka ko mun samu damar ganinka, munyi kewar mahaifinmu" kalamansu ba ƙaramin karya mashi zuciya suke Yi ba, sai dai yakasa cire takufan hannayenshi daga saman fuskarshi, Allahu akhbar, wato Iyaye dabanne, duk mun muƙamin mutun shi bakomai bane agaban Iyayenshi, gaba ɗayansu nan manyan mutanene masu ruƙe da manyan muƙaman ƙasa, masu ƙima da daraja a idon duniya, Yau gasu zazzaune gefen gadon mahaifinsu, sun tasa shi agaba suna lallashinshi, abun da yake ƙara haddasa mashi jin ƙaunarsu Biyayyar da suke yi mashi, tun suna ƙanana har zuwa girmansu bai ta6a danasanin kasancewarsu a matsayin ƴa'ƴanshi ba, basu ta6a sanyashi ciwon kai ba, samun ƴa'ƴa nagartattu irinsu abune mai wuya a zamanin nan, damuwarshi tasu ce, suna matuƙar ji dashi suna gatanta shi suna kyautata mashi shiyasa suke damun cigaba arayuwarsu saboda albarkar dayake sanya masu.


 Muryar His excellency deen Ce Ta katse mashi tunaninshi


  "Baba munji kayi shuru baka ce komai ba, Idan akwai abunda ke damunka please Ka faɗa mana, baka da tamkar mu a duniyar nan, ashirye muke da mu share maka hawayenka"


  da zolaya Sir mubarak Ya dubi jazz"faɗamin gaskiya kodai kaine ka 6ata mashi rai"?


 Jazz na murmushi yace"wallahi bani bane..." daƙyar ya ƙare maganar ganin irin kallon tsiyar da hajiya saratu take watsa mashi, Muryarta a kausashe tace"tunda ka kawo cake din miƙo min shi ka fuce kabamu wuri," Jiki asanyaye Jazz Ya nufeta Ya miƙa mata tray din, Tasa hannu ta ƙarba tana faman jifarshi da harara, sam bayason barin Ɗakin, idan Yana atare da su ji yake kamar Yana acikin danginshi mantawa yake yi da shi bakowa bane a family dinsu.


 Har Ya juya zai fuce Muryar Hateem ta dakatar dashi"Zonan jazz" dakatawa yai dayin tafiyar da sauri Ya koma gaban gadon, Hateem Ya sanya hannu ya kar6i cake din hannun saratu Ya miƙa mashi"kamar yadda ka kawo shi kai nake so ka fara bashi" ɗaure fuska hajiya saratu tayi badan tana jin shakkar Yaya hateem ba da kuwa babu abunda zaisa ta bashi cake din, bawan Allah Jazz sai faman sakin murmushi yake yi, ya kar6a Yana fadin"nagode daddy hateem," jinjina mashi kai Yai batare daya ƙara furta komai ba.


  Baba, zamu tafi bamusan ko mune ke bakason gani ba, His excellency abdul razak ne Ya furta hakan, Sai lokacin Dattijon arziƙi Ya zame tafukan hannayenshi daga saman fuskarshi, tsufanshi Ya ƙara bayyana sosai, tamoji tamoji duk Ya kame fatarshi, Zaro hanky Sir mubarak Yai daga cikin aljihun shi, Ya soma share mashi hawayenshi, Bayan Ya kammala yasoma dubansu ɗaya bayan ɗaya, bi da bi, gaba ɗaya kamannin fuskarshi suka ɗauko, Musamman sharuffudeen da hateem tamkar yai kakinsu, hatta hasken fatarsu kalar nashi ne, launin idanuwansu ne dai kalar na mahaifiyarsu reddish brown.




Ganin yadda duk suka damu ya sanya shi sakar masu fuska, cikin sanyin murya yace"kai nifa ba wani abu ke damuna ba, Farin Cikin ganinku ne ya sanya ni kuka, don haka ku kwantar da hankulanku, Jazz miƙo min cake din nan" Ya faɗa Yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadonshi, mimmiƙewa sukayi tsaitsaye suka kewaye shi, Tuni damuwar fuskarsu ta washe


  Miƙa mashi cake din Jazz Yai, sai da suka fara kirga mashi one two three kafin Ya hura Iska Candles din jiki suka mutu, tafa mashi hannu sukai, sai faman sakin murmushi yake Yi, 


   "Wazai fara bani cake din" ya fada yana dubansu, 


  Matsa ma jazz hanya sukayi Ya matso kusa dashi, Hajiya saratu ji take kamar ta ingiza ƙeyarshi taji haushin kasancewarshi acikinsu, aganinta bashi ya dace Ya shigo cikinsu ba, Ina laifin su twins suda su ke jikokinshi.




  Shikuwa Hannunshi Har kerma yake yi wurin daukar wuƙa, Ya gutsiro cake din Ya miƙa mashi abaki, Ya soma ci atsanake Yana duban Jazz hada ɗaga mashi gira Ya furta"Waye ya haɗa min wannan? Yai min daɗi"


 Jazz yace"mommyna ce ta haɗa maka shi" jinjina kai yai"amma ta iya na jinjina mata" daɗi jazz yaji An yabi cake din mahaifiyarshi, saratu kuwa takaicin duniya ya isheta.


   Daya bayan ɗaya suka soma bashi cake din Yana ci, Kafin shima Ya kar6a Ya bi kowannansu Ya bashi abaki, Bayan sun kammala ci, Ya daura cake din saman table,


 Rungumarsu Ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana bubbuga bayansu da hannayenshi kamar yadda ya saba yi masu tun suna Yara.


 Saman gadonshi Ya koma ya zauna yace masu duk su zazzauna yana son yaita kallonsu, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, kamar yadda ya basu umarni haka suka samu wuri saman mattress din suka kewaye shi.




  Banda jazz wanda tuni Yajima da komawa ƙofar ɗakin, ganin irin kallon barazanar da hajiya saratu take Yi mashi kamar zata shaƙe shi.




Tun wuraren ƙarfe goma sha biyu na safe, Hamshakan motoci keta kurɗaɗowa cikin gidan tunkafin lokacin da za'a fara gudanar da shagalin Ya gabato, sun Cika gidan, kasancewar Baba Obie mutunne mai tarin jama'a, wasu ma ba a ƙasar suke zaune ba, amma aranar sai gasu sun shigo Nigeria duk don saboda su halacci taron taya murnar ranar haihuwarshi, Masu aikin gidan sai zarya suke Yi wurin Kaima baƙi abinci dana sha, kitchen ya zama Dandalin magulmata, Bakunansu ko gajiya ba su yi da surutu.




  "Yau zamu ba idanuwanmu abinci har su ƙoshi" Safa ce tai maganar,


 Sophia tace"Hmm, aini yin aiki agidan nan gaba ta kai ni gobarar titi ajos, waiku kunga haɗuwar Prime minister Hateem da matarshi! Wow masha Allah, Allah Yayi halitta"


   Marwa tace"shi kaɗai kika gani kenan, baki ga Mai girma sharafudden ba, ai hadashi jiya cikin waɗanda sukaje airport tarbo prime minister, wallahi mutumin ba ƙaramin burgeni yake Yi ba, dashi da ɗan uwanshi hateem, mutanan badai aji ba, komai nasu da dattako suke Yin shi.




  Abla tace"yau zamuci uwar sabada, zamu tashe mu watse, Mu raƙarƙashe don nasan dole agayyaci mawaƙa da makaɗa, Ni nama rasa wani kaya zan sanya wallahi"




 da zolaya safa tace"kalar dangi, Uban wa kike tunanin zai barki ki shiga hall din taron? Ke kin isama? Sannu isassa mai walkin sa, ai kawai ki tsaya a iya matsayinki, Ta ina zaki nemi haɗa kafaɗa da Manya manyan hamshaƙan attajiran masu kuɗi, ai idan kin ganki a hall din can to amatsayin mai raba abinci zaki je" dariya suka saki.




  Abla tace"Nima fa da wasa nake wallahi, Ai ni tsoronma shiga zan ji, jiya izuwa yau bani da kwanciyar hankali saboda jami'an sojojin da suka kewaye estate din ciki da waje, nasan duk zuwan hateem ne yasa aka ƙara tsaro har haka"




  Marwa tace"ni

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post