Al'ummar Hayin Danmani Sun Karrama Mr. M.I Hassan Domin Gudunmawarsa ga Cigaban Gari da Matasa


AL'UMMAR HAYIN DANMANI SUN GIRMAMA MR. M.I. HASSAN 52U COORDINATOR KADUNA DOMIN GUDUMMAWARSA NA SA SOLOLI A MAQABARTA DAKUMA KOKARI WURIN CIGABAN MATASA TA HARKAR WASANNI.


Gamayyar Kungiyoyin Matasan Danmani, Dalibai, ‘Yan Kasuwa, Da Kungiyar Cigaban Al’umma sun baiwa Malam M.I lambar yabo Coordinator 52U na Jihar Kaduna, bisa la'akari da hidima ga bil'adama da kuma ci gaban al'umma a yankin.


Malam Hassan, dan asalin Hayin Danmani, ya nuna jajircewarsa ga matasa ta harkar kallon kafa da mata dan samarda abun dogaro a cikin al’ummarsa. Nasarorinsa masu ban mamaki sun haɗa da:


1. Sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a makabartar Hayin Danmani.

2. Bayan kammala zamanmu da Malam M.I Hassan ya ziyarci wani shiri na karfafawa mata Gwiwa ta hanyar koyon sana'o'i a fannin abinci, wanda ya dauki nauyin fom 50 don tallafawa wannan shiri.

3. Bugu da kari, ya bayar da tallafin kudi ga majinyata a asibitoci, inda ya nuna tausayi da sadaukar da kai wajen inganta rayuwar wasu.


A matsayinsa na tsohon kocin kwallon kafa a Hayin Danmani, yadda Malam Hassan yake taka rawar gani a wasanni ya taimaka wajen tsara wani sabon tsarin ci gaba ga matasa a cikin al’umma. Jagorancinsa da ƙwarewarsa sun taimaka wajen haɓaka ci gaban matasa da ƙarfafa mata ta hanyar dandalin dijital na 52U.


A yayin bikin karramawar, Mista Hassan ya nuna jin dadinsa ga karramawar da aka yi masa, ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya ga ci gaban matasa da mata a Hayin Danmani.


Ambasada Ahmad Ashir, Shugaban gamayyar Kungiyoyin Matasa, Dalibai, ‘yan kasuwa, da ci gaban al’umma ta Danmani, ya baiwa Malam Hassan lambar yabo, inda ya yaba da irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’ummar Hayin Danmani.


Comr. Ahmad Ashir 

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasa, Daliban Danmani

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post