Daga Usman Ibrahim
An haifi Abdul'azeez Butu ne a Jihar Borno dake Arewa ta gabashin Najeriya amma ya Girma a Barikin Soji ta NDA kuma a yanzu haka Yana zauna a Unguwar Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna a Najeriya.
Abdul'azeez Butu ya Fara Buga kwallon kafa ne a shekarar 2009 inda ya buga kungiyoyi daban Daban irinsu Mahuta United da Rakiya Football Academy ya kuma Bugawa DMF Football Academy wasu Muhinman Wasanni da dai sauransu.
Abdul'azeez ya zauna a jihohi irinsu Edo da Niger da Legas da Birnin tarayya Abuja da kuma Jiharsa ta Haihuwa Borno lokacin da mahaifinsa ke Aikin Sojan Najeriya.
Butu ya Fara yin tafiye tafiye ne tare da kungiyar kwallon kafa ta Rukayya Academy Kaduna inda ya kwashe wasu shekaru tare da Ita kuma Suka yi Tafiya jihohi daban Daban a Najeriya da Nufin Niman Aiki.
Bugu da kari, Dan wasan tsakiyan Abdul'azeez ya Samu damar zuwa wani wasan gwajin Daukar Yan wasa da Kungiyar Rukayya Academy inda a nanne Suka Buga wasan Sada Zumunci da Tawagar Coach Manu Garba a sansanin Tawagar Golden eaglet ta Kasa Yan Kasa da shekaru 17 Wadanda Suke dab da zuwa Brazil a shekarar 2016.
Sai dai abin takaicin an cisu a Wannan Wasa da ci 4 da 1 amma Alhamdulillah Abdul'azeez Butu da wasu Yan wasansa sun Samu Gayyata zuwa sansanin Golden eaglet a Filin wasa na goal Project Abuja inda Suka kasance domin samun Gurbi a Tawagar a shekarar 2015.
Abdul'azeez Butu har Ila yau anan ne ya Samu buga Wasannin Niman Gurbi tare da wasu fitattun Yan wasa a yanzu irinsu Victor osimen na Galatasaray da Nwakali da Daya daga Cikin abokansa dake Mando da kuma abokinsa na kusa da Suka taso a Barikin 81 dake NDA Kaduna wato Kingsley Michael.
Baya ga Wannan, Butu ya Buga wasa da wasu Manyan Yan wasa Kamar su Moses Simon( Ajala) na Super Eagles da Usman Amodu Wanda ya ci U17 da Tawagar Marigayi Yemi Tela da Dady Barau na kawo da kuma Sauran Abokan bugawarsa irinsu Abdulrazak ishaq na FC Andeletch ta kasar Belgium da Ibrahim yahaya na El kenemi ta Jihar Borno.
A lokacin da yake fadi tashi, Abdul'azeez Butu ya kuma yi tafiye tafiye zuwa jihohi daban Daban a Najeriya irinsu Lagos da Kogi da Anambra da Keffi da Nasarawa da kuma Babbar Birnin tarayya Abuja da Sauran wurare.
A cewar Dan wasan, a yanzu haka shi Dan kungiyar kwallon kafa ta Mahuta United ne dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Yanzu haka Abdul'azeez Butu yana ci gaba da Daukar atisaye da Buga Manyan Wasanni domin jiran wata dama da zata iya zuwa kuma Babbar fatanshi shine ya Samu dama ketara hazo zuwa Nahiyar turai duk da Cewa a Koda yaushe Yana baiwa Allah zabi ne akan abin daya fi zama Mashi mafi Alkhairi.