Da dumi-dumi: Uzurin Tinubu bai isa ba, APC na iya hukunta shi kan kalaman da Buhari ya yi

 Shugabancin jam’iyyar APC, ya ce jam’iyyar na iya hukunta jagoran ta na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kan kalaman da ya yi kan shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanakin baya.Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Asabar.

Idan dai za a iya tunawa, Tinubu a wata ziyara da ya kai wa wakilan jam’iyyar a jihar Ogun ranar Alhamis, an ga shi a wani faifan bidiyo a ranar Talata yana takama da cewa ya taimaka wa Shugaba Buhari da wasu mutane a zabe.

Duk da cewa Tinubu ya fitar da wata sanarwa domin fayyace kalamansa game da shugaban kasar a ranar Juma’a, Adamu, ya ce uzurin da aka bayar bai wadatar ba.

Adamu ya bayyana cewa "Muna iya hukunta shi (Tinubu) saboda kalaman da ya yi wa shugaban kasa".

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post